Zan kafa kamfanonin siminta a kasashe 18 – dangote
.
Alhaji Aliko dangote Shugaban Rukunonin Kamfanin DangoteA makon jiya ne fitaccen dan kasuwar nan kuma mai kudin Afirka Alhaji Aliko dangote ya kaddamar da sabon kamfaninsa na yin siminti da ya ci Dalar Amurka miliyan dari shida (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 250) a kasar Tanzaniiya. A tattaunawarsa da wakilinmu a can ya bayyana cewa yana shirin kakkafa kamfanonin siminta a kasashe 18 na Afirka da kuma kasar Nepal da ke yankin Asiya:
Aminiya: Me ya jawo hankalinka ka gina wannan kamfani a Tanzaniya?
dangote: Mun fara gina wannan kamfanin ne tun ran 7 ga watan Mayun shekarar 2013. Ga shi yanzu za a kadamar da kamfanin. Tanzaniya tana daya daga cikin kasashen Afirka da ake yin kasuwanci mai alfanu. Kuma gwamnati ke yin jagorancin kawo masu zuba jari cikin kasarta da gudunmawar bankuna da hanyar sadawar mai kyau da kuma tanadin doka. Jin dadin haka ya sa za mu zuba hannun jari a harkar gona a nan gaba. Kuma muna fata wasu ma za su zo kasar Tanzaniya don zuba jarinsu. Don haka ya sa arzikin kasar ke bunkasa har da kashi bakwai cikin 100 kowace shekara. Bankin Duniya ya nuna cewa in har kasar ta ci gaba da haka za ta samu bunkasa matuka. Kuma kamar yadda magabatan Afirka suka zayyana a kalmar Swahili wato Ujama, ma’ana Afirka ta farka, wato sai ’yan Afirka kadai ne za su iya daukaka Afirka. Bugu da kari na lura cewa ana ta yin gine-gine a Tanzaniya amma suna shigo da siminti ne daga waje, da na ga suna da dutsen hada siminta shi ya sa na zo don in zuba jari a wannan kasa. Akwai kuma wasu fagagen da za a iya zuba jari a cikinsu kamar bangaren noma da yawon bude ido da sauransu.
Aminiya: Me kake burin cimmawa?
dangote: Kamfanonin da ke nan zun gaza wajen wadatar da kasar da siminti, kuma muna da kwarewa don mun kafa kamfani a Habasaha da Kamaru da kuma Zambiya. Za mu ci gaba da daukaka kasar Tanzaniya domin ganin ta cimma burinta da kuma karuwar arziki da samar da aikin yi da dai sauransu.
Aminiya: Me ke jan hankalin masu zuba jari zuwa wata kasa?
dangote: Samun hadin kai daga kasar da alamun samun riba da zaman lafiya da lumana. Wannan ya sa na zuba kudi har Dala miliyan dari shida don in kara karfafa ci gaban kasar da kara daukaka zaman lumana da samar da aikin yi ga jama’a da dama.
Aminiya: Ka ce za ka wadata kasar Tanzaniya da siminti, bayan haka za ka fitar da shi zuwa kasashen waje ke nan?
dangote: Muna sa ran haka domin idan Tanzaniya ta wadata, to za mu sallama wa kasashen Mozambikue da Madagascar da sauran makwabta don su ma su inganta kasuwanci da gine-gine. Domin Tanzaniya tana da dutsen da ake sarrafa shi zuwa siminti da dama, kamar wannan waje akwai fiye da tan miliyan dari biyar (na irin wannan duste). Wannan ya ba ni kwarin gwiwa na kafa wannan kamfani a nan Mgao maimakon a birnin Daris Salam.
