ALHAMDULILLAHI-RABBIL-ALAMIN.
Ayau ne Alhazan Nigeria, zasu fara tashi zuwa kasamai tsalki, kuma Mahajjatan da za’a fara dauka duk Nigeria sune Alhazan Karamar-hukumar mulkin kaura-namoda jihar zamfara.
.
Ayau ne Alhazan Karamar hukumar mulki ta kaura namoda zasu fara tashi zuwa kasa mai tsalki, shugaban karamar hukumar mulki ta kaura-namoda, sannan kuma (shugaban commitin zirga-zirgar Alhazai) karkashin jagorancin “AMIRULL-HAJ” na jihar zamfara
ALHAJI LAWAL M.LIMAN (GABDON-KAURA) da kuma, maimartaba
Sarkin kiyawan kaura
Alhaji Ahmad muhammad Asha
Sun yi taron bankwana da Alhazai, a sakatariyar karamar hukumar mulki ta kaura-namoda.
.
Maigirma chairman Gabdon kaura, kuma (shugaban commitin zirga-zirgar Alhazai na jihar zamfara) alokacin ya “shawarci ma hajjata dasu du kufa wurin yiwa Kaura, Jihar zamfara, da Nigeria, baki daya Addu’ar samun zama lafiya da kwanciyar hankali” ya kuma shawar cesu dasu nace wurin neman gafarar Allahu (S.W.T)
.
Shima Maimartaba Sarkin kiyawan kaura, Alh Ahmad muhammad Asha, Alokacin ya Roki Allah yasa Alhazan suyi hajji kar6a66iya, ya kuma roki Allah yasa suje lafiya su dawo lafiya, sannan ya shawarcesu da sudu kufa wurin yiwa kawunansu Addu’a, da ma kasa baki daya, da kuma rokon Gafarar Allahu (S.W.T)
.
Bayan kammala wannan jawabin bankwana, shugaban karamar hukumar mulkin kaura-namoda kuma (shugaban kwamitin zirga-zirgar Alhazai) Hon. Gabdon kaura
Shida Manyan jami’an gwamnatinsa, sun raka Alhazan, zuwa Gusau headqotar jihar zamfara, domin Tabbatarda Kowane Alhaji ya shiga motar da zata dauke su Daga gusau, zuwa Jihar Sokoto, domin shiga jirgi zuwa kasa mai tsalki, kuma duk wannan karamci da maigirma shugaban karamar hukumar mulkin kaura Lawal M.liman ya nuna ga Alhazai bai rasa nasaba da irin yanda ya saba taimako ga talakawansa.
.
Tabbas; yanda Alhazan Kaura suka zamo cikin nutsuwa, da kamala, lokacin wannan zirga-zirga ya nuna cewa sun cancanta da wannan matsayi da aka basu na zama Alhazai na farko duk Nigeria, da zasu fara sauka kasa mai tsalki.
.
muna rokon Allah yasa Alhazan mu su je lafiya, su dawo lafiya, su kuma yi hajji kar6a66iya.

Advertisements