Jigon ISIS Ya Samu Bizar Zuwa Nijeriya Ne A Bisa Ka’ida, Inji Gwamnatin Tarayya
Shahararren daya daga cikin shugabannin ISIS, Ahmad Al Assir ya samu bizar shigowa Nijeriya ta hanyoyin da suka dace, kamar yadda mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya bayyanawaa majiyarmu ta Daily Times a jiya Laraba.
Al Assir, wanda yake da alaka da kungiyar ta’addanci ta ISIS, kasashe da dama sun jima suna nemansa ruwa a jallo.
An kama shine a filin tashi da saukan jirage na Rafik Hariri da ke birnin Beirut na kasar Labanon. Ya mallaki fasfon kasar Falasdin na bogi, da kuma bizar shigowa Nijeriya, wanda wa’adinsa ya kare.
Kwanakin baya dai kungiyar Boko Haram ta Nijeriya ta alakanta kanta da kungiyar ta ISIS wadda ta addabi kasashe irin su Iraki, Syria da Libya, inda kuma suke da shirin agazawa ‘yan ta’addan na Nijeriya.
A dalilin haka ne ya sa bayan an kama shi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Nijeriya da su gudanar da bincike kan yadda aka yi ya samu bizan Nijeriya na bogi.
Malam Garba Shehu ya bayyana cewa binciken ya nuna cewa Al Assir ya samu bizan ne ta hanyoyin da suka dace.
Ya ce ” duk wani zargi na neman alakanta mutumin da gwamnatin Nijeriya ba daidai ba ne. Mu burin mu shine gudanar da bincike kan takardun samun bizan. Idan har muka gano cewa babu wata matsala tattare da samun bizan babu wani matakin mai tsanani da za mu dauka, musamman da yake ya yi amfani da bizan da wa’adinsa ya kare ne”.
Kakakin shugaban kasan ya kara da cewa “gwamnati tana jira sakamakon binciken, amma rahotannin da suke bayyana sun nuna cewa takardardun samun bisan ba su da matsala. Idan har ya rubuto ne a matsayin dan yawon bude ido ko dan kasuwa, to babu wata kwakkwarar hujja da ma’aikatan bizan za su gabatar don zarginsa a matsayin dan ta’adda”.

Advertisements