GA SHARHIN JARIDUN NIGERIA
.
1-THE PUNCH
Shugaban nigeria PMB zai samo alkalai masu gaskiya da rikon amana da jajircewa akan aikinsu domin suyi shari‘ar mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa da sace kudin kasa@
.
2-DAILY TRUST
Rundunar sojojin saman nigeria ta fara ruwan bama bamai a cikin dajin sambisa matattarar yan boko haram, hakan na zuwane bayan an basu watanni 3 su kawo karshen B.H@
.
3-VANGUARD
Shugaban kungiyar boko haram (Abubakar Shekau) ya karyata ikirarin shugaban CHADI idris daby na cewa ya mutu, inda yace har yanzu yana nan a raye, a wani faifai audio@
.
4-NIGERIAN TRIBUNE
Wasu jiga jigan jam,iyyar PDP ciki kuwa hadda party chierman da tsohon mataimakin gwamna da membobi samada 1000 sun fice daga cikin PDP sun dawo APC@
.
5-THIS DAY
Kasar ENGLAND zata bude wani office a NIGERIA wanda zai hada karfi da karfe tareda hukumar yaki da cin hanci ta kasa mai zaman kanta ICPC domin su yaki cin hanci da rashawa@
.
6-LEADERSHIP
Mafarauta da sojoji sunyi nasarar kashe wata katuwar (Dorinar Ruwa) data addabi mutanen yankin dadin kowa dake yamaltu deba L.G.A Gombe State inda sukayi watandar namanta suka cinye@
.
7-THE NATION
Yau za‘a fara bincikar dakatarwar da tsohuwar gwamnati tayiwa wasu dakarun sojoji kimanin 4000 wai saboda sunki bin umurnin manyansu akan zuwa yakin boko haram a wancen lokacin@
.
8-#TAFIDANKAURAMEDIA
@Wata kungiyar matasa ta gudanar da wani maci zuwa fadar shugaban kasa dake birnin ABUJA domin nuna goyon bayansu ga PMB akan kokarinsa na kwato kudaden da jami‘an tsohuwar gwamnatin PDP suka sace a A Zamanin mulkinsu
.
9-TAFIDANKAURAMEDIA. Senator Tijjani Yahaya kaura senator Maiwakiltar zamfara ta Arewa, ya bayyana cewa: majalisa zata kafa dokar dazata habbaka samarda ma’adanan kasa.

Advertisements