BABIN AIKIN HAJJI (GA YANDA AKE AI-KIN HAJJI)
Hajji wajibi ne sau daya a rayuwa, ga ko wane mukallafi wanda ya sami iko, kuma baya inganta sai daga musulmi.
Hajji yana da Rukunai guda Hudu (4)
Gasu kamar haka:
.
1: Ihrami (Daura niyya) A wani lokaci na musamman shi ne shawwal da zul-ka’ada da zul-hijja, da kuma guri na musamman shi ne Makka, ga wanda yake mazauninta ne, da Zul-hulaifa ga wanda ya taho daga Madina, da Juhfa, ga wanda ya taho daga Misira ko sham, ko Magarib (Maroko) da Yalamlam, ga wanda ya taho daga Yaman, da Zatul-iriki ga wanda ya taho daga Farisa da Huraisana.
Kuma hajji baya Kulluwa sai da niyya wadda ake hada ta da magana ko aiki.
Mustahabbi ne ga mai aikin hajji, ya gusar da kazantar da take tare da shi kafin ya shiga aikin hajji, wato ya yanke faratansa ya gusar da gashin da yake jikinsa.
.
SUNNONIN IHRAMI KUWA GUDA HUDU NE:
.
1: wanka wanda zai kasance tare da Ihrami.
2: Tubuwa daga tufar da aka dinka, da sanya gyauto da mayafi da takalman fade guda biyu.
3: Yin sallah raka’a biyu wadda bata farilla ba.
4: Yin talbiyya: shi ne cewa:
LABBAIKALLAHUMMA LABBAIK LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIK, INNAL HAMDA WANNI’IMATA LAKA WALMULUK LASHARIKA LAKA,
Kuma ba zai dai na yin talbiyya ba sai ya shiga Makka, idan kuma yayi dawafi yayi sa’ayi sai ya ci gaba da yin talbiyya, saboda tafiya wajen Sallah na Arfa, kuma Ihrami iri hudu ne, amma wanda yafi shi ne Ifradi, shi ne mutun ya kuduri niyyar yin hajji shi kadai,
sannan idan ya idar An sunnanta masa ya kudiri niyyar Umra.
Kuma Ihramin namiji ya shafi fuskarsa da kansa, saboda haka ya haramta gare shi ya rufe kansa da abinda aka dinka mai rufewa ne kamar rawani ko wani yanki, haka nan ya haramta gareshi ya yi amfani da dukkan abin da ake amfani da shi saboda maganin sanyi ko zafi.
Haka ya haramta gareshi ya sanya zobe.
Ita kuma macce Ihraminta ya shafi fuskarta da tafikanta kawai, kuma ta na iya sanya wani yanki a fuskarta don sitircewa, amma kada ya zama ta dinke shi da allura ko makamancinsa.
Ya haramta ga Muhrimi ya shafa turaren da zai dade a jikinsa ko tufarsa, kamar almiski da turaran ambar, haka nan ya haramta a gareshi ya shafa mai a kansa, ko ya yanke farce, ko ya gusar da gashi daga jikinsa, ko yayi Jima’i ko abubuwan da a ke yi kafin jima’i idan ya zama ya faru ne kafin tsayiwar Arfa ko bayanta, kafin a yi dawafin Ifala, da jifar jamra a ranar yanka ko kafinta.
.
RUKUNI NA BIYU SHINE:
———————-
1:Dawafi shi kuma yana da abubuwa wajibabbu da sunnoni da mustahabbai, abubuwan da suka wajaba acikinsa (Dawafi) kuwa guda shida ne.
.
1: kubuta daga kari (bayan gida ko fitsari ko tusa) da dauda (janaba,haila)
2: Suturce al-aura
3: Sanya ka’aba a hagunsa
4: Yin dawafi sau bakwai acikin Masallaci.
5: Gabadayan jiki ya zama baya ta6a ka’aba.
6: Yin Sallah raka’a biyu bayan an kammala dawafin.
.
SUNNONIN DAWAFI KUWA GUDA BIYAR NE:
1: Yin Tafiya.
2: sumbantar hajarul-aswadi da baki a zagaye na farko idan mutun ya sami iko
3: shafar rukunil-yamani a zagaye na farko.
4: Yin Addu’a da yin salati ga Annabi (S.A.W).
5: Yin sassarfa a zagaye na farko wato karin hanzari a kan tafiya sak wanda bai kai gubu ba.
.
MUSTAHABBAN HAJJI KUMA SUNA DA YAWA:
Daga cikinsu akwai barin karatun Alkur’ani da yawa, da barin zance ko rera waka, da barin shan ruwa sai dai idan an ji kishirwa.
