Yunkurin Murde Lamurde ya raba kan majalisa
.
.
Sanata Bukola Saraki da Ibrahim LamurxeYunkurin binciken da Majalisar Dattawa take yi kan zargin da ake yi wa Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Ibrahim Lamurde na karkatar da Naira tiriliyan daya da hukuma ta kwato daga barayin gwamnati ya raba kan majalisar.
Kwamitin Bin ka’ida da Karbar Koke-Koken Jama’a na majalisar ya fara gudanar da bincike kan zargin ta hanyar fara sauraren shaida daga bakin wanda ya rubuta takardar zargin Mista George Uboh a shekaranjiya Laraba.
Shugaban kwamitin Sanata Samuel Anyawu ya kori Daraktan Shari’a na Hukumar EFCC Chile Okoroma da lauyan Lamurde Barista Osuagwu Ogbochukwu a yayin zaman kwamitin.
Kafin nan Shugabannin Sanatocin Jam’iyyar PDP sun cire kansu daga binciken inda suka ce ba su da wata masaniya kan akwai takardar kuka da ke zargin EFCC.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Sanata Godswil Akpabio da Sanata da Sanata Abiodun Olujimi da Sanata Emmanuel Bwacha da Sanata Philip Aduda ce ta bayyana haka.
Masu lura da al’amuran siyasa suna ganin wannan wani yunkuri ne na murde Lamurde domin binciken Hukumar EFCC bai tashi ba, sai bayan da hukumar ta gayyaci uwargidan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki don amsa tambayoyi kan almundahana. Magoya bayan Sanata Saraki sun bayyana gayyatar matarsa Misis Toyin Saraki a matsayin siyasa. Saraki yana fuskantar matsala da shugabannin Jam’iyyar APC game da yadda aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar bayan da jam’iyyar ta bukaci a zabi Sanata Ahmad Lawan daga Jihar Yobe.
Yana kuma fuskantar matsala bayan da ya ki bin umarnin jam’iyyar na ba wasu sanatoci ciki har da Sanata Lawan mukamai domin kawo karshen matsalar da ta taso.
bangaren da ke goyon bayan Sanata Ahmad Lawan da ake kira da The Unity Forum, ya zargi Sanata Bukola Saraki da keta doka a binciken na EFCC.
bangaren ya ce gayyatar da aka yi wa Lamurde haramtacciya ce kuma ta saba wa dokokin majlaisar, inda ya ce babu wata shaida da ta nuna an mika koken Uboh ga zauren majalisar.
Yayin da bangaren Saraki ya tsaya kai da fata cewa binciken yana kan ka’ida bangaren Lawan na ganin binciken a matsayin haramtacce da ya saba wa tsarin mulki.
Sanarwar da The Unity Forum ta fitar dauke da sanya hannun Sanata Ahmad Lawanb da Sanata George Akume da Sanata Abu Ibrahim da kuma Sanata Barnabas Gemade ta ce gayyatar Lamurde ya saba wa dokokin gudanar da majalisar.
“A ingantaccen tsari na tafiyar da majalisar takardar koke kan zo ne ta hannun ko dai Sanata ko dan Majalisar Wakilai. Kuma bayan an karbi koken wakilan za su sanar da shugaban majalisa sannan a gabatar da shi ga zaman majalisa, inda shugaban zaman zai gayyaci Sanata ko dan Majalisar Wakilan ya gabatar ga zauren majalisa, inda hakan kan say a zamo ya shiga hannun jama’a.”
Sun kara da cewa: “Bayan wannan ne sai shugaban zaman majalisar ya mika koken ga kwamitin da ya dace domin dubawa sannan ya maido wa zauren majalisar. Amma duk ba a yi haka a kan wannan batu ba.”
Sun ce ba a mika koken Uboh ga Majalisar Dattawa ba kafin tafiya hutu ranar 13 ga Agusta ba, inda suka ce Doka ta 41 (1) da ke cewa Sanata ne kawai zai gabatar da takardar koke dauke da sunansa a kai. Kuma sun kawo Doka ta 41 (2) inda suka ce: “Sanatan da zai gabatar dab koke zai yi bayanin takaitaccen abin da bangarorin biyu suka ce da yawan wadanda suka sanya hannu a hade da ita da abin da ake zargin an aikata tare da karatun abin da ake roko a cikin wannan koke.
bangaren Lawan ya karfafa hujjarsa da Doka ta 41 (3) da ke cewa: Dukkan koke-koke da aka gabatar da su ba tare da an bincika ba, kuma aka gabatar da su a kan teburin majalisar. Za a mika wa kwamitin sauraren koke-koken jama’a ne. “Don haka kungiyar Unity Forum na Majalisar Dattawa ta goyi bayan matsayin da wasu sanatoci suka dauka na a jingine binciken Lamurde domin ba a bi ka’ida ba. Ba ma goyon bayan wannan bincike. Haramtacce ne ya saba wa tsarin mulki domin ba a bi doka ba,” inji su.
