Buhari Da Obasanjo Sun Yi Ganawar Sirri A Villa
A yammacin yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo a fadarsa da ke Villa.
Shugabannin biyu sun yi ganawar tsohon awa daya a ofishin shugaban kasan.
Saidai har lokacin kammala wannan rahoto ba a tabbatar da musabbabin zaman ba. Sannan kuma Obasanjo ya ki amsa tambayoyin manema labarai bayan da Buhari ya rako shi har wurin motarsa da misalin karfe 4:17.
Obasanjo ya fadawa manema labaran cewa irin gurbataccen turancin nan da ake kira da pigdin, inda ya ce musu ‘comot joo’, wato su matsa su ba shi wuri.

Advertisements