Manzon Allah (SAW) Yace “Babu
wata rana da Allah
(SWT) Yake ‘yanta bayi dayawa
daga wuta kamar ranar Arafa.
A wani Hadisin da As-habus-
Sunna suka ruwaito, Manzon Allah (SAW)
Yace “Mafi Alkhairin addu’a itace
addu’ar Arafa, kuma mafi falalan
Abinda na fada ni da
Annabawan da sukazo kafin ni
shine “LA’ILAHA
ILALLAHU WAHADAHU LA
SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU
WA LAHUL
HAMDU WAHUWA ALA KULLI
SHAI’IN QADEER” .
Saboda haka ‘Yan Uwa muyi
kokari mu dage da fadar
wannan Azkhar A wannan rana
ta Arfat domin neman Babban
Rabo daga Allahu (S.W.T) Ya Allah ka Azzirta mu da shiga
Aljannar fir-dausy don darajar
wannan rana mai Tarin albarka.
Allahumma-Amin.

Advertisements