Kotu Ta Dakatar Da Gwamna El-Rufa’i Daga Rusau, na gine gine
.
Wasu da suka mallaki gii a filin makaranta da ke kusa da titin Constitution a cikin garin Kaduna sun mika gwamnatin jihar ga kotu kan sanyawa gine ginensu maki da ta yi domin rusa su.
Majiyarmu ta Premium Times ta rawaito a makon da ya gabata cewa gwamna Nasir El-Rufa’i ya gargadi mazauna wannan yankin kan rusa gine gine da din da zai yi a wannan yanki.
.
Amma bayan mako guda sai wasu mutane gome daga cikin wadanda suka mallaki gini a wannan yanki suka kai kukan su kotun daukaka kara karkashin jagorancin mai shari’a B.U Sukola domin dakatar da gwamnan daga rusau din.
Don haka ne bayan sauraren koken, mai shari’a B.U Sukola ya dakatar da gwamnatin jihar da sauran ma’aikatun da suke da alhakin yin rusau din daga rusa ginin wadanda suka kawo kukan. Sannan kuma an dage sauraren karar har zuwa 26 ga wannan wata
.
Wadanda suka kai karar sun hada da Dan Kaduna Trade Ltd, Na’Atta Communication & General Enterprises Ltd, Fashum Company Nigeria Ltd, Bashir Zuntu, Renyam Nigeria Ltd, Dr. Baba Usman, Abubakar Mustapha, Bonat Charles, Vincent U. Nnaegbuna da Bulus D. Kwande
.
koya kuke kallon wannan kiki-kaka data kunno kai tsakanin Gwamna Elrufa’i da wadannan mutane??

Advertisements