TSAYA KA/KI, KARANTA TABBAS ZA KU AMFANA,
BABIN WANDA YAYI KWANA BAIYI SALLAH BA,
Yau zamuyi bayani akan wanda kwana ya kwashesa baiyi Sallah ba.
.
Hadith-26: Kuma Malik Yabani labari, daga zaidi dan As’lama, cewa shi yace: “manzon Allah (s.a.w) Ya sauka domin hutawa awani dare Yana kan hanyarsa ta zuwa makka, sai ya wakilta Bilal yatashesu lokacin Sallah, sai kwana ya kwashe Bilal kuma suma kwana ya kwashesu harsai da suka farka hakika rana tana mai fito wa garesu, sai mutane suka farka hakika suna afirgi ce, sai manzon Allah (s.a.w) Ya umar cesu su hau abin hawansu sufita daga cikin wannan kwaren, kuma Yace: hakika wannan kwaren akwai shedan acikinsa, sai suka hau abin hawansu har sai da suka fita a wannan kwaren sannan manzon Allah (s.a.w) Ya umar cesu da su sauka kuma suyi Alwala, kuma Ya umarci Bilal Yayi kiran sallah ko yayi iqama, sai manzon Allah (s.a.w) yayi sallah tare da mutane, sannan Ya juya zuwa ga resu hakika Yaga halin da suke ciki na razani (saboda kwanan da ya kwasheshu basuyi Sallah ba) sai Yace: “Yaku mutane hakika Allah ya kar6i rayukanmu, da yaso da sai ya maido da ita zuwa garemu acikin wani lokaci ba wannan ba
To idan kwana ya kwashe dayanku daga barin yin sallah, ko ya mance ta, sannan ya tashi afirgi ce zuwa gareta, to Ya sallah ce ta kamar yanda ya kasance yana sallatarta acikin lokacinta”,
Sannan manzon Allah (s.a.w) Ya waiwaya zuwaga Abubakar sai yace dashi:
“Hakika shedan ne ya zowa Bilal kuma shi (Bilal) Yana tsaye yana sallah, sai ya kishingidar dashi,
Bai gusheba yana lallashin sa ( kamar yanda ake lallashin yaro inzai kwana) Har sai da Yayi kwana”
Sannan sai manzon Allah (s.a.w) Ya kira Bilal, Sai Bilal Yabaiwa manzon Allah (s.a.w) labari kamar misalin Labarin da manzon Allah (s.a.w) ya baiwa Abubakar,
Sai (Nan Take) Abubakar Yace:
Na shaida kai manzon Allah ne.
.
Wannan Hadith yana Karan tar damu darussa guda hudu (4):
.
1: ya na nunar damu cewa: Idan kwana ya kwashemu har lokacin sallah ya wuce bamuyi taba,sai bayan muntashi daga kwana muka yi gaggawar yin ta, cikin firgici da nuna bakinci akan kwananda ya kwashemu bamu yitaba
To zamuyi sallar tamkar mun sallah ceta A cikin lokacinta
Amma idan dagangan mukayi kwana, ko kuma bayan mun tashi daga baccin muka tuno bamuyi sallar ba kuma mukaki gaggawar yinta, sai daga baya to wannan zamu zamo masu Zunubi, kuma Sallar zata zamo munyi ta ne amma ba a cikin lokacinta ba.
.
2: wannan Hadith Yana nunar damu cewa: kowa ne dan adam kwana na iya rinjayar idonsa_ domin ga manzon tsira (s.a.w) shida sa habbansa (A.S) kwana Ya kwashesu.
.
3: wannan Hadith na nunar damu cewa: Allah yana sanarda manzon tsira (s.a.w) Ilmin Gaibi, in mukayi duba izuwaga Labarin da Shi s.a.w ya baiwa Abubakar (R.A) lokacinda Bilal baya wurinsu, kuma da manzon tsira s.a.w yakira Bilal (R.A) sai ga Bilal ya gayawa manzon Tsira (s.a.w) labarin irin wanda (S.A.W)ya fadawa Abubakar (R.A)
.
4: Hadith din Yana nuna muna cewa:shedan Har sahabban manzon tsira s.a.w Yana SHagartarwa awatarana to ballantana mu.
.
Saboda haka ya dace akullun muyi taka tsantsan wurin fadawa da ga tarkon shedan La’a lanne,Wallahu A A Lamu,
Allah ka amfanarda Al’ummar musulmi, baki daya.
Allah ka kiyaye mu fadawa cikin tarkon shedan jefaffe
Daga rahmarka
Amin.
.
Lectureraminukaura.wordpress.com

Advertisements