GA MAGUNGUNA DAGA ASIBITIN MANZON ALLAH (S.A.W).
—————————————–
* 1-Idan BAQIN CIKI ne ya dameka, Ko
Quncin Rayuwa, Ko rashin Ciniki a
Kasuwa, Ko Rashin jin dadi awajen
aikinka, Ko kuma MIJIN AURE kike
nema, to ga Wata Mafita daga
Asibitin Manzon Allah (saww) :
– Yawaita Salati gareshi yana
kawowa samun biyan bukata da
yayewar bakin ciki, da samun farin
ciki, Farin jini, da kuma daukakuwar
al’amuranka awajen Allah da
bayinsa.
.
2- Yawaita Istighfari yana kawo
gafarar Zunubai, albarkar rayuwa,
Bullowar hanyoyin arziki, Toshewar
kofofin Musibu, Yayewar talauci,
Bunkasar arziki, etc.
.
3- Idan Kuma al’amura ne suka
chunkushe maka, Makiya sun
sawoka agaba, Mahassada sun sa
maka ido, Suna ta Qulla Maka sharri
da makirci, To kyalesu ka kama
Allah. Ka yawaita “HASBUNALLAHU
WA NI’IMAL WAKEEL” _Da ita ne
Annabi Ibraheem (as) ya kubuta
daga sharrin Maqiyansa. Kuma da
ita ne Annabi Muhammadu (saww)
da Sahabbansa suka samu kariya
daga sharrin Kafiran duniya alokacin
da suka hada kai domin rushe
Musulunci daga doron Qasa.
.
4- Ita kuwa Fadar “LA HAULA WALA
QUWWATA ILLA BILLAAHIL
ALIYYIL AZEEM”, Taska ce daga
taskokin gidan Aljannah. Don haka
mai yawan yinta ba zai, shiga Qunci
ba. Kuma Mahassada ba zasuyi
nasara akansa ba inshaAllah.
.
5-Idan Jinya (rashin lafiya) ce take damunka, ka
rasa yadda zakayi, To ka dauki
addu’ar Annabi Ayyoob (as) “ROBBI
INNEE MASSANIYADH DHURRU WA
ANTA AR-HAMUR ROAHIMEEN”
Zaka samu waraka da kuma
yayewar chutarka tare da ninninka
maka Arzikinka da lafiyarka (kamar
yadda akayi ma Annabi Ayyoob din
a. s.) InshaAllah.
.
6-Idan kuma biyan bukata kake
nema, ko yayewar wani hali, ko
neman shiriya daga halin da kake
ciki, to ka yawaita yin addu’ar
Annabi Yoonus (as) :
“LA ILAHA ILLA ANTA SUB’HANAKA
INNEE KUNTU MINAZ
ZWAALIMEEN”Allah zai amsa maka kuma Zai yaye
maka halin da kake ciki. in sha
Allahu.
.
7- Idan Kuma rashin samun Haihuwa
ne, ko kuma rashin Shiryuwar
‘Ya’yan da ka haifa, to ka yawaita yin
addu’ar Annabi Zakariyya (as) :
“ROBBI LA TADHARNEE FARDAN WA
ANTA KHAYRUL WARITHEEN”.
.
#Ya Allah ina rokonka da sunayenka
Tsarkaka, da Siffofinka madaukaka
Ka biya bukatu na, da na duk wanda ya
karanta rubutun nan. Da wanda yayi
#Share, Da wadanda sukayi
#comment,ko #Like, da wanda yayi #forwading, don Soyayyar da Muke
yiwa Annabinmu Muhammadu
(saww), da Iyalansa da sahabbansa tsalkaka.

Advertisements