Sai dai bangaren Saraki sun ce sun dogara ne da oda ta 103 ta dokar gudanar da majalisar wajen wannan bincike.
Shugaban Kwamitin Labarai na Majalisar Sanata Dino Melaye, wnda har wa yau kakakin bangaren Saraki ya ce sun kuma dogara da sashi na 88 da 89 na tsarin mulkin Najeriyaa da ke cewa, “Majalisar Dattawa tana da ikon bayar da umarni ko ta sa a yi bincike a kan kowane al’amari.”
Ya kara da cewa takardar koke tana iya zuwa kai-tsaye ga Shugaban Majalisar ko wani sanata don mikawa ga zauren majalisar don haka bai kamata a nemi bata sunan majalisar kan cewa majalisar ta gayyaci Lamurde ne kan takardar koken da ba ta bi ka’ida ba. “…Takardar koke zuwa ga majalisar kan iya zuwa kai-tsaye ga Shugaban Majalisar ko ta hannun daidaikun sanatoci domin gabatarwa ga majalisar,” inji shi.
Ya ce mai koken, George Uboh, ya tura kokensa ta hannun Sanata Peter Nwaoboshi na (Delta ta Arewa) wanda ya mika ta ga ofishin Shugaban Majalisar. “Don haka bai kamata a tsaya cece-ku-ce kan hanyar da wani jama’a suka gabatar da koke ga wakilansu ba wadanda za su gabatar ga majalisa saboda oda ta 25 (c) na gudanar da Majalisar Dattawa ta nuna a fili cewa “Shi (Shugaban Majalisar Dattawa) zai iya karbar duk wani sako da aka mika wa majalisar,” inji shi.
Ya ce yadda ake gudanar da harkokin majalisar dokoki a duniya shugaban majalisa bayan ya karbi wani sako yakan mika ne ga kwamitocin da abin ya shafa don daukar matakin da doka ta tsara ya alla majalisa tana zama ko ba ta yi. “Duk da majalisa tana hutu amma ta bayyana cewa wasu daga cikin muhimman kwamitocinta za su ci gaba da aiki ba tare da cikas ba,” inji Melaye a cikin sanarwar.
Bayan sallamar wakilan na EFCC ne sai sanatoci suka fara sauraren bayani kan zargin yadda Lamurde ya karkatar da kudin sata da hukumar ta kwato da suka haura Naira tiriliyan daya.
Shugaban Kamfanin Panic Alert Security Systems, Dokta George Uboh wanda ya rubuta takardar koken ga majalisar, ya ce kashi 95 na kudin da aka kwato Shugaban na EFCC bai shigar da su asusun gwamnati ba.
Ya ce gidaje hudu da aka kwace daga tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha a Landan da aka kimanta kudinsu kan Fam miliyan 10 (kimanin Naira biliyan uku da miliyan 350) da kuma gidansa na Cape Town da ke Afirka ta Kudu da aka kiyasta kudinsa a kan Dala miliyan daya da dubu 200 (kimanin Naira miliyan 253) da tsabar kudi Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 211) da aka samu a dakinsa na Landan duk an karkatar da su.
Kuma ya yi zargin cewa Hukumar EFCC ta karkatar tare da boye Naira miliyan 779 da aka kwato daga hannun tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Mista Tafa Balogun.
“A cikin bayanan hukumar (abin da ya kamata ta kwato shi ne Naira biliyan uku da miliyan 37 da dubu 255 da 521 da Kwabo 60, ba Naira biliyan biyu da miliyan 258 da dubu 100 da 516 da Kwabo 98 ba), kuma maimakon tura Naira biliyan uku da digo uku daga bankin Spring Bank zuwa asusunta na kwato kudi da ke bankin Access Bank, sai EFCC ta tura Naira biliyan biyu da digo biyu kadai ta boye sauran a asusu daban-daban,” inji shi.
Ya ce ya rubuta wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan koka kan karkatar da kudin da EFCC ta yi, amma Jonathan ya yi watsi da wasikarsa.
Ya bukaci Majalisar Dattawa ta tilasta wa Hukumar EFCC ta mika wa Asusun tarayya Naira tiriliyan biyu da biliyan 51 a matsayin jimillar kudin da aka kwato.
Ya yi zargin cewa ma’aikatan Hukumar EFCC a karkashin Lamurde suna kasuwanci da kudin da aka kwato daga barayin gwamnati inda a tsakanin 18 ga Janairun 2010 zuwa 30 ga Oktoban 2013 suka samu ribar Naira miliyan 474 da dubu 294 da 582 da Kwabo 46.
“Idan bayan kwana 30, shaidun da na gabatar karya ne a kama ni, idan kuma gaskiya ne a kama Lamurde,” Uboh ya shaida wa sanatocin, inda ya tabbatar da cewa zargin nasa yana kan hujja.

Advertisements