Aminiya: Shin ko za ka fadada kasuwancinka zuwa wani bangare?
dangote: Ina da burin zuba jari a aikin gona da na tashar fito da jiragen ruwa. Kuma alfanun da kasar za ta samu sun hada da karuwar kudin shiga. Mu dai muna neman addu’a ne domin shi ya sa muke da burin daukaka Afirka, shi ya sa muke ta zuba jarinmu a nan kasar domin muna son ci gaban Afirka gadan-gadan ba mu kai wani bangare na duniya ba.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da kirkiro shirin Ujuma a harshen Swahili wato ’Yan Afirka ne kadai za su inganta Afirka da magabata suka yi?
dangote: Lallai Afirka ce kadai za ta iya inganta kanta, amma ba wasu daga wata kasa ba. Kuma mun yunkuro, domin ta hanyar kasuwanci za a iya cimma haka a daukaka Afirka nan ba da dadewa ba. Ina yin tuni cewa, Afirka a matsayinta na nahiya mai tasowa, tana da kalubale da dama da sai an dage matuka sannan za a ci nasara a kansu. Wannan ne ya sa na ga ya dace ’yan kasuwa su tallafa don daukaka wannan yanki. Wannan ya sa muka ga ya dace mu ba da gudunmawa don daukaka Tanzaniya kamar yanda muka kuduri yi a sauran kasashen Afirka.
Aminiya: Ta wane irin yanayi ne za a inganta zuba jari a Afirka?
dangote: Zuba jarin ’yan kasuwa don tallafa wa gwamnatoci ya dace a bangaren daukaka kasa don haka shi ne mafita, saboda sai an tallafa wa gwamnatoci kafin a samu daukaka gaba daya na al’umma. A takaice wannan kamfani kamar yadda muka kudiri yin wasu kamfanonin siminti guda 18 na cikin shirinmu na bunkasa Afirka. Kuma wannan kamfanin a Tanzaniya yana daya daga cikin kamfanonin siminti da aka yi saurin kammalawa domin an yi haka ne ne a cikin kimannin wata 20. Bugu da kari a watan Agusta ne muka kaddamar da na kasar Kamaru da na Zambiya. Sannan an kaddamar da na kasar Habasha mai samar da tan miliyan biyu da rabi a shekara. Amma kamfanin Tanzaniya shi ne kamfanin siminti mafi girma a yankin Afirka ta Gabas da Afirka ta Tsakiya.
Aminiya: Mene ne kudirin kamfanin dangote a harkar zuba jari?
dangote: Kafin karshen wannan shekara, muna son kaddamar da kamfanonin dangote a kasashen Senegal da Afirka ta Kudu, sannan sauran muna sa ran a kaddamar da su a shekarar 2016. A watan Agustan da ta wuce a birnin Legas muka ba da kwangilar Dala miliyan hudu da dubu 340 domin kamfanin SINOMA na kasar China ya gina mana sababbin kamfanoni guda goma a fadin Afirka da daya a kasar Nepal da ke yankin Asiya. Kuma ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da zuba jari.
Aminiya: Mene ne yawan saminiti da dangote ke samarwa?
dangote: Ya kai kimanin tan miliyan 25 a kowace shekara. Kuma nan da shekara biyar masu zuwa muna sa ran zai kai tan miliyan 81, wanda wannan zai sa mu zama daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a duniya. Kuma kamfanin dangote Cement PLC shi ne kamfani mafi girma da ke zuba jari ba ma kadai a Najeriya ba har ma da yankin Afrika ta Yamma. Kuma muna da burin fara hada-hadar hannun jari a Cibiyar Hada-Hadar Hannun Jari ta New York da ke Amurka da kuma ta Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu cikin shekara biyu masu zuwa. Amma duk wadannan nasarori suna samuwa da gudunmawar gwamnatoci da kuma jama’a.
Aminiya: Wace gudunmawa talakwan wannan yanki za su samu daga wannan kamfani?
dangote: Tsarin wannan kamfani ne ya tallafa wa jama’ar inda kamfaninmu yake. Don muna gina kasuwa da makaranta da sauransu kamar yadda muka yi a Obajana da Gboko a Najeriya. A nan Tanzaniya za mu yi hakan kuma har mun raba Dala rabin miliyan ga marasa karfi da ke wannan yanki.
Aminiya: Wadanne kalubale ka ci karo da shi a nan Tanzaniya?
dangote: Ba mu yi saurin fahimtar yadda dokar kasar take ba. Wannan ne ya sa muka dauki lokaci tun shekarar 2008 muna tattaunawa. Amma daga baya mun zauna da Shugaban kasa da Firayi Minista har tsakar dare muna tattaunawa sannan muka samu fahimtar juna