Barayin gwamnatin Nigeria sun fara amai
.
*Ma’aikata ‘masu kazaman kudi’ suna rige – rigen sayar da kadarorinsu
Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa ta kasa (ICPC) ta fara sanya barayin gwamnati amayo dukiyar da suka mallaka ta haramtacciyar hanya, bayan da gudumarta ta fara sauka a kan ma’aikatan gwamnati da suka tara kazamar dukiya fiye da samunsu.
Hukumar ta kwato gidaje da filaye 24 daga wasu ma’aikatan gwamnati uku, inda daya daga cikinsu ya mallaki gidaje da fulotai 18 masu dan karen tsada.
Wasu takardu da suka fito daga ofishin Shugaban Hukumar ICPC, Mista Ekpo Nta, mai taken ‘Sanarwar kwace kadarorin da za a iya dauka da wadanda ba za a iya dauka ba, bisa dogaro da sashi na 45 (4) (a) – (b) na dokar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan da suka jibinci haka ta shekarar 2000,’ ta bayyana cewa hukumar ta kwace kadarorin wasu ma’aikatan Hukumar Neja-Delta su uku.
ICPC ta ce kadarorin da aka kwace sun fi “karfin albashin ma’aikatan da lamarin ya shafa.”
Takardar mai dauke da kwanan wata 11 ga Agusta, 2015, ba ta bayyana mukaman jami’an ba, amma wata majiya ta ce, jami’an uku dukkansu manyan akantoci ne a ma’aikatar, wadda take daya daga cikin ma’aikatun da Hukumar ICPC ke gudanar da bincike a kansu a halin yanzu.
Jami’an Ma’aikatar Neja-Delta da aka ambata a takardar sun hada da Poloma Kabiru Nuhu da Mangset Longyl Dickson da kuma Daniel Obah.
Shugaban Hukumar ICPC ya ce shawarar kwace kadarorin za a tura ta ga hukumomin da ke rajistar filaye da sauran sassan da ke daukacin jihohin kasar nan da kadarorin suke.
Ya ce, “Hukumar tana bincike kan wani lamari da ya shafi wasu ma’aikatan Ma’aikatar Neja-Delta da suke da wasu kadarori da suka mallaka da hukunar ke da yakinin cewa bisa binciken da take yi kadarorin da wadannan mutane da ke aiki a Ma’aikatar Neja-Delta suka mallaka sun wuce samunsu bisa lura da albashi da hakkokinsu da sauran hanyoyin samunsu. Don haka hukumar tana sanar da daukacin jama’a cewa dukkan filaye da gine-ginen da wadannan ma’aikata suka mallaka kuma aka bayyana su a nan an kwace.”
A cewar Shugaban Hukumar ta ICPC, daya daga cikin ma’aikatan wato, Nuhu, yana da fili mai girman hekta 10 da takardar mallaka a Kuje da ke yankin Abuja da aka kiyasta kudinsa a kan Naira miliyan 50. Ya kara da cewa wannan ma’aikaci yana da gidan kasaita da ba a kammala ba a rukunin gidaje na Diamond Estate da ke Apo, Abuja, da ya kai Naira miliyan 90. Mista Nta ya kuma ce Nuhu yana da fulotai 16 wadanda duka suke da takardar mallaka a sassa da dama na Gwagwalada, Abuja.
Wani ma’aikacin da ke cikin jerin sunayen na ICPC, shi ne Dickson, wanda aka ce yana da fuloti a gundumar Kubwa, Cadastral Zone, Abuja, fulotin da aka yi masa kudi kan Naira miliyan bakwai. Ma’aikaci na uku Obah, an ce ya mallaki fulotai a Abuja da Fatakwal ta Jihar Ribas.
Mista Nta ya ce, Obah yana da gidan kasaita mai dakunan kwana hudu a Gundumar Karsana ta Kudu da ke Abuja da aka yi masa kudi kan Naira miliyan 60, sai kuma fuloti a Ozuoba da ke Fatakwal ta Jihar Ribas.
Sauran fulotan da aka ce na Obah ne sun hada da na unguwar Umuodili Odubo da ke Jihar Ribas da ya kai Naira miliyan 16 da rabi; sai na Olipobo Rumuekini Layout, a karamar Hukumar Obio Akpor da aka yi masa kudi kan Naira miliyan 18 da wani fuloti a rukunin gidaje na Libingstone Estate Umuogodo, Igbo Etche a karamar Hukumar Obio Akpor duk a Jihar Ribas.
