TATTAUNAWA: Rigimata Da Gwamna Nasir El-rufa’i Ta Neman Gyara Ce —Sanata Shehu Sani
.
Ga duk masu bibiyar abubuwan da ke faruwa a jihar Kaduna, ya san akwai wata babbar matsala a tsakanin Gwamna Nasiru El-rufa’i da Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya,SANATA SHEHU SANI, musamman idan aka yi la’akari da irin kalaman da shi Sanatan ke furtawa game da Gwamnan. Wannan ne ya sa wakilinmu,ya tuntubi Sanatan don ji me ya yi zafi haka. A cikin wannan tattaunawar, Sanata Shehu Sani ya bayyana wa wakilinmu namu manyan abubuwan da suka sa ya zare takobin yaki tsakaninsa da Gwamnan, amma ya ce duk da wannan shirin yaki da ya yi, ba wata manufa yake yi ba, sai don neman gyara. Ga cikakkiyar hirar mu nan dashi:
.
Wani al’amari da ya dauki hankulan jama’a a halin yanzu shi ne abin da ake ganin cewa tamar wata matsala ce ta sarke a tsakaninka da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i. Wane karin haske za ka yi wa jama’a?
.
Da farko dai, a matsayina ni Sanata ne, na yi takara na kuma kayar da wanda ke kan kujera, kuma takarar da na yi, ban bukaci goyan bayan kowa ba, sai talakawa. Sannan akwai mutanen da suka yi takarar Gwamna a jihar Kaduna, akwai Isah Ashiru, da shi Nasiru da kuma Haruna Sa’idu, wani abin ban mamaki, dukkaninsu su ukun nan, kowanne yana da nasa dan takarar Sanata a mazabar Kaduna ta tsakiya, amma ni ba na tare da ko daya daga cikinsu, kuma dukkaninsu sun yake ni, saboda suna da wanda suke son ya zama masu Sanata, kuma na hade su gaba daya na rushe.
Ni kuma na ci Sanata ta wani abu na ikon Allah, saboda ban ba kowa ko kwabo ba aka zabe ni. kafin nan, sai da na tara dukkan wakilai gaba dayansu, na ce masu ni ba zan ba kowa ko kwabo ba, amma idan kun ga na cancanta, ku zabe ni, idan kuma kuna ganin ban cancanta ba, ku je ku zabi duk wanda kuke so, kuma Allah cikin ikonsa ya nufa na yi nasara.
To tun daga wannan lokaci abubuwa da dama suka rinka faruwa, wanda na yi ta hakuri na rike shi a zuciyata. Ka ga abu na farko, sau biyu Shugaban kasa Buhari yana zuwa Kaduna, amma su su Nasiru suka hana a sanya sunana daga cikin wadanda za su yi magana da shi. Na farko ya zo lokacin da aka kaddamar da Nasiru a matsayin dan takarar Gwamna, sannan na biyu ya zo lokacin da Nasiru yake yakin neman zabe, sannan abu na uku shi ne zuwan da Mataimakin Shugaban kasa na yanzu ya yi, inda ya zo ya bayar da taimakon gwamnatin tarayya ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, a nan wajen ma aka bar manyan mutane suka yi Magana, amma ni a matsayina na Sanata aka hana ni.
Bayan na ci zabe, El-rufa’i bai taba daukar waya ya kira ni ya ce yana taya ni murna ba, lokacin da na ci zaben fitar da gwani, da kuma babban zabe gaba daya. Bayan wannan, a matsayinsa na dan takarar Gwamna a jam’iyyarmu ta APC, na ba shi dukkan goyan bayan da ya dace, wallahi, wallahi, wallahi na rantse maka har sau uku ko? Har iyalaina na dauka na je gidansa na Abuja, iyalina suka gana da iyalinsa domin kara dankon zumunci.
