LABARAI A TAKAICE HAR GUDA ASHIRIN DA
DAYA 21
.
1- A taron da suka gudanar a jahar Adamawa
Gwamnonin Jam’iyar Apc A Nigeria sun sha
Alwashin Lalumo hanyoyin da zasu Samawa
Matasa aiki akasar nan da lokaci kadan
.
2-Rundunar sojan nigeria ta 25 sunyi Nasara
Gano wasu Wurare da ake har hada abubuwan
Fashewa tare da Cafke wasu Manyan Mayakan
kungiyar Boko haram su 4 akauyikan
Sandiya,kokakowa,Nyaleri dake karamar
hukumar Damboa
.
3- Shugaban kasa Muhammadu buhari ya Nada
Manyan Sabbin Mukame a Gwamnatinsa amma
Ya bar baya da kura inda ake sukansa tare da
zargin nuna bangarenci a fili
.
4- Babban Bankin nigeria CBN Ya Amincewa
Jahoshi 27 da karbar bashin da zasu yi Albashi
(Salaries and Arrears) na tsawon wata da
watanni da jahoshin basuyi ba
.
5- Shugaban kasa nigeria Muhammadu buhari
yace yan nigeria suyi hakuri zai samar da
daidaito a mukaman da zai Nada Nan Gaba
.
6- Hukumar kula da Jami’o’i ta( National
Commision University) ta fitar da sunayen
Jami’o’i 65 da Basu Cancanci Zama Jami’a ba

7- Diyar tsohon Mataimakin nigeria Fatima
Atiku Abubakar an bada kwamonshiniyar lafiya
a jahar adamawa kuma tace duk albashin ta
tare da Alawus ta Sadaukar dashi ga Masu
bukata a bangaren lafiyar jahar
.
8- A ranar Juma’a 4 ga watan Gobe na Satumba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai cika
kwanaki Dari 100 akan mulki kuma zaiyiwa yan
kasa bayani akan halin da ya karbi kasar nigeria
.
9- Babban Sufeto na Yan sandan nigeria Mr
solomon Arase Ya Nada Mace Acp Olabisi Alofe
Kolawole A matsayin Kakakin Rundunar Yan
sanda ta riko
.
10- Gwamnan jahar Kwara Abdulfatah Ahmed
Ya bawa Akanta Janar na jahar cewar lallai Ya
fitar da kudi a yi albashi na tsawon wata biyu 2
da ba ayi ba a jahar
.
11- Al’ummar Igbo na cigaba da caccakar
Gwamnatin Muhammadu buhari bisa zargin da
suke yana Maida su saniyar ware akasar
.
12- Shugaban Yan sandan Nigeria Mr Solomon
Arase Yayiwa wasu Manyan Jami’i an Yan sandan
58 sauyin wuraren aiki
.
13- Hukumar Fasakwabri ta nigeria(custom)ta
cafke wasu motoci masu sulke tare da kadarori
da suka kai Naira Miliyan 545 a jahar Imo acikin
Makon da ya Gabata
.
14- Kananan Yara na cigaba da fuskantar cutar
tamowa a sansanin Yan gudun hijjira na jahar
Borno
.
15- Wata Gobara ta tashi agidan shugaban
majalissar wakilai Yakubu Dogara a Unguwar
Maitama A Abuja jiya juma’a da Misalin karfe
10:05am
.
16- Jakadan nigeria a kasar Amerika Prof Ade
Adefuye ya Rasu sakamakon wata karamar jinya
.
17- Babban sakataren Gwamnatin jahar Jigawa
Alh Adamu Abdulkadir Fanini yace zargin da ake
na cewar tantance ma’aikatan jahar da akeyi
Korar ma’aikata za’ayi to ba gaskiya bane
.
18- Rundunar Yan sandan Nigeria tace bata fara
diban Yan sanda ba akasar kamar yadda yanzu
haka wasu Yan damfara suke karbar kudade a
hannun jama’a na cewar zasu sama musu aikin
Yan sandan inda Rundunar tace dazarar an bada
umarnin daukan Yan sandan to zasu sanar
agidan Radiyo da Talabijin
.
19- Gwamnan jahar Imo Mr Rochas Ikoracha
Yace tun kafin ya hau gwamnan jahar yake da
jirgin sama na kansa kuma ya siyar shi yayiwa
al’ummar jaharsa albashi
.
20- Shahararen Marubucin nan na kudancin
nigeria Prof Wole Soyinka yacewa tsohon
shugaban kasar nigeria Olusegun Obasanjo
Makaryaci ne
.
21- Shugaban kasa Muhammadu buhari yace
Cancanta ce takesawa ya bawa Mutum Mukami

Advertisements