BABBAN LABARI MA HAJJATAN BANA.Mutane Milyan Da Rabi Za Su Sauke Farali A Duniya, Dubu 76 Daga Nijeriya
*.Ba Za Mu Tura Jami’ai Ba-Buhari
*.Za Mu Gudanar Da Aiki Kyauta-Sarkin Musulmi, Adadin kudin da akebiya, zuwa Makka.
.
A matakin da ta dauka na rage yawaitar kudaden da take kashewa a wajen tafiyar da Gwamnati; Shugaba Muhammadu Buhari ya fito fili ya bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ba za ta tura wakilanta a aikin Hajjin bana ba bisa la’akari da yanayin da tattalin arzikin Nijeriya yake ciki.
.
Matakin da Gwamnatin ta dauka zai sa Gwamnatin ta adana dala milyan daya wadanda a shekarun baya a ke kashewa wajen daukar nauyin wakilan Gwamnati.
A bayanin da ya sanyawa hannu, Babban Mataimakin Shugaban Kasa kan sha’anin yada labarai, Malam Garba Shehu ya bayyana cewar rashin wakilan Gwamnati a Hajjin bana ba zai sanya Gwamnatin yin kasa a guiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta kan aikin na ibada ba.
Ya ce Gwamnatin za ta bayar da kulawar da ta saba kan kula da ‘yan kasarta da ke kasa mai tsalki da kuma kulawa da su kan sha’anin kiyon lafiya, tsaro da kuma tallafa masu gwargwadon hali.
A cewarsa Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ne saboda yanayin da tattalin arzikin Nijeriya yake ciki yana mai cewar “Gwamnatocin jihohi idan suna bukata za su iya daukar nauyin nada nasu Amirul Hajj, sai dai a wannan shekarar a tsakiya, ba za mu sa kanmu a ciki ba.” Kakakin ya kalato Shugaba Buhari yana bayyanawa.
.
A wannan shekarar dai Gamnatin Kasar Saudiyya ta kebewa Nijeriya adadin kujerun aikin hajji dubu 76, 000 domin gudanar da aikin hajji kuma daya daga cikin shika-shikan Musulunci a shekarar nan ta 2015 wadanda a ka rarraba ga jihohi.
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON a jawabin da ta fitar daga Shugaban Sashen yada labarai Uba Mana ya bayyana cewar Gwamnatin Saudiyya ta kebe adadin kujerun ne domin amfanin jihohin Nijeriya 36 da kuma Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar ta kuma bayyana cewar daga cikin kujerun da a ka ware 66, 000 an kebe su ne ga jihohi 36 da Birnin Tarayya da kuma Rundunar Soji, yayin da sauran ragowar kujeru 10, 000 an kebe su ne ga wadanda ke shiga jirgin kasa da kasa na International.
“A kan haka, wannan hukumar take kira ga maniyyata aikin hajji da su tuntubi ofishin hukumar jin dadin alhazai a jihohin da suke domin biyan kudi da sauran abubuwan da suka wajaba domin tashinsu zuwa Saudiyya.”
.
Mutane milyan 1.5 za su gudanar da ibadar aikin Hajj a wannan shekarar kamar yadda Ma’aikatar Lamurran Hajji ta Saudiyya ta bayyana a makon nan. Ma’aikatar ta bayyana adadin ne bayan taron tattaunawa tsakanin babban kwamitin tsara aikin hajj wanda ke karkashin jagorancin daya daga cikin sarakunan kasar Makka, Sarki Khalid Al-Faisal.
Khalid al-Faisal ya bayyana cewar mutane milyan 1.535 ne za su shiga kasar Saudiyya daga kasashen waje da kuma mutane 185, 000 daga wasu sassa na Saudiyya. Ya kara da cewar tuni daruruwan mutane suka riga suka shiga kasar ta Saudiyya.
Za a dai fara aikin hajjin wannan shekarar ne a ranar 20 ga Satumba.
Adadin masu zuwa aikin hajji a duniya bakidaya sun ragu bisa ga adadin mutanen da suka gudanar da aikin hajji a 2014 domin kuwa a Shekarar da ta gabata mutane milyan biyu ne suka yi aikin hajj.
.
Duk dai da dakatar da tawagar jami’an Gwamnatin Tarayya zuwa aikin hajjin wannan shekarar; A yunkurinsu na ganin an samu tawagar Gwamnati a hajjin bana, Sarakunan gargajiya sun kafa wani karamin kwamiti domin sanya idanu kan aikin hajji a karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’adu Abubakar III.
A bisa ga wannan Shugaba Muhammadu Buhari ya aminta da kafuwar kwamitin wanda manbobinsa suka bayyana cewar za su gudanar da aiki kyauta ba tare da karbar ko sisin kwabo ba a aikin wanda ke a karkashin Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON). Sarkin Musulmi zai samu wakilci a kwamitin daga Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
A bisa ga wannan ci-gaban; Mataimakin Shugaban Kasa kan yada labarai, Malam Garba Shehu ya yi karin haske kan hakan da cewar amincewar da Sugaban Kasa ya yi bai sabawa ainihin matsayar da ya dauka ta dakatar da daukar nauyin kwamitin hajji na 2015 ba a a bisa ga rage kashe kudaden al’umma.
