Gwamnatin Tarayya Ta Soke Ofishin ‘First Lady’
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har zuwa yanzu ba a baiwa uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari damar gudanar da harkokin ofishin matar shugaaban kasa da aka fi sani da ‘First Lady” ba. Inda yanzu haka aka sauyawa ofishin suna zuwa ofishin matar shugaban kasa, sannan gwamnatin tarayya ta kara da bayyana cewa uwargidan shugaban kasan A’isha Buhari zuwa yanzu za ta dinga kula da al’amuran da suka shafi mata da matasa ne a kasar nan.
Haka kuma gwamnatin tarayyar ta musanta batun da wasu kafafen yada labarai suka yi ta yadawa na cewa matar Buharin ta koma ofishin na ‘First Lady’ da ke Villa.
Malam Garba Shehu, wanda shine mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa ofishin matar shugaban kasar na zamanin Buhari zai bambanta da gwamnatin baya, inda ya ce batun uwargidan shugaban kasa ta sanya kanta cikin al’amuran rijiyoyin man fetur da yin lasisi ya wuce