LABARAI A TAKAICE HAR GUDA ASHIRIN 20
.
1- Yan Majalissar Dadtawa na Jam’iyar PDP sun
ki Amincewa Majalissar ta tuhumi shugaban
hukumar EFCC Ibrahim Lamorde bisa zarginsa
da karba tare da Almundaha da kudin da ya kai
Naira Tiriliyon 1tr
.
2- Wasu Tsofin Manyan Hafsan sojojin nigeria
tare da masu bada shawara akan harkar tsaro su
19 za’afara tuhumarsu akan kudin siyan
Makame tun daga shekara ta 2007
.
3- Hukumar zabe ta INEC a nigeria ta fidda
ranakun 2 da 7 ga watan September da za’asake
yin rigistar masu zabe a jahoshon Kogi da
Bayelsa sakamakon zaben Gwamnoni da za’ayi a
jahoshin biyu
.
4- Babban Hafsan Sojojin nigeria MJ Tukur
Brutai An fara shiga Daji dashi dan Yakar
kungiyar Boko haram akasin abinda tsofin
manyan hafsan sojojin nigeria basuyi ba abaya
.
5- Tsohon gwamnan jahar Kaduna Alh Balarabe
Musa Yace idan har Buhari da gaske yake wajen
yaki da cin hanci da rashawa to ya tuhumi
Gwamnatinsa ta baya lokacin mulkin soja a
1985
.
6- Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA
ta fara tuhumar wani ma’aikacin jirgin saman
Arik Airline dan Asalin nigeria da aka kama da
Miyagun kwayoyi mai dauke da nauyin
kilogiram 2.7 a filin jirgin sama na Murtala
Muhd dake Lagos zai kaisu kasar ingila
.
7- Shugaban kasar nigeria Muhammadu Buhari
yace Gwamnatocin da suka shude tun lokacin da
ya bar mulkin a 1985 sun nuna rashin imani da
tafka ha’inci musamman ga tallafin Manfetir da
gwamnati ke bayarwa
.
8- Shahararen dan wasan nan na fina finan
kasar Japan Jakie chan zai kawo ziyara nigeria a
watan Gobe dan ganawa da buhari tare da wasu
masu shirya fina finan kasar
.
9-Gwamnan jahar Imo Rochas Okorocha yace
da shi da shuwagabannin Al’ummar kabilar Igbo
zasu hada kai dan marawa buhari baya
.
10- A jiya talata 25-8-2015 Yan Matan
Makarantar Garin Chibok dake jahar Borno da
Yan boko haram suka Sace sun cika kwanaki dari
biyar 500 da sacewa
.
11- Kamfanin dake samar da wutar lantarki ta
KEDCO yace zai raba Na’urar dake rarraba wuta
a gidaje (Metres) har guda 100,000 ga mutane
390,000 a jahoshin Kaduna,Kebbi,Za
mfara,Sokoto
.
12- Gwamnan jahar Rivers Mr Nyeson Wike ya
zargi tsohon gwamnan jahar Mr Rotimi
Ameachi da ranto kudi a babban bankin nigeria
CBN har biliyan 3b dan aikin Gona amma ya
karkatar da kudin a lokacin yakin neman zabe
.
13- Shugaban kasar Faransa Francious Hollande
yace zai Gayyaci wasu kashashen duniya zuwa
kasar nigeria dan tattaunawa da shugaban kasar
ta nigeria Muhammadu buhari bisa yadda za’a
yaki Boko haram
.
14- Gwamanan jahar Jigawa Alh Muhammadu
Badaru ya mikawa Majalissar jahar sunayen
Wadanda yake so ya nada a matsayin
Kwamanshinoni 13 tare da masu bashi shawara
12 dan tantance su
.
15- Hukumar EFCC ta musanta zargin da
Majalissar Dadtawa takewa shugaban hukumar
ta EFCC ibrahim Lamorde da Al’mundaha tare
da karbar toshiyar baki har Tiriliyon daya 1tr
.
16- Shugaban kasa Muhammadu buhari ya soke
Ofishin Matarsa Aisha buhari sabida babu
ofishin a kudin tsarin mulkin kasa
.
17- Wata babbar kotun tarayya a jahar Kano tayi
Watsi bisa karar da Sanata Bashir Lado ya shigar
akan zaben da akayiwa Sanata Rabiu Kwankwaso
.
18- Tsohon Gwamnan jahar Jigawa Sule lamido
Ya rabawa Matasa A jahar kayan kallo Talabijin
TV dan suna kunnawa suna ganin irin aiyuka da
tsohuwar gwamnatinsa ta yi a lokacin mulkinsa
.
19- Ana tunanin tsohon gwamnan jahar kaduna
lokacin mulkin soja MJ Hamid Ali zai Maye
Gurbin Shugaban hukumar EFCC ibrahim
Lamorde
.
20- Wani dan kasuwa Mai Suna Mr Muyiwa
Owolabi ya bukaci wata Kotu a Birnin Ado Ekiti
na jahar Ekiti Ta raba musu Aure shida matarsa
Mrs Tinuola Bisa zargin ta da Iskanci ta hanyar
Sadarwar zamani(social Media) irinsu facebook
Whatsapp Twitter inda suke iskanci tare da tura
hotunan Batsa
Menene Ra’ayinku? Ko kuma wani Labari ne yafi
Jan hankalinku?
Ya Allah kasa Mudace duniya da Lahira AMEEN

Advertisements