Sannan ana gobe za a gudanar da zabe, mun yi salla a masallacin Tudun Wada Kaduna, na dauki Nasiru na kai shi gidanmu wajen mahaifiyata suka gaisa, bayan an kammala zabe, aka kafa kwamitin karbar mulki, aka sanya dukkan jama’a, amma ni aka ki sanya ni a ciki, daga cikin wadanda aka sanya sunayensu, har da wani wanda ya yi takarar Sanata a yankin Kudancin Kaduna, amma bai ci ba, an sanya shi ciki, amma ni ba a sanya sunana ba. Sai na kira shi ta waya, na ce, Nasiru me ya faru za a kafa wannan kwamiti a sanya kowa a ciki, amma ni a matsayina na Sanata a ce babu sunana? Sai ya ce mani ai shi bai sani ba ne, yana ganin an yi mantuwa ne, shi ne sai ya sa aka kira Sakataren gwamnatin jihar, sannan aka yi wasu gyare-gyare aka ce an sanya sunana. Sau biyu ina zuwa ina zama a wannan kwamitin domin in bayar da tawa gudumawar.
.
Bayan an gama wannan, sai ya kasance an zo an kafa gwamnati, da aka kafa gwamnati, da farko aka yi taro na karrama shi saboda ya ci Gwamna, a gidan gwamnatin jiha. Da na je wannan wuri, na samu kowa yana da wajen zama, amma ni a matsayina na Sanata ba ni da wajen da zan zauna, duk an cika ko’ina, haka na tashi na kakkabe rigata na bar wajen.
Bayan wannan, sai aka zo maganar nada mukamai. Kamar yadda kowa ya sani, mu biyu ne Sanatoci na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, ni da Suleman Hunkuyi. Amma Sanatan da na kayar, Sani Sale aka ba shi Kwamishina da Kantoman riko na Karamar Hukuma, domin an bukaci ya kawo sunan mutanensa, kuma ya kawo aka bayar. Haka shi ma Sule Hunkunyi, aka ba shi Kwamishina da Kantoman riko, ni a matsayina na Sanata a Karamar Hukumar da na fito ta Kaduna ta Kudu, ko Masinja ba a ce in kawo ba, duk da cewa tun da farko ya ce in bayar da sunaye, kuma na bayar din, ya kuma ce ya gani, zai duba, kuma zai bayar, bai ba ni ba, bai kira ni ba, sannan daga baya ma ya zama baya daukar wayata, duk irin kiran da zan yi misa, saboda haka sai na kyale shi kawai.
Amma shi zai ji dadi a ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zo ya dauki mukamai ya ba Isah Ashiru, wanda ya kayar a zaben fitar da gwani, ba tare da sanin sa ba? Saboda haka sai na kara fahimtar cewa akwai wani wanda yake da burin ya sanya shi ya yi takarar Sanata a mazabar Kaduna ta Tsakiya a 2019. Sai na ce tun da abin ya zamo wulakanci da cin mutunci ne, to bari zan rabu da su, za mu hadu kawai a filin daga, shi ne na ja layi. Kuma da na ja wannan layin ne, sai hankalinsu ya tashi. Kuma na gaya masa cewa, ni mutum ne mai tarihi na yaki, domin ni ba dan siyasa ba ne, ba na bukatar samun ko kwabo a cikin gwamnatinsa, tun da aka fara mulkin dimukradiyya a Nijeriya, bana shekara 16, ko kwangilar Biro ban taba yi ba a jihar Kaduna, kuma babu wani Gwamna da zai ce ya taba ba ni kwabo a jihar Kaduna. Saboda haka idan har na yi shekara 16 a hakan, to menene shekara 4? Shi ne yake Gwamna, shi zai sha surutu, kuma shi zai sha adawa.
.
