DADINA DA GOBE SAURIN ZUWA
Ana Kyautata Zaton Shugaban kasa
Muhammadu Buhari Zai iya Bayyana Sunayen
Ministocinsa A Sati Mai zuwa da zamu shiga
.
Inda Yanzu haka wasu Ruhotannin suka ce Tini
Shugaban kasar ta Nigeria Ya turawa Uwar
Jam’iyar tasa ta Apc Sunayen Ministocin da yake
son Nadawa Dan Neman Shawarar su
.
Kamar Yadda Yanzu haka wasu Jaridun nigeria
suka rawaito Sun Nuna cewar Shugaban kasar
Muhammadu Buhari ya tura sunayen Ministocin
da yake son Nadawa zuwa ga Iyayen uwar
Jam’iyar dan Neman shawarar su
Bayanai da wani Dan kwamatin Amintattau na
Jam’iyar ta Apc ya Tseguntawa wata Jarida ya
Nuna cewar Shugaban kasar zai iya bayyana
Ministocin da yake son Nadawa da zarar Iyayen
Jam’iyar tasu ta Apc Sun nuna Goyon bayansu
ga wadanda Ya zaba
.
Haka kuma wani daga cikin Jigo na Jam’iyar ya
sake tseguntawa Jaridar cewar Asatin da ya
Gabata shugaban kasa ya Gana da Shugabannin
Jam’iyar tasu ta Apc akan wasu Batutuwa
Bayan haka kuma Mutumin ya sake tseguntawa
Jaridar cewar Anasaran Akwai wasu Tsofin
Gwamnoni acikin ministocin wadanda suka hada
da Na River da Lagos wato Rotime Ameachi da
Babatunde Fashola har da wasu wadanda suka
hada Babagana Kingibe da Postor Bakare
Haka kuma ya kara da cewar daga Yanzu zuwa
ko yaushe acikin wannan watan shugaban kasar
zai gabatar da sunayen Ministocin ga Majalissar
Dokokin kasar
Shugaban kasar dai ta Nigeria na Kokarin Cika
Alkarinsa ne dubba da cewar Yayi alkawarin
bayyana Sunayen Ministocin nasa a wannan
watan na Satumba
Ya Allah kakawo mana cigaba kasar Mai Amfani
AMEEN

Advertisements