TUNA BAYA:
KO SHUGABAN KASA GOODLUCK JONATHAN BAI ISA YA GINA COCI A JAMI’AR BAYERO BA – Inji Sarkin Kano Ado Bayero
Zaman babbar kotun Shari’ah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta kai Masarautar Kano, saboda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr Ado Bayero yasa an rushe wata Coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami’ar Bayero Kano (BUK).
A zaman kotun da akayi a ranar Litinin 3 Feb, 2014, kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Prof Rasheed, da wakilin kungiyar Kiristoci ta kasa, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga Prof Rasheed da mataimakin shugaban CAN sun mike tare da Lauyoyinsu amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba.
.
Daga nan sai jagoran Alkalan kotun Justice Alakola Nweri yace da yake muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari’ar zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kafin wadannan mintoci.
Daga nan sai Justice ya dubi Prof Rasheed yace a baya Kotu ta baku umarnin Gina Coci a Jami’ar Bayero, ko kunbi umarnin kotu?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi umarnin Kotu, dan sai da ginin Cocin ya kai linta sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya jagoranci Rushe ginin gaba daya.
Justice yace, kuna nufin kenan kunyi watsi da umarnin kotu kunbi na Sarki?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda Sarki Ubanmu ne, kuma shine Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan Sarkin Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi masa biyayya ba.
Daga nan sai Justice ya umarci Prof Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa?
Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya ne hukumar Makarantar Jami’ar Bayero ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda haka muke rokon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya zauna.
.
Sannan kotu ta nemi Sarkin daya bayyana a gabanta, ana haka sai ga Sakataren Gwamnatin Tarayya Dr. Anyim Payios Anyim (wanda kirista ne) ya bayyana a gaban kotun, anga Alkalan kotun sun mike tsaye domin girmamawa ga Dr. Anyim.
Daga nan Dr. Anyim yace ya Mai Shari’ah ni ne wakilin Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayero, ya umarceni dana wakilceshi a wannan koto domin amsa kira.
Justice yace, kana nufin kana tsaye anan a matsayin Maimartaba Sarki kenan?
Dr. Anyim yace kwarai kuwa, kuma duk abinda zan fada ba ni na fada ba His Royal Highness ne ya fada.
Justice yace, muna jinka.
Dr. Anyim yace, Sarki yace na sanar da wannan Kotu shi yasa a rushe Cocin, badan komai ba sai dan basa bukatar ganin cocin a Jami’ar, Sannan yace na gayawa wannan kotu mai daraja cewar, idan za’a gina Coci sau 10 a Jami’ar to kuwa zai sa a rusheta sau 10.
Sannan Galadiman Kano Alh. Tijjani Hasheem yace na gayawa wannan Kotu ko Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai isa ya gina Coci ba a harabar Jami’ar Bayero, ba tare da yardar Mai Martaba Sarki ba, Dr. Anyim ya cigaba da cewa, wannan shi ne sakon da Mai Martaba Sarkin Kano da Mai Girma Galadiman Kano suka turo ni domin na sanarwa da wannan kotu na gode.
Daga nan, anga Alkalan Kotun suna tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga bisani akaga Babbansu ya daga waya yana magana, daga nan sai Alkalin yace to duk munji baya nan ku, dan haka, wannan kotu tana kira ga Shugaban kasa daya duba wannan Lamari idan yaga da yiwuwar gina Cocin to ya bada umarnin ginin, idan kuma yaga ba sai an gina ba to shikenan.
.
Daga karshe Kotu ta Sallami wannan Kara, kuma tare da yiwa Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya kara masa lafiya da adalci.
Sai dai bayan gama wannan Shari’ah, Mai Girma Galadiman Kano, ya bayar da sanarwar cewa Babbar Mai Shari’ah ta kasa Justice Maryam Aloma Mukhtar da Alkalan kotun da suka jagoranci Shar’ar da su gurfana a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero CFR. LLD. JP.
Allah Ya Jaddada Rahama Ga Sarki Ado Da Galadima Tijjani Hashim Da Dukkan Musulmai, Allah Ya Kai Masa Ladansa Na Yiwa Addinin Musulunci Hidima.

Advertisements