Tambayar da ya kamata mutane su yi shi ne, kafin 1999 waye El-rufa’i? Mu kuwa ‘yan Kaduna ne, wadanda suka jagoranci yaki da gwamnatin Babangida da ta Abacha, an daure ni a kurkuku da yawa, shi kuwa babu wanda ya san shi sai a shekarar 1999, lokacin da aka kafa dimukuradiyya aka ba shi mukami, amma duk wanda ya san tarihin Shehu Sani, ya san da cewa na zauna a kurkukun Kaduna, na zauna a kurkukun Kirikiri shekara 4, na zauna a kurkukun Fatakawl na zauna a kurkukun Aba ta jihar Abia, caji ofis da dama na tsinci kaina a wajen, duk a matsayina na dan gwagwamarya a wancan lokacin, ballantana yanzu ina kan mulki, ka ce za ka taka ni? Ka dauko wasu hanyoyi na neman bata wa jam’iyyarmu suna, har ka sanya jama’a su fara nadamar menene ya sa suka zabeka. Shi ya sa tun daga yanzu na ja layi a kai, ba wai maganar cewa ana jam’iyya daya ba ne, domin ita jam’iyya ba kungiyar asiri ba ce, ballantana a ce ba za ka yi magana ba, idan ka ga ana yin abu ba daidai ba. Domin an fadi cewa, ko musulmi dan uwanka sai ka fada masa gaskiya, ballantana wata aba wai ita jam’iyya, wacce a duniya muka same ta, kuma a duniya za mu bar ta.
.
Wani abu wanda jama’a ke nuna damuwa a kai shi ne, yadda ake ganin cewa ba ku dade da kama madafun iko ba, wadannan abubuwa suka fara tasowa. A iyaka fahimtarka, kana ganin menene ya sa Gwamna da Mukarrabansa suke yi maka haka?
Wato muna da bambancin akida ta siyasa da Nasiru, domin ni akidata ta talakawa ce, shi kuma akidarsa ba ta talakawa ba ce, ta jari hujja ce. A rayuwar Nasiru gaba daya babu maganar talaka a ciki akidarsa, domin ta jari hujja ce, a sayar da kamfanonin gwamnati, a taka kowa, a kwashe kowa, masu kudi su kara kudi, a kawata gari, a yi garari a yi bushasha. Ni kuwa akidata ta gwagwarmaya ce da taimakon talakawa, ka ga mun saba da shi ta bangaren akida.
Abu na biyu kuma, shi bukatarsa ita ce ya zama cewa babu wani tauraro mai haskawa a jihar Kaduna sai shi kadai, duk wani wanda ya san cewa yana da haske, to zai yi adawa da shi bakin rai bakin fama, ni kuwa a Kaduna, a nan aka haife ni, a nan aka haifi iyayena, a nan na tashi, a nan nake zaune, kuma a nan na ci zabe, matana guda biyu, duk a Kaduna suke. Amma shi kuwa sai da ya ci Gwamna sannan ya dawo Kaduna ya zauna, ka ga kuwa ba zai nuna mani Kaduna ba, babu wata Unguwa a Kaduna wacce ban santa ba, ko ba a sanni ba, ko kuma ba zan nuna maka akalla mutum guda wanda na sani a Unguwar ba. Saboda haka mu ‘yan wuri ne, nan muke, nan ya zo ya samemu, kuma ni ba wai na fara adawata a CPC ko APC ba ne, ni fa shekara 30 ina gwagwamarya. Saboda haka abin da ya sa muka rabu, akwai bambancin akida a tsakaninmu, sannan kuma akwai wani kulli a zuciyarsa, wanda ya dade yana yi mani, amma ina shanyewa, don a zauna lafiya, Muhammadu Buhari ya samu nasara.
A 2011 abin da suka yi mani ke nan, wanda na kayar, suka dauki zabe suka ba shi, amma na kyale, saboda burin da nake da shi na Buhari ya ci zabe ne. Saboda haka sun ga wannan lokaci Allah ya nufa na yi nasara a kan ‘yan takararsu, shi ne suka dauko wadannan hanyoyi na yakata, ni kuma na bayyana masa cewa babu abin da na kware a rayuwa kamar yaki. Saboda haka idan yaki yake so, za a yi shi, kuma za a kara, kuma babu wani wanda zai iya kare shi, domin dukkan wadanda yake sanyawa suna magana a kafafen yada labarai, kudi ne yake ba su, kuma sun yi wa gwamnatocin baya aiki, ni kuwa tawa akida ce ta talakawa, tsagwaron aikinsu muka sa a gaba.
