Wata rana wani mutum yazo wajen
manzon Allah
( s a w) yace ya Rasulillahi matata ta
haihu Kuma
gobene ranar da zan radawa jinjirin suna amma ba
ni da dabbar da zan yanka masa
Ka taimake ni ka bani dabba don na biya
bukatata”
Sai Annabi ( s a w ) yace” ka je gurin
Abubakar ka ce na ce ya baka dabbar da za kayi suna da
ita”
Sai mutumin nan ya tashi aka nuna masa
gidan
Sahabi Abubakar dama bai san Abubakar
ba, ya je ya tarar da wani mutum a kofar wani gida
ya na
ba wa dabbobinsa abinci sai ya wuce bai
yi masa
magana ba.
Da ya je can gaba sai ya sake yin tambaya a nuna
masa gidan Sahabi Abubakar, sai aka ce
masa ai
shine Wanda ka wuce a kofar gida ya na
bawa
dabbobi abinci Sai ya dawo ya yi wa Abubakar sallama
sannan
yace” Muhammadurrasulillah ya ce ka ba
ni dabba
daya gobe zan yanka ta domin in
sanyawa yaron da na haifa suna” sai Abubakar yace me
kace??? Sai yakara
cewa Muhammadur Rasulillahi ne yace
kabani dabba daya
sai
abubakar ya kara ce masa me kace??? Sai
mutumin nan ya fusata ya ce wallaha
idan har sai
na kara fada to sai dai kada ka bani
dabbar
Har ya juya Ya kama hanya sai Abubakar ya kira shi
ya ce wallahi nna jin dadi ne a duk
lokacinda aka
kira sunan annabi kuma wallahi da ka
kira shi sau
dari (100 ) da na baka dabba dari. Amma yanzu ka shiga cikin wannan
garken ka kama
rago guda 2 duk wanda ka ke so ka tafi.

Advertisements