Abin da ya sa ba a hada sunayen ministoci da ma’aikatunsu ba – Sanata Enang
.

Babban Mai tallafa wa Shugaban kasa kan Harkokin Majalisar Dattawa Sanata Ita Solomon Enang ya ce dalilin da ya sa Shugaban kasa bai hada sunayen ministocin da ya mika ga majalisar tare da ma’aikatunsu ba, shi ne idan ya yi hakan duk lokacin da za a sauya wa wani minista wurin aiki sai an koma majalisar.
.
Sanata Ita Enang, wanda yake magana a gidan Rediyon Tarayya, ya ce shugaban kasa ya tura sunayen ne domin a tantance su a matsayin ministocin Najeriya, hakan zai ba shi damar tura mutum duk ma’aikatar da ya ga dama. “Amma da ya hada sunan ministan da yake son nadawa tare da ma’aikatarsa ya tura wa majalisar, babu dama ya sauya wa wancan minista ma’aikata sai ya sake komawa majalisar ya nemi amincewarta, wanda hakan yana iya kawo tsaikon aiki a ma’aikatu,” inji shi.
.
Majalisar Dattawan dai ta tantance mutum 18 daga cikin 37 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata yana son nada su ministocin gwamnatinsa.
Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki ne ya jagoranci zaman tantance mutanen inda aka amince da ministocin daya bayan daya.
A ranar Talata majalisar ta tantance mutum 10 sannan shekaranjiya Laraba ta tantance mutum 8, sai dai a yayin da ake sa ran ta ci gaba da tantance sauran ministocin a jiya ne sai majalisar ta bayar da sanarwar cewa sai ranar Talata mai zuwa za ta ci gaba da tantance sauran.
.
A yanzu dai akwai mutum 19 da ke jiran a tantance su, inda za su gurfana a zauren majalisar don amsa tambayoyi kan batutuwa da dama. An dai tantance minsitoci 18 din ne daga zubin farko na mutum 21 yayin da za a hada sauran biun da zubi na biyu don tantancewa. Ministocin zubin farko da ba a tantance ba su ne tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi wanda ake jiran rahoton Kwamitin da’a da Sauraren koke-koken Jama’a na majalisar da ke binciken wani korafi a kan zarginsa da almundahana kafin ta tantance shi, da kuma Adebayo Shittu daga Jihar Oyo, mutum na uku a zubin farko, Alhaji Ahmed Ibeto daga Jihar Neja, Shugaba Buhari ya janye sunansa.
Ministocin da suka tsallake siradi sun hada da Sanata Udoma Udo Udoma daga Jihar Akwa Ibom DA Kayode Fayemi daga Ekiti da Audu Ogbeh daga Benuwai da Ogbonayya Onu daga Abiya da Osagie Ohanire daga Edo da Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga Kano da Alhaji Lai Muhammed daga Kwar da Hajiya Amina Mohammed daga Gombe da Injiniya Sulaiman Adamu daga Jigawa.
Sauran su ne: Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga Nasarawa da Babatunde Raji Fashola daga Legas da Ibe Kachukwu daga Delta da Alhaji Abubakar Malami (SAN) daga Kebbi da Hajiya A’isha Alhassan daga Taraba da Barista Solomon Dalung daga Filato da Sanata Chris Ngige daga Anambra da Sanata Hadi Sirika daga Katsina da Misis Kemi Adeosun daga Ogun.

Advertisements