.
Ga shi nan dai kowa ya gani, tun da ya ci Gwamna, babu mai zuwa gidansa, ‘yan jam’iyyar ma kuka suke yi da shi. Ya za a yi a ce ina matsayin Gwamna, ‘yan jam’iyyata ba za su iya ziyarata ba? Ga shi dai yanzu kai ka gani, ka zo tattaunawa da ni, ka samu jama’a jibge a kofar gidana sun zo wajena. Saboda haka, ka gaya mani, wani dan APC a Kaduna, wanda ya isa ya kai ziyara gidan Gwamna ya gan shi. Ko kadan akidata ba daya bace da tasa, kuma abin da ya boye a zuciyarsa a kaina, ba abu ba ne mai kyau, kuma ya yi da mai yi, shege ka fasa!
To akwai masu ganin cewa a matsayinka na Sanata, aikinka yana birnin tarayya Abuja ne, domin ka wakilci jama’arka, saboda haka kalubalantar Gwamna da kake yi, ko kadan bai dace ba?
Saboda aikina na Abuja ne, an ce in kare bukatun mutanen Abuja ne? Saboda haka jama’ata suna Kaduna ne, dole in kare muradunsu. Ka je ka tura masu motoci sun rusa masu gidaje, kai ba ka ba su gidan da za su zauna ba, ba ka ba su wani filin da za su gina ba, ka zo cikin gari kana yi wa mutane tijara, kana masu girman kai da isgilanci a gari, saboda kawai kai Gwamna ne! Ya samu wadansu mutane da suke adawa da ni ya hada kai da su suna yakata, to ni ma babu makawa dole zan fuskance shi. Ai kamar yadda na gaya maka ne, idan ka ga ana zaune lafiya, to babu shakka ana adalci ne. Ni kai na ba wai son raina ba ne abubuwan da suke faruwa, to amma ya zama wajibi a gere ni da in fito in yake shi, saboda ya dauko hanyar yaki da mutane. Aikinasa shi ne kare hakkin mutane, kuma dukkan wani wanda ya zalunce su dole ne in yake shi.
.
Abin da nake bukata ka sani fa, shi ne, talakawan nan su suka zabe mu, gwamnati ta ba su kudade da atamfofi da sabulai, amma suka ki zabarta, suka zabe mu, takawan nan fa an musguna masu, wasu an kasha su, wasu an kore su, an ci mutuncinsu, amma duk da haka suka tsaya suka ce sai APC, to mutanen nan idan ba mu dadada masu ba, to menene za mu yi masu?
Yanzu ka duba matakan da ya dauka. Da farko dai ya je ya dauko mutanen da ba’yan jihar Kaduna ba ya ba su mukamai, idan ka ga mutum ya yi haka, to dayan biyu ne, ko dai bai da bukatar mutanen jihar Kaduna, ko kuma yana da burin mutanen da ya dauko su yi misa wani aiki a niyyar da yake da ita na wata takara a nan gaba. Sannan ya bi ya rushe gidajen mutane, har ma da wadanda suke da takardu gaba daya, domin sun kawo mana mun gani. Sannan ya zo ya kori jama’a, wadanda suke gudanar da sana’o’i a kan titi, wanda mutanen nan kai ba aiki ka samar masu ba, ba jari ka ba su ba, kai ba gidanka suke zuwa cin abinci ba, amma duk ka bi ka kore su. Sannan ka zo ka kori mabarata, wanda yake mabaratan nan, da kutare da makafi da guragu, su ne suka fito cikin rana suka bi layi suka zabe mu, aka rinka kwasarsu ana zubawa a motoci, wai ana kai su jihohinsu na asali. A nan Kaduna, Hedikwatar Arewa, mu da muke bakin ciki a kan yadda ake kwaso mabarata ‘yan Arewa daga jihohin Kudu ana dawowa da su gida, sai ga shi yanzu ana haka a nan Arewa.
