Namiji Ya Yi Shigar Mata Har Tsawon Watanni Takwas Yana Aikin Gida Ba Tare Da An Gane Ba
Ba karamin abin al’jabi ba ne a ce iyalan wani gida da suka dauki dan aikin da ke kula da yara ciki har da ‘yan matan da suka soma tasowa har tsawon watanni takwas, amma bas u san cewa namiji ba ne yay i shigar mata.
Kamar yadda majiyarmu daga shafin sadarwa na Twitter mai amfani da suna Trebble_D ta rawaito, asirin mutumin bai tashi tonuwa ba, har sai lokacin da yay i maigidan sata har ta kai ga an mika shi wurin jami’an ‘yan sanda domin gudanar da bincike.
A sakamakon mika shi wurin jami’an ‘yan sandan ne masu gidan suka gano cewa ashe da namiji suke tare har kusan shekara guda amma bas u sani ba

Advertisements