YANDA AKE SALLAR JANA’IZA
.
GA YANDA AKE SALLAR JANA’IZA, DA GAGA RUMAR GARA 6ASAR,LADAR DAKE GA DUK WANDA YAJE AKA YITA DASHI.
Itadai sallar jana’iza farilla ce ta kifaya (wasu na dauke ma wadansu ita)
Rukunanta guda biyar ne Gasu kamar haka:
.
NA DAYA:yin Niyyah.
NA BIYU:tsayuwa [awajen yinta]
NA UKKU: kabbara shine ayi kabbarori guda hudu. [4] amma ko liman ya qara kabbara ta biyar sallarsa da ta wadanda suke bin sa ba ta baci ba, sai dai za su yi sallama ne ba za su saurare shi ba.
_kuma musta habbi ne (Anso) a daga hannu a kabbarar farko kawai.
.
NA HUDU: yin Addu’a ga mamacin da kowace addu’a ta saukaka. Ba mustahabbi ba ne a yi wata Addu,a ta musamman (ma’ana, ayi dawata Addua ke6an tacciyaba)
NA BIYAR: Sallama kuma liman zai yi sallama ne guda daya a damansa ta yadda zai jiyar da kansa da wanda yake binsa, sannan mamu ma ya yi sallama guda daya, ya jiyar da kansa kawai, amma ba zai mayar da sallama ga liman ba.
.
Sallar Jana’Iza tana da
kabbarori guda hudu (4)
KUMA
Kowa ce, Da Abinda Ake fada A
Cikinta. (1). KABBARA TA FARKO Ana karanta
{suratul- fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko
wata A’yah
(2) KABBARA TA BIYU Ana karanta
Salatin Annabi (s.a.w) bawani salati na daban da aka ke6e
(3)
KABBARA Ta Uku Ana yin addu’a ga Wanda
yamutu mace ko Namiji
(4) KABBARA TA
HUDU Zakayi addu’a ne a Kanka da Sauran
Al’ummar Musulmi.
.
ga wata Addua daga cikin Addu’o’in da manzon Allah [S.A.W] yayi alokacin sallar janaza
Kuma daga Abu Hurairah [R.A] ya ce:
Manzon Allah [S.A.W] ya kasance idan yana sallah a bisa jana’iza yana cewa:
“ALLAHUMMA AGFIR LIHAYYINA,WAMAYYITINA,WASHAHIDINA,WAGA IBINA,WASAGIRINA,WAKABIRINA,WAZAKARINA,WA UNSANA.
ALLAHUMMA MAN AHYAI TAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAMI,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATA WAFFAHU ALAL IMANI.
ALLAHUMMA LA TAHRIMNA AJRAHU
WALA TUDILLANA BA’ADAHU”.
wannan hadisi:
Muslim da mutane hudu suka ruwaito shi.
FASSARA:
Allah kayi gafara ga rayayyunmu,da matattunmu,dawadanda suke ahalarce,dawadanda basanan,da kanananmu,da manyanmu,da mazajenmu,da matayenmu.
Ya Allah wanda karaya shi daga cikinmu to karayashi akan muslunci,wanda kamatar dashi daga cikinmu to kamatar dashi akan imani.
Ya Allah kada ka haramta muna ladarsa kuma kada ka 6atar damu abayansa.
.
GA LADAR DA A KE SAMU WAJEN YIN SALLAR JANA’IZA:
Kuma daga Abu Hurairah [R.A] ya ce Manzon Allah [S.A.W] ya ce:
Wanda ya halarci jana’iza har yayi Sallah a gare ta, to yana da kiradi guda na lada wanda kuwa ya halarce ta har aka bizne, to yana da kiradi biyu na lada,,
Sai aka ce To minene kiradi?? Sai yace “Shine kwatankwacin manyan duwatsu guda biyu”
An gamu akan wannan hadisi kuma daga muslim yace “har aka ajiye ta a qabar”.
Kuma ga Buhari daga hadisin Abu Huraira [R.A] “wanda ya halarci jana’iza har yayi sallah a gare ta aka kuma kare bizneta, hakika zai dawo da kiradi biyu na lada, kowane kiradi kwatankwacin dutsen Uhudu”.
.
ALLAHU WA’A LAMU. ALLAH KA AMFANARDA MUSULMI.
Ya ‘Yan uwa ahakika yanada matukar amfani agunmu mu rika kasan tuwa awajen sallar jana’iza, domin samun wannan gara6asa daga Allahu [S.W.T]
Allah yasa mutace Amin.