Sannan ka duba wani mataki da ya dauka na hana ba mutane abinci a lokacin azumi, tunda aka yi jihar Kaduna, babu wani Gwamna wanda bai bayar da abinci ga masu karamin karfi a lokacin azumi ba, kai ba ma jihar Kaduna ba, dukkan Nijeriya, har da jihohin da ba na musulmi ba, kamar jihohin Enugu da Anambra da Bayelsa da sauransu da dama. Idan lokacin azumi ya yi, gwamnatocin jihohin na ware kudade domin a sayo abinci a rarraba wa marasa karfi, amma shi ya ce ba zai yi ba, menene amfanin haka?
Sannan ka duba aikin hajji, shi ma ya ce wai ba zai taimaka wa wadanda suke zuwa suna mana addu’o’in na samun zaman lafiya a kasa ba. Sannan ka duba abin bakin cikin da ya faru a Zariya, inda ya kira mutane da sunan tantance ma’aikata, aka zo aka kashe mutane masu yawa a wajen, amma a ce Gwamna ya gaza kiran iyalan wadannan bayin Allah ya taimaka masu da abin da za su rayu da shi na tsawon rayuwarsu? Saboda haka abubuwan da ya rinka yi a Abuja a 2007, to a Kaduna yin hakan ba zai yiwu ba a 2015, domin Nijeriyar 2007 daban take da Nijeriyar 2015, mutane sun wahala sun azabtu a cikin mulkin PDP, to kamata ya yi kuwa da APC ta kafa gwamnati, a samu sauki.
Sannan wannan suka da nake yi masa, ba wai don ba na sonsa ba ne, sai dai ina yi ne don a samu gyara, amma shi ya dauki hanyata ta yakata da kuma kwashe mani kafa, shi ne ya sa na ce to zan taka maka birki, idan ya so dukkanin abin da zai faru, ya faru.
.
To akwai wadanda ke ganin cewa duk wannan dambarwa da ke faruwa a tsakaninka da Gwamna, ta biyo bayan wani buri da kake da shi ne na yin takarar Gwamna a 2019?
Lallai kam mutane na ta yayata wannan magana, amma ya za a yi a ce a matsayina na Musulmi, wanda Allah ya ba wannan matsayi, kuma ban san mene ne zai faru da ni a gobe ba, sannan in tsaya ina maganar shekaru hudu masu zuwa nan gaba? Saboda haka abin da ya dame ni yanzu shi ne, aikin Sanata, da kuma kare muradun talakawan da aka zalunta, babu wanda ya san gobe sai Allah. Shi kanshi da ake kuranwa cewa wai zai zama shugaban kasa a 2019, mu dai muna da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, saboda haka babu dalili, domin ana zuga ka, har ya zama cewa ka je ka dauko wasu jama’a wadanda ba ‘yan jiha ba domin su zo su yi maka yakin neman zabe. Ni tsarina ba irin wannan ba ne, abin da da na sanya gaba shi ne, yadda zan taimaki jam’ata, wadanda suka zabe ni, abin da zai faru da ni gobe kuwa, yana wajen Allah ne, yana iya yiyuwa wannan Sanata da nake yi, na karshe ne a rayuwata, yana kuma iya yiwuwa akwai wani tanadi da ya yi mani. Saboda haka a matsayina na musulmi, abin da zai faru da ni gobe, yana wajen Allah ne, amma maganar mutane, wannan ni ba zan hana su maganarsu ba.
.
Yanzu misali idan aka ce za a yi zaman sulhu da kai da Gwamna, shin za ka amince da wannan zama?
Ni ba ma sai mun zauna ba, amma idan na ga ana yi wa mutane abin da ya kamata, shike nan babu korafi, don haka ba sai mun zauna ba. Ya zamana cewa an daina cutar da mutane ana cin zarafinsu da zaluntarsu, kuma a daina yakata ta bayan gida. Idan wadannan abubuwa suka tabbata, shike nan, ni ba sai na yi zama da shi ba. Amma idan ya koma yana yakata a boye, ko yana kwashe mani kafa, yana haddasa mani matsaloli, to ina tabbatar maka lallai za mu ci gaba da karawa da shi.

Advertisements