GA YANDA AKE GUDANAR DA
Tsayuwar Arafat Da Muhimmancin TSAYUWAR TA ARAFAT.
.
Manzon Allah (SAW) ya ce “Hajji ita ce Arfa.’’ Wannan jimlar tana nufin dukkanin ayyukan Hajji da hukunce-hukunce ta yana rana daya ne wato ranar Arfa. Ma’ana aikin Hajji yana zama cikakke ne idan mahajjaci ya yi tsayuwar ranar Arfa tare da sauran mahajjata, kuma ya bi dukkannin dokoki da sharuddan aikin Hajjin. Idan dai mahajjaci bai tsaya tsayuwar Arfa ba, ko da kuwa ya yi kwanaki ne da dama a garin Makkah to hajjinsa ba ta yiwu ba.
.
Sunan Arfa an ambace shi da yawa a cikin Hadisan Manzon Allah (SAW): ko kuma cewar Hajji ita ce Arfa( kamar yadda Imam Ahmad da wasu hudu daga cikin masu ruwaito hadisi). An ambaci sunan Arfa a cikin suratul bakara (2:198).
Da akwai fassarori da dama da aka yi akan me ya sa wannan rana ake cewa da ita ranar Arfa, amma har yanzu babu wani kwakkwaran hadisi kuma ingantacce da wanda yake da alaka da cewa Manzon Allah (SAW) ya ce. Amma duk da haka malamai a cikin littattafansu sun rubuta akan akhbar ko kuma labarurrukan da. Saboda haka ga wasu daga cikin ra’ayoyin wadannan malaman kamar haka:
Arfa waje ne da Annabi Adamu da Hauwa’u suka hadu bayan an sauko da su daga aljanna. Kowanne daga cikinsu an sauke shi a waje daban, amma daga baya sun hadu a wannan wajen da ake kira da Arfa. A nan ana nufin Arfa tana nufin wajen sake haduwa da wanda ka sani. Masu wannan ra’ayin suna ganin Annabi Adamu da Hauwa’u sun sake haduwa a wannan fili da ake cewa Arfa.
A lokacin da Mala’ika Jibrilu ya zo ya koyawa Annabi Ibrahim
(AS) hukunce-hukunce n aikin Hajji da kuma nuna masa sauran wuraren ibada, sai yace masa ‘’A’raft’’? ko kuma ka gane wannan? Shi kuma Annabi Ibrahim (AS) sai ya mayar masa da ‘’Araft’’ ko kuma e na gane. Don haka ake cewa da wannan waje Arfah, wato ya koyi wani abu.
.
Waje ne da mutane suke sanin juna wato Arafa. Tunda wannan waje yana zama inda mahajjaci yake zama tun safe har zuwa faduwar rana, wannan yana bawa mahajjata damar sanin mutane. Don haka tunda mutane suna samun damar sanin junansu don haka ake kiran wannan waje da Arafah.
Kalmar A’rf tana nufin kamshi, kuma tunda wannan fili na Arfah waje ne da ake kyautata zaton samun rahamar Ubangiji da yafiyarsa a wannan waje, mutane suna kwatanta wannan waje da wannan ranar da wadannan mutane da suka halarci wannan waje da cewar suna kamshin ‘’Arafah’’. Haka kuma saboda rahamar data ke sauka a wannan waje a kan wannan dutsen da mahajjata suke haduwa ake cewa da wannan dutsen , dutsen rahama.
Duk da wannan sabanin ra’ayi da aka samu akan malamai na dangane da sunan wannan rana ta Arfah, babu wanda zai musanta ko kalubalanci muhimmancin wannnan rana da kuma irin ladar da mahajjaci zai samu.
.
Za mu kawo ayyukan Hajji da suka zama wajibi ga kowane mahajjaci.
A wannan rana ta Arfah yawancin mahajjan suna Mina. Za su yi sallar asubahi a tantinansu da ke Mina, idan rana ta fito kuma sai su fara shirye-shiryen tafiya.
Tafiya daga Mina zuwa filin Arfah babu nisa, amma saboda cunkosan mutane da ababan hawa sai a dade ba a je ba.
.
