Kaka da jikanyarta suna jayayya kantakardun gida

Kaka da jikanyarta na jayayya kan takardun gida
.
ARan Alhamis ne Kotun Shari’ar Musulunci ta biyu da ke Magajin Gari a cikin garin Kaduna ta saurari kara kan rikici tsakanin kaka da jikanyarta a kan takardun gida.
Wacce ake kara ita ce Hajiya Maryam Sidi, wacce kuma kaka ce ta wajen uwa ga mai kararta, watau Aisha Ibrahim.
Ita Aisha ‘yar shekaru 23 da haihuwa, ta shigar da kara ne domin a taimaka wajen karbo mata takardun gidan da ta gada da ke hannun kakartata shekaru bakwai da suka wuce.” Tun bayan rasuwar mahaifina babu wani ko wata mata da tallafa mani a matsalolin rayuwata fiye da mahaifiyata, wadda a yanzu haka tare da ita nake zaune a Chiranchi dorayi, Kano.’’
“ Tun da na sayi gidana a kan kudi Naira milliyan goma a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2008 a Kaduna, Hajiya Maryam Sidi kakata ta wajen uwa ta karbe mani takardun gidana, yau shekaru bakwai ke nan ba ta ba ni ba, kuma ba ta da niyyar bayarwa,” inji Aisha, a cikin wata takardar koke da ta shigar kotu wanda aka rubuta a ranar 20 ka watan Satumbar 2015.
Aisha ta kuma shaida wa kotu cewa, yau shekara goma sha bakwai ke nan da rasuwar mahaifinta. Ta ce gidan nata na gado na nan a kan titin Kinkinau a GRA ne a Unguwar Rimi Kaduna, kuma duk kokarinta na ganin kakartata ta ba ta takardun gidan ya ci tura.
Ita kuwa Hajiya Maryam a bayaninta a cikin Kotu, ta fada wa alkali cewa mahaifiyar Aisha ce ta ba ta takardun gida ta rike ba Aisha ba, saboda haka ba Aisha ya dace ta tambaye ta takardun ba.
“ Bayan haka ina ganin idan na bai wa Aisha takardun nan tana iya salwantar da dukiyar kuma daga baya a dawo suna damuwa, ni kuma ba zan so ganinta da kanwarta a cikin damuwa ba.’’ Domin akwai rumfuna da ita Aisha suka sayar tare da salwantar da kudin, shi ya sa ita kuma ta ki ba ta takardun gidan.
Shi ma lauyan wanda ake kara Barista Nuhu Ibrahim, ya fada wa kotu cewa, fahimtar wacce ake kara ita ce, ita Aisha ba ta mallaki hankali ba da za ta iya rike wannan dukiya, saboda gudun salwantar da dukiya ya sa ba a ba ta takardun ba.
Sai dai ita kuma Aisha ta musanta cewa ba ta mallaki hankalinta ba, inda ta fada wa Alkali cewa shekarunta 23 da haihuwa kuma tana da cikekken hankalin da za ta kula da dukiyarta, domin a yanzu haka ita daliba ce da ke karatun digiri a kasar waje, sannan nan tana sa ran yin aure a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2015.
Alkalin Kotu Mai Shari’ah Aliyu Muktar ya dage saurarar karar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba 2015, tare da bukatar wacce ake kara da ta tabbatar ta kawo wa kotu takardun wannan gida.

Published by Lecturer Aminu Muhammad kaura

Lecturer Aminu Muhammad Kaura Namoda LG zamfara state Nigeria.

Leave a comment