An kama wasu matasa kan yi wa budurwa fyade
.
An gurfanar da wasu matasa uku a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Tashar Babiye a garin Bauchi bisa zarginsu da sace wata budurwa (an sakaye sunanta) da ke zaune a Unguwar Nuru Kwatas a garin Bauchi, inda suka yi mata fyade.
Mai gabatar da kara a kotun dayyabu Ayuba ya ce a ranar 27 ga Satumban bana da misalin karfe 4:00 na yamma, matasan da suka hada da Shafi’u Mohammed mai kimanin shekara 21 da Ahmed D. Hassan mai shekara 22 da Mohammed Usman mai shekara 23, sun sace budurwar suka kai ta dakinsu a Unguwar Sabon kaura a wajen garin Bauchi inda suka yi mata fyade. Ya ce yin haka ya sava wa sashi na 129 da na 95 na dokokin manyan laifuffuka na Jihar Bauchi na shekarar 2000.
Da kotu ta tambayi wadanda ake zargin dukkansu sun amince cewa kowane dayansu ya yi lalata da ita.
Alkalin Kotun Mai shari’a Is’hak Magaji ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Oktoban nan domin yin nazari da yanke hukunci.

Advertisements