Wata majiya ta ce tun a watan Yuli Gwamnatin Tarayya ta umarci ICPC ta binciki ma’aikatan gwamnati ‘masu kazamen kudi’ da suke da dimbin kadarori da dukiyar da ake ganin na almundahana ne. Rahotanni sun ce Hukumar ICPC ta haska tocilarta a kan ma’aikatan gwamnati da suka mallaki kadarorin da ake tababar halaccinsu a Birnin Tarayya Abuja.
Majiyar ta ce an umarci jami’an gano dukiya da kwatowa na Hukumar ICPC su gayyaci wadanda ake zargin don yi musu tambayoyi tare da kwato duk wata dukiyar da aka samu ta haramun da suka mallake ta. Kuma an ce ICPC ta kara karfin wannan sashi da karin ma’aikata don tabbatar da nasarar wannan yunkuri.
Ko a ranar Larabar makon jiya sai da Odita Janar na Tarayya Mista Samuel Ukura ya amince a kwato kimanin Naira biliyan 183 na kudin da aka ware domin bunkasa yankin Neja-Delta wadanda ake zargin an karkatar da su zuwa wasu manufofi na daban.
Mista Ukura wanda ya bayyana haka a cikin rahotannin binciken kudi uku na musamman da ya aike wa Akawun Majalisar Dokoki ta kasa Malam Salisu Maikasuwa, ya ce an gano adadin ne a cikin binciken shekara-shekara da ofishinsa ya gudanar tsakanin shekarar 2008 da 2012.
A cewarsa an biya Naira biliyan 70 da miliyan 400 a matsayin kudin fara ayyuka da dama ga wadanda ba su je wuraren da za a gudanar da ayyukan ba, yayin da aka kara kasafin Naira bikiyan 90 da miliyan 400 don ayyukan yau da kullum ba tare da amincewar hukumomin da hakan ke wuyansu ba.
Kuma ya ce, an cire harajin Naira biliyan 10 ba tare da gabatar da takardar cewa an mika kudin ga Hukumar Tara Haraji ta kasa (FIRS) ba, sai Naira biliyan biyar da miliyan 800 da aka biya ’yan kwangila alhali ba su yi aikin komai ba, ko kuma sun fara suka bari da kuma Naira biliyan daya da miliyan 200 na harajin da aka ki cirewa daga ’yan kwangilar.
Mista Ukura ya ce an kuma sauya wa wasu Naira biliyan uku da miliyan 100 asusu zuwa asusun da doka ba ta amince da shi ba, sai Naira biliyan daya da miliyan 700 na kudin da aka ba ma’aikata su je aiki da ba a bayyana irin aikin ba, yayin da aka karkatar da Naira miliyan 785 daga cikin Naira biliyan daya da miliyan 100 da aka ware don sayen kujeru da teburan zama ga wasu makarantu a Jihar Delta. Ya ce kudin da aka ware don sayen kujeru da teburan an nuna an sayo su, amma ziyarar ganin kwaf da ofishin Odita Janar ya gudanar ya gano ko kujera daya ba a ba wata makaranta a wannan lokaci da ake magana ba.
Matakin da Hukumar ICPC ta dauka na kwato kadarorin ma’aikata ‘masu kazaman kudi,’ dai ya sanya ma’aikata rige-rigen sayar da zababbun gidaje da motocin kasaita da suka mallaka don kauce wa rasa kadarorin ga shirin Shugaban kasa Buhari na yaki da almundahana.
Wata majiya ta ce wasu ma’aikatan gwamnati sun fara matsa wa dillalan gidaje a Birnin Tarayya, Abuja kan su taimaka wajen sayar musu da gidajensu, yayin da masu dukiya suka fara kwasar garabasar wannan dama. Majiyar ta ce cinikin gidaje da filaye a Abuja ya karu da kashi 30 cikin 100 bayan hawan wannan gwamnati gadon mulki, kuma cinikin ya dada karuwa sosai a makonni hudu da suka gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a tsakanin Janairu da Mayun bana.
Dillalan gidaje a Abuja sun shaida wa majiyar cewa karuwar sayar da gidaje da filayen ba za ta rasa nasaba da binciken jami’an gwamnati da kuma kwace kadarorin barayin gwamnati da ICPC ta fara ba.
