*****************************
Kadan daga darajojin Nana
Aisha (r.a)
1— Itace budurwa aduk
matan Annabi (s.a.w).
2— Itace wadda aka tambayi
Annabi (s.a.w) akan wa
yafiso? Sai yace Aisha.
3— Itace wadda Suke tsere
da Annabi s.a.w
4— Itace wadda Idan tasha
abu a kofi, Annabi (s.a.w)
yake karkato saitin inda tasa
baki shima yasa nasa bakin.
5— Itace wadda idan ta
gutsiri qashi, Annabi (s.a.w)
yake gutsurar inda ta
gutsura.
6— Itace wadda akewa
Annabi (s.a.w) wahayi suna
cikin mayafi daya.
7— Itace wadda aka binne
Annabi (s.a.w) acikin dakinta.
8— Itace wadda aka karbi
ran Annabi (s.a.w) atsakanin
qirjinta da cinyarta.
9— Itace wadda ta tauna
Asuwakin Annabi s.a.w
naqarshe abakinta tasa masa
abakinsa.
10— Itace wadda tafi kowace
mace Ilimi a matan zamanin.
11— Itace wadda duk wanda
bai yarda da Mamansa bace ،
to ba Mumini bane.
12— Itace wadda Allah
yasaukar da ayoyi kusan 18
kuma ake karantawa akan
wanketa a zargen da akai
mata.
Aminci ، jinqayi, Gafara, da
Rahamar Allah su tabbata ga
wanda ya qaunaceta,
Asara, Talauci, Musiba, da
qasqanci su tabbata ga
wanda ya zageta, ko yayi
mata qazafi.
Ameeeeeeeeeeeen

Advertisements