WAJABCIN, YIN (SAKE) ALWALA GA WANDA YA SHAFI-ZAKARINSA_KODA WAJEN WANKAN JANABA NE IN DAI, BAYAN YA WANKE GABOBIN ALWALA.
———————————————
Hadith-58: Yahaya Yabani Labari, daga malik,daga Abdullahi Dan Abubakar Dan Muhammad Dan Amri Dan Hazami, cewa shi Yaji Urwata Dan zubairi Yana cewa:
Na shiga Gidan marwanu Dan Hakami sai muna Tunatarda juna abinda Alwala ke kasan cewa saboda shi, sai marwanu Yace: Kuma Alwala na kasan cewa saboda shafar zakari.
Sai Urwata Yace: Ni Bansan wannan ba. Sai marwanu dan hakami Yace:
Busratu ‘Yar Safwanu ta bani labari:
Cewa Ita taji manzon Allah (s.a.w) Yana cewa:
“Idan Dayanku ya shafi zakarinsa Yayi (Ya sake) Alwala.”
.
Hadith-59: Kuma Yabani Labari daga malik, daga Ismail dan muhammad Dan Sa’ad dan Abi waqas, daga Mus’ab dan sa’ad dan Abi waqas, cewa shi Yace:
Na kasance Ina rike da Alqur-ani wurin Sa’ad Dan Abi waqas sai na Ajiye shi, Sai Sa’adu Yace: Halan kashafi zakarin ka? Sai Yace Sai Nace Na’am. Sai Yace: Tashi Kayi Alwala, Sai Na tashi Nayi Alwala sannan Nadawo.
.
Hadith-60: kuma Yabani Labari daga malik, daga Nafi’u cewa Abdullahi Dan umar Yaka sance yana cewa: Idan dayanku ya shafi zakarinsa to hakika Alwala ta wajaba aga reshi.
.
Hadith-61: kuma Yabani Labari daga malik, Daga hisham dan urwata daga Babanai cewa shi yakasance Yana cewa: Wanda duk Ya shafi zakarinsa to Alwala ta wajaba ga reshi.
.
Hadith-62: Kuma Yabani Labari daga malik, daga Dan shihab, daga Salimi dan Abdullahi cewa shi yace: Naga Babana Abdullahi Dan umar Yanayin wanka (Na janaba) sannan Yayi Alwala sai nace dashi: Ya Babana shin wanka bai isarma kaba ga Alwala? Sai Yace A,a! Sai dai ni wani Lokaci ina shafar zakarina sai Inyi (in sake) Alwala.
.
Hadith-63: kuma Ya bani labari daga malik,daga Nafi’u daga salimi dan Abdullahi cewa shi Yace: na kasan ce tare da Abdullahi dan umar Acikin wata Tafiya, sai na ganshi Yayi Alwala Bayan hudowar Rana, sannan Yayi Sallah, Yace:
Sai Na ce dashi: hakika wannan sallar baka kasan ce kana sallatar ta ba ne? Yace: Ai Ni Bayan Nayi Alwalar sallar Subahin Na Shafi Farji-na, Sannan Na Mance Inyi (In sake) Alwala, shine sai nayi Alwala nadawo don yin (In sake) sallah ta.
(Muwadhdha malik- Babul wudhu’i min-massil-farji-15)
.
Malam Mai Izziya Acikin Littafinsa (FASALUN NAWA QIDHUL WUDHU’I) Yace:
Alwala tana walwalewa ne idan mutun ya shafi zakarinsa kuma shafar ta kasance Da Tafin hannunsa ko da gefen hannun, ko da tafin ‘yan Yatsunsa ko da Gefensu, ba tare da wani abu da ya raba tsakanin (Hannunsa da zakarinsa) ba da Gangan (ya shafeshi) ko da mantuwa, ya ji dadi ko baiji dadi ba, ya shafi kan kaciyar ne ko wani Gurin (kaciyar).
Amma alwala bata warwarewa idan aka shafi zakari ta kan wani abu da ya raba tsakani, koda kuwa wannan abin marar kauri ne. (kamar inya shafe shine saman Suturarsa, daya sa ajikinsa).
.
Allahu wa’alamu Allah Ya Amfanar da mu baki daya, don Allah ka/ki yi SHARE/ ko comment, Na wannan Tunatarwa domin ‘yan uwanku su gani suma su amfana, kai kuma kasamu “Lada”.

Advertisements