Yayin da mahajjata suka dau niyyar tafiya daga Mina zuwa Arfah za su yi ta fadin ‘’lab-bayka Allahumma lab-bayk, lab-bayk laa sharika laka labbaik, innal hamda, wan ni’imata, laka wal mulk, lashari kalak’’. Wannan talbiyah da za su rinka yi shi ne yake nuni da wannan tafiya sun yi tane domin Allah, kuma su bautawa Allah shi kadai.
.
Idan mahajjatan sun isa filin Arfah kowa zai tsaya a tantinsa har lokacin kiran sallah.
A lokacin da Manzon Allah(SAW) ya isa fiilin Arfah kafin sallar azahar ya tsaya ne a inda masallacin Masjid Namira yake wanda ake kira a da da Wadi Urana.
Ba kamar yadda aka san masalllacin a yau ba, gaban masallacin baya cikin filin Arfah inda Manzon Allah (SAW) ya yi hudubarsa. Bayan ya gama hudubarsa sai ya jagoranci mahajjata suka gabatar da sallar Azahar da La’asar a hade, sannan ya shiga cikin filin Arfah har rana ta fadi.
Idan lokacin sallah ya gabato limamin da ya gabatar da Huduba zai tashi a cikin wannan taro da suka hadu a masallacin Namira da kewayensa ya gabatar da huduba mai taken hudubar Arfah. Sannan sai a yi kiran sallah, liman zai jagoranci sallar Azahar da La’asar a hade, kowacce za ayi ta raka’a biyu, kiran sallah daya da ikama biyu.
Wannan huduba ana nunata a ko’ina a kasashen duniya. Wani babban kuskure da mahajjatan suke yi kuwa shi ne na bin limamin da yake masallacin Namira wanda ya kan kasance da akwai nisan mila-milai tsakaninsu da limamin, maimakon kowanne tanti ya yi sallarsa daban ba tare da yin wata hudubar ba, wadda limamin masallacin Namira ya yi ta wadatar.
Da an idar da sallah mahajjata sai su koma tantinsu domin samun fakewa daga zafin ranar Saudia. Dole ne mahajjata su tsaya a cikin filin Arfah wanda aka yi wa sheda da wani katon allo da aka yi wa fentin ruwan dorawa, an kafa shi a ko’ina. Dole ne mahajjata su tsaya a cikin wannan fili har zuwa faduwar rana, duk wanda bai tsaya ba kuwa hajjinsa ta baci.
Mahajjata suna amfani da wannan ranar ne gaba dayanta suna addu’o’i da zikiri da neman rahama da gafarar ubangiji har zuwa faduwar rana. Mahajjata za su iya karanta al-kur’ani da sauran addu’o’i, amma abinda aka fi so mahajjaci ya yawaita yi shi ne talbiyya.
Duk da cewa azumtar ranar Arfah abu ne mai kyau, an yi hani ga mahajjaci ya azumci wannan rana. Koyarwar Manzon Alllah (SAW) ce mahajjaci ba zai azumci wannan rana ta Arfah ba. Ya yi amfani da sauran kuzarin daya ke da shi domin bautar Ubangiji
Bayan sallar La’’asar yanayin filin Arfah sai ya canza, zaka ga dubban mutane sun dage suna ta addu’o’i kafin rana ta fadi, domin samun dacewa.
Mutane wasu a zaune, wasu a tsaye, wasu akan motocinsu, wasu akan hanya wasu gefen hanya, wasu akan dutsen rahama sun daga hannuwansu sama suna ta addua’a, wasu suna kuka domin Allah ya gafarta mana zunubanmu ya ‘yanta mu.
.
Babu wata rana a wajen Allah kamar ranar Arfa. A wannan rana ne Allah zai kusanto ga duniya, kuma zai zama yana alfahari da bayinsa na duniya, har ya ringa cewa ‘yan aljanna ’’ku kalli bayina, sun zo daga wurare masu nisa da kuma wadanda suke kusa, fuskokinsu duk kura suna neman rahamata’’. Ana ‘yanta mutane da dama daga cikin wutar jahannama a ranar Arfah fiye da kowacce rana’’ ( Abu Ya’la, Ibn Khzayma, Al-Bazzar da Ibn Hibban).