Dillalan gidaje sun ce wasu daidaikun mutane sun fara tuntubar dillalan gidaje suna neman su taimaka wajen sayar musu da gidajensu. “Binciken da ake yi ya jawo tashin hankali. daidaikun mutane sun shiga tuntubarmu suna neman mu taimaka mu sayar musu da gidajensu. Ba za su gaya mana cewa suna kokarin kauce wa bincike ne ba, amma mafi yawanmu mun san wannan ne abin da suke guje masa,” inji wani dan kungiyar Dillalan Gidaje ta Najeriya (REDAN) da ya nemi a sakaye sunansa.
Daga aka tuntubi tsohon Shugaban kungiyar REDAN, Cif Olabode Afolayan ya ce bangaren gidaje ya samu karuwar ciniki a ’yan makonnin nan. Ya ce, “A ’yan watannin da suka gabata babu wata harka ko kadan. Tsakanin Janairu da Mayu, komai ya tsaya cik. Amma abin da muke gani a yanzu harka ta bude kuma muna sa ran komai zai daidaita.”
Da aka tambaye shi ko sayar da gidajen na da alaka da yaki da cin hanci da rashawa da Shugaban kasa ya kaddamar a yanzu da kuma fara hukunta barayin gwamnati, sai ya ce: “Wannan yana iya zama gaskiya.”
Ya kara da cewa masu harkar gidaje ba su da wata damuwa domin su ba ma’aikatan gwamnati ba ne, suna sayar da gidajensu ne. Amma masu gidajen da suka fara sayar da gidajensu a yanzu me yiwuwa dalilin na da alaka da abin da muke gani a yanzu, wato yadda gwamnati take kokarin magance matsalar almundahana.”
Shugaban kungiyar REDAN mai ci Mista Oguchukwu Chime ya shaida wa manema labarai cewa ana sa rai sayar da gidaje ya karu, inda ya ce ma’aikatan gwamnatin da ta gabata da dama za su iya sayar da kadarorinsu a yanzu.
Ya ce, “Ba mu gudanar da wani nazari a yanzu ba. Amma abu ne da ake sa rai. Wasu jami’an gwamnatin da ta gabata ba za su so ci gaba da zama a Abuja haka kawai ba, wannan abu ne da ba zai yiwuwa ba. Wadanda suke zuwa tare da sabuwar gwamnatin su ma suna ta dawowa Abuja kuma suna son sayen gidaje. Su kuma na gwamnatin da ta gabata za su so sayar da gidajensu ko don su warware wasu bukatunsu ko don su bar Abuja.”
Shugabar kungiyar ta REDAN reshen Abuja Misis Binta Ibrahim, ta ce ba za ta iya jingina rige-rigen sayar da gidajen da mutane ke yi kan binciken da ake yi ba, amma ta lura an samu karuwar masu sayar da gidajensu. “Mutane suna saye, kuma sayar da gidaje ya karu bayan zuwan wannan gwamnati, musamman a ’yan kwanakin nan. Sai dai ba zan iya cewa wadanda suke sayar da gidajensu ma’aikata ne da suke kokarin kauce wa binciken almundahana da Shugaban kasa ke yi ba,” inji ta.
Tuni kungiyar Manyan Ma’aikata ta Najeriya (ASCSN) ta rubuta wa Hukumar ICPC tana neman bayani kan ma’aikatan gwamnati da suka mallaki kadarori na biliyoyin Naira, inda ta ce ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ba ta bayanan ma’aikatan da aka gano sun yi amfani da mukamansu wajen sayen gidaje da kadarori a Abuja da Legas da sauran biranen kasar nan.
Babban Sakataren kungiyar ASCSN, Bashir Lawal ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da manema labarai suka nemi jin ta bakinsa kan rahoton da ICPC ta fitar cewa ma’aikatan gwamnati da dama ne ake zargi da mallakar gidaje da fulotai masu tsada na gani a fada.
Lawal wanda ya ki cewa komai kan rahoton ya ce, kungiyar tana bukatar ta ga rahoton na ICPC kafin ta furta matsayinta a kai.
Ya ce “Akwai bukatar mu tabbatar wadanda suka mallaki kadarorin shin da gaske ma’aikata ne; a lokuta da dama ana shigo da wasu mutane cikin aikin gwamnati; shin ana magana ne kan mutane da ’yan siyasa suka shigar da su cikin aikin gwamnati ko kuwa ma’aikatan gwamnati na gaskiya. Mun nemi bayani daga ICPC, lokacin da muka samu bayanin ne za mu mayar da martani yadda ya kamata.”

Advertisements