Hajjin bana: Akwai tababa kan matsayin Amirul Hajji A Nigeria:
:
A sakamakon sanarwar da gwamnatin tarayya ta bayar na soke tawagar gwamnatin tarayya a aikin hajjin bana, an samu rudani dangane da matsayin Amirul Hajji wanda shi ne a ka’ida yake jagorantar tawagar ta gwamnatin tarayya a duk shekara. Tun da gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar soke tawagar, Aminiya ta yi kokarin samun karin bayani daga Kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, amma bai dauki wayarsa ba lokacin da aka buga masa, kuma bai bayar da amsar sakon tes da aka tura masa ba. Shi ma shugaban hukumar Alhazai ta kasa, Abdullahi Muhammad Mukhtar, bai amsa wayar da aka buga masa ba, haka shi ma kakakin hukmar Alhazan, Uba Mana. A karshe dai duk kokarin da Aminiya ta yi na samun karin bayani ya ci tura. Sai dai kuma wata hira da sashen Hausa na BBC ya yi da Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a farkon makon nan, ya bayyana cewa shi kam ba shi da masaniya ko soke tawagar gwamnatin tarayya da aka yi ya shafi kujerar Amirul Hajji, kuma ya yi tsokaci game da dalilin da ya sa aka soke tawagar gwamnatin tarayya a aikin hajjin bana. Ga yadda hirar ta kasance:
Tambaya: Me ye gaskiyar labarin cewa gwamnati ba za ta kara tura tawagar musamman ba zuwa aikin hajji?
Malam Garba Shehu: A’a, ba gaskiya ne ya ce ba za ta kara turawa ba. Abin da ya ce a wannan shekara gwamnati ta tsakiya, gwamnatin tarayya a nan Abuja, ba za ta tura tawagar gwamnati ba a wannan shekarar. Amma ma’aikatan lafiya da ma’aikatan hurdan jakadanci na kasa-da-kasa da ma’aikata masu kula da jin dadin alhazai na Najeriya ba abin da za a rage.
Tambaya: Domin haka za a iya cewa ba za a tura Amirul Hajji ba, wanda shi ne yake jagorantar wakilan gwamnatin tarayyar Najeriya?
Malam Garba Shehu: Eh, to ban sani ba ko Amirul Hajji na ciki, amma ina so na tabbatar maka da cewa jihohin suna da damar su yi yadda suke so. Ita gwamnatin tarayya ba ta da tawaga bana, sai dai ma’aikata wadanda aka saba wanda hakkin gwamnati ne ta kare duk dan Najeriya da yake kasar waje yake aikin hajji. Duka za a kyautata wa mutane kamar yadda aka saba. Amma tawaga wadda yake matsayinta dama ba da shawara a kan wannan aikin hajji, ya ce a’a, a dakata tukuna.
Tambaya: Amma ba ka ganin kasancewarsa kamar kwamiti ne na ba da shawara galibi kwamitin ba da shawara sukan sa ido kan j=ami’an da ke kula da alhazai a can, wadanda za su ba da shawarwari kan inganta aikin hajji. Yanzu hakan na nufin haka alhazan za su je babu mai kula da su ne?
Malam Garba Shehu: A’a, ba haka ba ne. Duk ma’aikatan gwamnati ba wadda ba zai yi aikinsa ba. Kuma ka san akwai ma’aikatu na huldar jakadanci a can, ma’aikatar harkokin waje, ma’aikatar lafiya duk ga su nan. Babu wanda aka hana, kowa zai yi aikinsa. Gwamnati ta san hakkinta a kan jama’a. Za ta aiwatar da shi. Ba za ta yi sakaci ko sassauci a kan kare hakkin ’yan Najeriya ba.
Tambaya: Wadansu na iya ganin irin wannan mataki zai nuna kamar gwamnati ba ta damu da aikin hajji ba wanda yake daya ne daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. Ba ka jin za a iya cewa ba ku damu da addini ba?
Malam Garba Shehu: A’a idan ka yi haka ba ka yi adalci ba. Saboda ita wannan tawaga idan ka duba dokar da ta kafa hukumar alhazai ba ta da matsaya a ciki, a tsarin mulki na Najeriya ba ta da matsaya a ciki. Ita kanta gwamnatin Saudiyya ba ta da wani matsayi da suka ajiye wa tawagar kasa-da-kasa. Alfarma ake yi a kyautata wa mutane. Halin da tattalin arziki da ake ciki a wannan shekarar a Najeriya watakila sai a ji tausayi a yi adalci ga kasa na wannan dan karamin lokaci. Kafin shi Shugaba Muhammadu Buhari ya tattare kwaryar kafin da ta fashe a hannu, sai ya mika wa mutane. Hakki ne na dan Najeriya a matsayinsa na alhaji a duk idan yake, babu abin da za a rage, sai ma a kyautata abin da ake yi a baya.
Tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ne dai ta nada Abdullahi Muhammad Mukhatar a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta kasa, bayan kammaluwar wa’adin tsohon shugabanta Muhammad Musa Bello, amma Majalisar koli ta Addinin Musulunci da ke karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar,ta rubuta wa Majalisar dattijai takardar korafi inda ta bukaci kada ta amince da nadin Abdullahi Mukhtar a matsayin shugaban hukumar domin kuwa a fahimtarta ba a bi ka’ida ba kafin a mika sunan nasa. Daga bisani dai Majalisa ta amince da nadin Abdullahi Mukhtar.
A halin yanzu jita-jitar da ake bazawa , wadda Aminiya ta yi kokarin fayyacewa amma lamarin ya gagara, ita ce, akwai alamun cewa danganta tsakanin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da Shugaban hukumar Alhazai ta kasa Abdullahi Mukhtar ta yi tsami, an fahimci haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar aikin Hajji da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa ya daga ranar fara tashin alhazan kasar nan da ake sa ran za a yi a ranar 18 ga watan nan zuwa ranar 23 ga wata, domin kamar yadda ya ce, an sanya wancan ranar ne ba tare da an tuntube sa ba, a matsayinsa na Amirul Hajji na dindindin sai dai kawai ya ji a labarai. Haka kuma Sarkin Musulmin ya canja wurin da za a yi bikin tashin farko daga Yola zuwa Kaduna.Sannan kuma ya nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin Amirul Hajji na wannan shekarar.
Gwamnatin tarayya dai ta ce a sakamakon soke tawagar da ta yi za ta samu rarar kudi Dala Miliyan daya da kuma Naira miliyan 30 da za ta kashe a cikin gida Najeriya wajen shirye-shiryen tafiyarsu. Kamar yadda kakakin Shugaban kasa Garba ya nuna, gwamnati ta dauki wannan matakin ne a kokarin da take yi na taka-tsantsan wajen kashe kudi.

Advertisements