Idan mutun bako ne ya yi kokarin ya yawaita dawafi domin shi ya fi masa akan yin Sallah.
*Mustahabbi ne ga wanda ya zauna a cikin masallaci ya fuskanci ka’aba, kuma makaruhi ne yin karatu da yin talbiyya acikinsa.
.
RUKUNI NA UKU (3) SHINE:
Sa’ayi tsakanin safa da marwa sau bakwai, kuma zai fara safa ya kammala a marwa, kuma zai kirga farawar ne a matsayin sawu daya komawa ma a matsayin sawu daya.
Kuma Sa’ayi baya inganta sai dawafi ya gabace shi sai dai ba sharadi ba ne dawafin ya zama na wajibi, mustahabbi ne dangane da sa’ayi a sami sharadan Sallah acikinsa, banda fuskantar alkibla da tsayuwa akan dutsan safa da na marwa, da yin addu’a a kansu, kuma wannan ba shi da wata iyaka.
Lallai mutun ya guji abin da wadansu suke yi danga ne da gudu daga safa zuwa marwa sai dai namiji ba macce ba shi ne zai yi sauri a tsakanin alamomin nan koraye guda biyu.
Amma idan ya yi sassarfa a cikin sa’ayinsa gaba daya sa’ayinsa bai 6aci ba sai dai ya munana.
Wannan hukunci dai dai ya ke da idan bai yi sassarfar ba ma gaba daya.
.
RUKUNI NA HUDU (4)
——————–
Tsayuwa a Arfa gwargwadon wani lokaci a daran ranar yanka, amma tsayiwa a kan abin hawa shi yafi sai dai idan dabbar tasa tana da wani uziri. Haka kuma tsayuwa tafi zama. Kuma tsayuwa da rana tare da liman wajibace idan mutun ya barta sai ya zubarda jini.
.
FASALI:
————-
Umra sunna ce sau daya a rayuwa, kuma rukunanta sune rukunan hajji, ban da tsayuwar a arfa, sannan tana da mikati guda biyu, na guri wanda shi ne mikatin aikin hajji, sai dai dangane da wanda yake a Makkah domin shi zai fita ne zuwa gurin da ba na aikin hajji ba ya dauro niyya daga can. Amma abin da yafi shi ne Dauro niyya daga ja’ir nata mikati na lokacin, shi kuma shi ne dukkanin kwanakin shekara. yadda ake daura niyyar ta kuwa
Ya danganci mustahabbancin wanka da tsaftacewa. Da irin tufar da ta halarta ya sanya da wadda ta haramta gare shi, da sanya turare da sauransu, kamar dai aikin hajji.
Kuma makaruhi ne a mai-mai ta (Umra) acikin shekara guda.
Sannan Umra tana 6aci da Yin jima’a da abin da ya dangance shi. In dai ya faru kafin a kammala rukunanta.
.
KAMMALAWA
——————
Idan mutun (mahajjaci) ya fita daga Makka. To niyyarsa da abin da ya sa gaba ya zama shi ne ziyarar Annabi (S.A.W) domin ziyartarsa (S.A.W) sunna ce da aka yi ijjima’i a kanta, kuma daraja ce da aka kwadaitar acikinta.
Idan mai ziyara ya nufi Annabi (s.a.w) kada ya hada kowa da shi, domin shi Annabi (S.A.W) abin bi ne ba mai bi ba ne ga wani.
Kuma mustahabbi ne mutun ya sauka a wajen madina, yayi wanka ya sanya turare kuma ya sanya mafi kyawon tufafinsa. Sannan idan ya shiga masallaci ya fara yin sallah idan lokacin ya halatta ayi nafila a cikinsa,
Idan kuwa ba haka ba sai ya fara nufar kabari mai daraja, amma kada ya danfara a jikinsa, sannan ya bawa alkibla baya ya fuskanci kabari mai daraja ya ce:
ASSALAMU ALAIKA AYYUHAN-NABIYYU WARAHAMATUL-LAHI WABARAKATUHU,
Sannan ya gusa wajan damarsa gwar-gwadon zira’i ya ce: ASSALAMU ALAIKA YA ABABAKAR ASADDIK,
Sannan ya kuma gusawa zuwa wajan damarsa gwar-gwadon zira’i ya ce:
ASSALAMU ALAIKA YA ABA HAFSIN UMMARUL-FARUK,
Kuma ya zama yana yin sallama duk lokacin da ya shiga ko ya fita.
.
Allahu wa’alamu wannan shine cikakken bayanin aikin hajji, muna rokon Allah ya amfanar da Al-ummar musulmi gabaki daya, ‘Yan uwa Don Allah kuyi #COMMENT da #LIKE, da #SHARE domin Sauran Yan uwa su ma su gani su amfana.

Advertisements