Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Siyan Fom Din Shiga Makarantun Gaba Da Sakandire
Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufa’I, ta bayyana cewa daga yanzu babu wani dalibi mai neman shiga makarantun gaba da sakandare mallakan jihar da zai biya ko sayi wata fom domin cikawa.
Gwamnatin ta kara da cewa kyauta za a dinga cika fom din ta hanyar yanar gizo ko takarda, ba tare da an biya ko sisin kobo ba.
Kwamishinan ilimin jihar, Dakta Adamu Shehu, shi ya bayyana hakan, inda kuma ya kara da cewa duk wanda ya san yana zaune a gidan malamai a makarantun sakandaren jihar kuma shi ba malamin makarantan bane, to ya gaggauta tashi nan da kwana 90.
Gwamnatin ta kara da cewa za ta dinga ba dalibanta masu koyan aikin asibiti naira 15,000 duk wata a matsayin wani tallafi na musamman.

Advertisements