FALALAR ISTIGFAR, DA KUMA ISTIGFAR WANDA YAKE SHUGABA GA KOWANE ISTIGFAR:
———————————
Annabi (S.A.W) Yace: Shugaban istigfar shine kace:
Allahumma Anta Rabbi la’ilaha illa Anta, khalaqtani wa ana Abduka, wa ana ala ahdika wa wa’adika masta da’atu, A’uzu bika min sharri ma sa na’atu, Abu’u laka bini’imatika A Layya, Wa Abu’u bizanbi, fagfirli-fa innahu la Yagfiruzzunuba illa Anta.
===
duk wanda ya fadi wannan istigfarin da rana yana mai sakankancewa ya kuma mutu kafin yamma, to shi dan aljanna ne, in kuma ya fada ne da daddare yana mai sakankancewa ya mutu kuma kafin asubahi to shi dan aljanna ne.
( Buhari da nisa’iyu suka ruwai toshi, daga shaddadu Ibni Ausi)
R.A
.
Annabi (S.A.W) Yace; duk wanda ya nemi gafara bayan kowace sallah sau uku yace: Astagfi-rulla-hallazi laa ilaha illa huwal hayyul kayyum wa a tuubu ilaihi.
Za’a gafarta masa zunubansa koda ya gudo daga gun yaki ne.
.
Annabi (S.A.W) yace; duk wanda ya nemawa muminai maza da muminai mata gafara a kullum sau (27) Allah zai sashi daga cikin wadanda Allah yake amsar addu’arsu, Yake kuma azurta wanda suke kan doron kasarnan saboda albarkacin su.
.
Annabi (S.A.W) Yace: wanda ya fada yayin da yazo kwanciya: Astagfirulla-hallazi la ilaha illa huwalhayyul qayyum wa a tubu ilaihi.
Ya fadi haka sau (3) an gafarta masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi, koda ya kai yawan ganyen bishiyu, koda yakai yawan adadin rairayi, koda yakai adadin kwanakin duniya.
.
Annabi (S.A.W) Yace; wanda duk ya lazimci yin istigfar, Allah zai kawo masa mafita a kowane irin kunci, da farin ciki a kowane bakin ciki, zai arzurta shi kuma ta inda bai zata ba.
.
Allahu Akbar sada qata Rasulullahi (S.A.W) Ya Allah kabamu ikon yin istigfar ako yaushe, kakuma ga farta muna dukkan kura-kuranmu..

Advertisements