‘Yar Gidan Atiku Da Ta Zama Kwamishina Ta Sadaukar Da Albashinta Ga Al’ummar Jihar
Bayan rantsar da ‘yar gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wato Fatima Atiku, a matsayin kwamishinar ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa da gwamnan jihar Jibirilla Bindow ya yi, ta bayyana cewa ta sadaukar da duk albashinta da alawus da za ta samu a matsayin gudunmawarta ga ci gaban fannin kiwon lafiyar jihar.
Tare da cewa ta kudiri aniyar sadaukar da albashinta ne bisa la’akari da irin kalubalen da fannin lafiyar jihar ke fuskanta.

Advertisements