FALALAR FATIHA
*******************
Wannan hadisin da zan kawo muku yana daga
cikin abubuwan da Manzo (saww) yake karbowa
daga wajen Ubangijinsa ba tare da Mala’ika
atsakani ba.
.
Manzo (saww) yace Allah yace “NA RABA SALLAH
ZUWA KASHI BIYU TSAKANINA DA BAWANA.
KUMA BAWANA ZAI SAMU ABINDA YA ROKENI.
IDAN BAWA YACE:
“AlhamdulillahiRabbil
Alameen”. Sai Allah yace “BAWANA YA GODE
MIN”.
idan yace “ARRAHMANIR RAHEEM”. Sai Allah
yace ”BAWANA YAYI YABO AGARENI”.
Idan yace: “MALIKI YAUMID DEEN” Sai Allah
yace: “BAWANA YAYI MIN KIRARI”.
Idan yace “IYYAAKA NA’ABUDU WA IYYAKA
NASTA’EEN” Sai Allah yace:.”TO WANNAN
TSAKANINA DA BAWANA NE. KUMA BAWANA YA
SAMU ABINDA YA ROKA”.
Idan kuma yace: “IHDINAS SIRAATAL
MUSTAQEEM. SIRAATAL LADHEENA AN’AMTA
‘ALAIHIM, GHAYRIL MAGDHOUBI ‘ALAIHIM
WALADH DHAALLEEN”.
Sai Allah yace: “WANNAN NA BAWANA NE.
KUMA BAWANA ZAI SAMU ABINDA YA ROKA”..
– Imamu Muslim ne ya ruwaito hadisin…
.
Hakika wannan hadisin yana karantar damu
tsantsar falala da kuma, gaga rumar Albarkatun dake cikin wannan sura.
.
Ya Allah ka Qara mana Imani da Ikhlasi da
Taqwah wajen bautarka da neman yardarka. Ka
gafarta mana dukkan zunubanmu ka yake mana
laifukanmu don albarkacin Alqur’aninka wanda
ka saukar ma fiyayyen Annabawanka (saww).
*************

Advertisements