GA SHARHIN JARIDUN NIGERIA
.
1-THE PUNCH
Sakataren majalisar dinkin duniya (Mr Bank Moon) yana cigaba da ziyarar wuni 2 a NIGERIA inda jiya yayi taro da gwamnoni yau kuma zai gana da kungiyoyin fararen hula dagabisani ya gana da PMB@
.
2-THE NATION
Rundunar sojojin sama ta NIGERIA takai hari kan wasu manyan motoci 2 kirar tirela da suke daukeda kayan yan boko haram akan iyakar nigeria da kamaru, inda aka tarwatsasu@
.
3-LEADERSHIP
Shugaba BUHARI ya bukaci kungiyar lauyoyi su kawo sauyi a harkar shari‘ar NIGERIA a sakonsa daya mika musu a lokacin babban taronsu na shekara shekara da suka sabayi@
.
4-VANGUARD
Jam,iyyar APC ta kushe zababben gwamnan jahar EKITI (Mr Ayodele Fayoshe) inda tace watanni 10 da hawansa kan kujerar gwamnan jahar, amma bazai iya nuna aiki 1 tak da yayiwa al‘ummar jahar ba@
.
5-NATIONAL MIRROR
Tsohon shugaban nigeria (Olusegun Obasanjo) yace jama‘ar nigeria sunyi dacen zaben shugaban kasa BUHARI ya kara da cewar su goya masa baya tareda tayashi addu‘a@
.
6-THE PUNCH
Rundunar sojojin kasa ta nigeria karkashin jagorancin (Major T.Y Buratai) ta dawoda sojojin kimanin 2800 wanda aka kora daga aiki saboda an zargesu da kin zuwa yakida boko haram@
.
7-DAILY TRUST
Nigeria ta samu karfin wutar lantarki NEPA daya kai megawas dubu 4,720 inda yanzu haka ake shan wutar (18-huors) a manyan birane da kananan garuruwan nigeria a cewar daraktan wutar (Mr Godnos Agali)@
.
8-COMPLATE SPORT
Kungiyar kwallon kafa ta nasarawa united ta karya tarihin da kano pillers take kai daci 2 v 1 a filin wasa na abacha dake birnin KANO bayan ta kwashe shekaru 12 ba‘a cita a wasan gidaba@

Advertisements