Buhari Zai Kirkiro Kotun Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Domin Hukunta Barayin Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta soma shirin kirkirar kotun musamman domin sauraren shari’ar al’amuran da suka shafi rashawa da makamantansu, a shirin da ake na yakar rashawa da cin hanci a kasar nan.
Kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudirin yin hakan ne domin samun mafita ga matsalar rashawa a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa har shugaban kasa ya kammala shirin mika kudirin na gina kotun hukunta barayin gwamnati ga majalisa.
Idan ba a mance ba rahotanni sun bayyana a kwanakin baya na cewa shugaba Buhari yana neman alkalai marasa tsoro da zai ba su ragamar sauraren shari’ar barayin gwamnatin.
Haka kuma bincike ya nuna cewa za a kirkiri kotun ne a jihohi 36 da ke fadin kasar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Advertisements