Shugaban Karamar hukumar Bukuyun Ya Nemi A Binciki Yadda Akai Kai Masa Hari
.
Shugaban Karamar Hukumar Bukuyum, Hon. Shehu Buda ya koka kan rashin hukunta wadanda suka kai masa hari a lokacin da Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Abubakar Yari ya kai ziyarar salla a Karamar Hukumar. Hon. ya yi wannan kuka nasa ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Gusau.
Wakilinmu ya shaida mana cewa a wanncan lokaci, Shugaban ya gamu da fushin wadansu ‘yan dabar siyasa ne dauke da adduna da itatuwa, suna sanye da riguna masu dauke da hotunan dan Majalisar jihar mai wakiltar Bukuyum, Hon. Mani Mumuni da tsohon Kwamishinan sufuri, Hon. Nasiru Zarumai, suka tunkari tawagar Shugaban Karamar Hukumar da sara da duka, inda har suka jikkata mutum uku daga cikin tawagar.
Hon. Shehu Buda ya kara da cewa, “wannan hari da gungun ‘yan ta’addan da suka zo daga Masama, ni su ka yi harin ganin bayana, ba wai magoya bayana ba, kuma a lokacin suna dauke da ganguna suna rawa suna zagina, inda nagode ma Allah, duk wanda ke tare da ni babu mai ko allura, kuma a gaban jami’an tsaro aka yi wannan ta’addancin, su ne shaiduna, abin ya fi karfin su ne kawai. Amma daga baya ya kamata su dauki mataki, amma har yanzu shiru kake ji. Duk da a gaban su aka sari Aminu Ibrahim Bukuyum da Ibrahim Isah Bushasha da Kasimu Abubakar Nasarawa, wadannan dukkansu magashiyan aka kai su asibiti. Idan jami’an tsaro ba su dauki mataki a kan wadannan mahara ba tun da wuri, to nan gaba ba zai hafar mana da da mai ido ba.”
Da aka tambaye game da matsalolin da ke faruwa tsakaninsa da Hon. Mani Mumuni da Tsohon Kwamishina Nasiru Zarimi. Hon. Shehu cewa ya yi, “su bukatar su a zaben da ya gabata, in tozarta wadanda su ka yi adawa da mu, wato ma’aikatan Kananan Hukumomi da masu mukaman Sarauta, ni kuma na ki, domin ina koyi ne da Gwamna, ban ga wanda ya tozarta ba.”

Advertisements