Abu Ad-Darda ya rawaito Manzon Allah (SAW) yana cewa babu ranar da Shaidan ya tsana kamar ranar Arfah, saboda a ranar ne yake raina kansa da kansa, an kaskantar da shi da ringa jin haushi. Dalilin jin haushin Shaidan kuwa a wannan rana shi ne saboda Ubangiji yana ‘yanta bayinsa da dama a wannan rana, babu wata ranar da ta kai wannan ‘yanta bayi sai dai ranar yakin Badar, wanda Ubangiji ya ‘yanta bayinsa da dama a wannan ranar, wannan ya sa Shaidan yake kasance cikin kunci a wannan rana.
Idan rana ta fadi , sai Mahajjata su fara haramar komawa Minna. Kafin su isa Mina za su tsaya a Muzdalifa, dole ne Mahajjaci ya tsaya a Muzdalifa ya yi sallar magriba da isha’i a hade. Sallar magriba ana yin raka’a ukunta cikakkiya, sallar isha’i kuma ana yin raka’a biyu.
Sunnar Manzon Allah (SAW) ce ya tsaya ya huta a Muzdalifa, babbar ibada a Muzdalifa ita ce mutum ya kwanta ya yi barci. Mahajjaci ya kamata ya yi amfani da wannan damar domin ya huta, saboda yini guda da ya yi a filin Arfah yana ibada, sannan kuma ya yi shirin wayewar gari wato ranar Nahr, ranar Idi.
.
An yi wa Mahajjaci afuwa, zai iya barin Muzdalifa kafin safiya, idan ya yi rabin dare sai ya kama hanyar komawa Mina, saboda cinkoson mutane da abin hawa. Tsofaffi da marasa lafiya da masu nakasa an yi musu izini su bar Muzdalifa da wuri kafin cinkoso ya yi yawa.
Idan safiya ta waye Mahajjata za su cigaba da ayyukansu, kuma ranar ce ranar sallah wato 10 ga watan Zul Hijja.
Tsayuwar Arafat
Bayan da mahajjaci ya shiga kayansa na Ihram cikin niyyarsa ta barin Makka, zai fara tafiyarsa ne inda zai yi kudurin fuskantar gabas (Arafat) zai kuma kasance a can ne har zuwa lokacin kusa da faduwar rana ta tara da wata. A kan hanyar dawowa Mahajjaci zai zai dan yada zango a Mashar daga nan sai Mina.
Sabanin abubuwan da aka fada maku za’a fara tafiya sannu a hankali, daganan sai tafiya ba kakkaftawa cikin farin ciki kan hanya zuwa Arafat ba tare da tsayawa ba, wannan kuma daga safe a rana ta goma zuwa sha biyu ga wata ( ko kuma sha uku wannan fa ba tilas ba ne sai idan mutum ya yanke shawara ta kasancewa a Mina .
.
Babu wata alama da za ta bambanta wurare uku, daga nan sai wata hanya da take mil sha biyar ne wadda ta hade da Makka. A kan hanyar babu wasu abubuwa da suke nasaba da tarihi ko addini, ko kuma wani manuni da ya bambanta wannan wuri zuwa wancan. Su iyakun sun suna nunawa ne yadda ayyukan da za ka yi na Hajji suka bambanta da juna.
Wani muhimmina al’amurri ne muhimmancin da za’a danganta da tsayawa su wuraren da suka kasance matakai ne kansu na daga cikin ayyukan da Maniyyaci zai yi. Dalilan da suka sa aka ba da shawarar ya zarce da duk wani abin da mutum zai tunani akan ranar Arafat wato tara ga watan Zulhajj, ko kuma kasancewa a Mashar saboda a tsinci duwatsun jifar Shaidan saba’in.
Ya zama da’iman a tsaya a Mina ranakun goma sha daya da goma sha biyu saboda su ne kwanaki biyu da suke bin ranar da Maniyyata ke yanka dabbobi na layya da ta kasance goma ga watan Zulhajj. Koda yake dai wannan yana nuna kamar Maniyatta sun kamala zaman su ne na Mina bayan sun yanka dabbobin layya misalign karfe goma sha biyu na rana bayan yin layya da kuma jifar (Shaidan) amma duk da haka dai sai an dakata a Mina.
.