“Da yake amsar aikin kwamitin na fisabilillahi, Shugaban Kasa ya bayyana karara cewar Gwamnatin Tarayya ba za ta bayar da ko naira ba ga kwamitin da ke karkashin Mai Martaba Sarkin Kano ba. Haka ma Gwamnati ba za ta sanya ko da mutum daya a cikin kwamitin ba.”
Mai magana da yawun Shugaban ya jaddada cewar an riga an dauki dukkanin matakan da suka kamata domin kula da jin dadin mahajjata a kasa mai tsalki a karkashin kananan kwamitoci daban-daban a fannonin kiyon lafiya, masauki, zirga-zirga, sadarwa da yada labarai da kuma tsaro domin samun nasarar aikin hajjin bana.
Wakilinmu ya bamu labarin Sarkin Musulmi wanda Gwamnatin Jonathan ta nada a matsayin Amirul Hajj na din-din-din ya tura Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar El-Kanemi da Oba na Lagos Rilwanu Akiolu domin su jagoranci aikin hajji a shekarar 2013 da 2014. A yanzu kuma Sarkin ya bayyana cewar nadin Sarkin Kano an yi shine bayan tuntube-tuntuben masu ruwa da tsaki.
.
WAKILINMU Ya labarto cewar a ranar Asabar din makon jiya ne a ka kaddamar da tashin Alhazzan Nijeriya zuwa kasa mai tsalki. Mahajjatan sun tashi takanas ta Kano ne zuwa Saudiyya daga filin sauka da tashin jirage na Kaduna da Alhazzai 285.
Gwamna Nasir El-Rufa’i wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kwamitin Sarakuna na aikin hajjin bana yana dauke da mutane biyar kacal wadanda suka hada da Sarkin Zonga a jihar Kwara, Dakta Aliyu Yahaya da Dakta Ibrahim Datti Ahmed da Zakariya’u Babalola da Basaraken jihar Edo, Aliyu K. Danesi a matsayin manbobin kwamitin karkashin San Kano Muhammadu Sanusi II.
Da yake kira ga alhazzan kan su zamo jakadu nagari a kasa mai tsalki, haka ma Shugabna Buhari ya yi kira gare su da su yi wa Nijeriya addu’a domin a samu shawo kan kalubalen ta’addancin da ke faruwa ta hanyar kai hare-hare da kisan wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
A jawabansu daban-daban Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar da Mai Martaba Sarkin Gwandu Muhammadu Ilyasu Bashar da Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris duka sun yi kira ga Alhazzan da kada su yi aiki a cikin rashin sani, wato su rika tambaya kan duk wani abu da ya shige masu duhu kan sharudda da dokokin hajji.
A jawabinsa Shugaban Hukumar Hajji ta Nijeriya Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar ya bayyana cewar kamfunan jirage shida da jirage 13 wadanda za a yi mafani da su wajen jigilar mahajjatan, za su kwashe duka mahajjata dubu 66 gabanin ranar 17 ga watan Satumba da za a rufe bakin sararin iyakar kasar Saudiyya.
“Kamar yadda Gwamnatin Saudiyya ta bayyana, akwai yiyuwar za a yi hawan Arafat a ranar 22 ga Satumba. Haka ma jirgin farko zai fara dawowa gida a ranar 27, haka ma jirgin karshe a ranar 27 ga Okroba.” Ya bayyana.
Ya luma ce “A bisa ga kokarin Mai Alfarma Sarkin Musulmi da sauran masu ruwa da tsaki da a ke samun nasara, wadanda suka fara barin Nijeriya, insha Allahu sune na farko da za su fara barin Saudiyya zuwa Nijeriya.”
Daga nan sai kuma ya bayyanawa mahajjatan cewar kada su sayi ruwan Zanzam domin hukumarsa da kuma kamfunan jiragen sun riga sun yi tanadin wadatattun ruwan Zamzam ga Alhazzan bakidaya.
.
A jihar Kaduna dai Gwamna El-Rufa’i ya aminta da tura jami’an 116 da za su tallafawa mahajjatan jihar a kasa mai tsalki kamar yadda Mai Magana da yawun Gwamnan Samuel Aruwan ya bayyana a wani bayani da ya fitar. A cewarsa Gwamnatin jihar ta yi nasarar ajiye rarar sama da Naira miliyan 200 sakamakon dakatar da daukar nauyin da yawa daga cikin al’ummar jihar domin gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar.
Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ne Gwamnatin Kaduna ta bayyana a matsayin Amirul Hajj na jihar. Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, an samu sawu 6 dauke da maniyyata 2,072 daga jihar Kaduna.
.
LEADERSHIP Hausa ta kalato Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya ta na bayyana kudaden zuwa aikin hajjin 2015 da cewar wadanda za su je hajji daga Arewacin kasar nan za su biya N758,476.59 a matsayin kudin karamar kujera da guziri $750; haka kuma kudin matsakaiciyar shi ne N798,476 da kudin guziri $1,000; yayin da babbar kujera kudin ta shi ne N897,476 da guzirin $1,500.
Kamar yadda Kakakin Hukumar Uba Mana ya bayyana, masu tafiya Hajji daga Kudancin kasar nan za su biya kudin karamar kujera N766,556 da kudin guziri dala 750; matsakaiciyar kujera kuwa za a biya N806,556, sannan kudin guzirin ta shi ne dala 1000; sai babbar kujera wadda za a biya N905,556 da guziri dala1,500.

Advertisements