Wannan ba wai ya nuna an tsaya ba ne domin zama, al’amarin ya wuce hakanan domin kuwa kamata ya yi idan ayarin tafiyarku ya tsaya ka tsaya, idan kuma za’a cigaba da tafiya sai ayi hak anan. A duk wurin da aka tsaya sai ku tsaya saboda ita Mina ta kasance wuri ne da za’a yi kwana uku.
Ya kuma kamata a lura ba wurin da za’a je ba ne fa’ida, amma yaushe ne za’a kammala, ko ina shi wannan ayari na ku ya dosa, ko kuma ku ina kuka niyyar zuwa?
Duk wadannan ba wasu abubuwan da za su sha maku kai bane , saboda kuwa manufa ita ce ana bukata ne ta a kara jaddada maku shi aikin Hajji yana daga cikin rukunan musulunci wadanda suka rataya ga ko wane musulmi ko musulma su samu wata dama ta yin haka a rayuwar sa, idan dai da halin yin haka din.
.
Ita wannan ziyara ta Ibada ana yin ta ne saboda Allah Subahanahu Wata’ala, kuma dukkan ayyukan da ake yi lokacin suna daga cikinn ibada kamar yadda ya bada umarnin a yi.
Dukkan al’amura da abubuwa masu karewa ne amma ikon Allah shi zai kasance ko wane lokaci Kur’an 29: 88
Za’a fara daga Makka a tafi kai tsaye zuwa Arafat, daga nan kuma daga wannan rukuni zuwa wancan har a dawo zuwa ga Ka’aba.
Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma: (alkur’an 2: 56.)
Abubuwan da aka yi bayani akan sun kunshi alaka ne zuwa da dawowa, a kwai tafiye tafiye da ake yi da zummar zuwan ba ne da za’a je kawai, amma don a cimma wasu muradu. Shi yasa wurin wani abu shi ya sa al’amari na aikin Hajji duk ya kunshi tafiye tafiye ne. Ko da yake ana iya cewar ba tafiye tafiye ba ne saboda suna da karshe, shi aikin Hajj ana son a cimma wani buri ne don haka shi ba wani wuri ba wani wuri ba ne da za’a je amma wai buri da ake bukatar cimmawa. Shi ya sa idan Mahajjata sun dawo daga Arafat za su ya da zango ne a Minna a bayan Ka’aba ba kuma cikin dakin Ka’aba, wane shi ne ake nufi da muradi ba wai a isa ba.
A cikin aikin Hajj akwai rukunai masu karfi da suka hada da ( Arafat, Mashar da kuma Mina) wadanda ayyuka ne da suka kamata dole ne sai an yi su. Ba kawai don yin ziyara ne za’a je wuraren ba. Ya kuma kamata a lura sosai don bayanin muhimmancin da aka yi akan yada zango a duk ko wane mataki, sai kuma ayyukan da za’a yi wadanda kuma sun bambanta a wuraren da za’ yi aikin ibada.
Wadannan wurare uku a naku ganin me suke wakilta wato ayyukan ibada da suka sha bamban da juna? Allah madaukakin Sarki da kan shi ya ba su sunaye masu ban al’ajabi don muhimmacin su a musulunci.
Arafat tana nufin’’ Ilmin kimiyya’’ yayin da Mashar ita tana nufin ‘’Hankali da Fahimta’’ sai kuma Mina wannan ‘’ Soyayyar mahaliccin mu Allah ce tare da kuma Imani da wadannan abubuwan da ya muka san su suka kuma kasance kamar darasi ne ga mu’’.
Tafiya daga Makka zuwa Arafat (Ya Allah wurin ka dukkan bukatunmu suke karbuwa) sai kuma komowa daga Arafat zuwa Ka’aba (Allah mai girma gare ka duk zamu koma).
Arafat tana a matsayi ne na fara halittar dan Adam. A tarihin Annabi Adamu ( Halittar mutum a doron kasa). An ruwaito cewar bayan da Adam ya bayyana a doron kasa cikin ikon Allah ya samu Hauwa’u ne a Arafat kuma a can ne suka fara fahimtar juna sosai har suka kai ga shakuwa. Daga nan sai aka umurci Adam ya bar wurin( bayan da ya aikata laifi) ba kuma ita ce (Aljannar) da aka yi albishirin samu ga duk wadanda suka rayuwa ta gari, kowa ke muradin samu bayan ya kammala rayuwar sa ta duniya.