Watarana wata mata kyakkyawan gaske ta kudiri aniyar cewa
zatayi aure ammana da sharadin saita samu ustazi mutumin kirki
zata aura wanda yake azumi a kullum har shekara ta zagayo kuma
kullum sai ya sauke Qur’ani kuma yana kwana yana tsayuwan dare
yana bautawa Allah.
Matar ta hadu sosai kowani Mutum yanason aurenta ammana
suna tsoron wannan sharadin data gindaya shiyasa basu xuwa
neman aurenta har Allah Ta’ala Ya kawo wani mutum yazo ya
kudiri aniyar zai cika sharadin nata aka daura musu aure.
A rana ta farko na aurensu taga mutuminnan baiyi qiyamul laili ba,
bai sauke Qur’ani ba, bai kuma yi azumi ba. Tayi hakuri tajira taga
ko zai cika wannan buri nata xuwa wani lokacin taga shiru. Sai
Kawai takai karanshi kotu. Dukkansu sai suka gurfana a gaba
alkali, sai alkalin yacewa miji: ” kaji matarka tana karanka a kotu
akan batun auren ku domin baka cika sharadin auren naku. Shin
menene sharadin auren naku? ” Sai mijin: “sharadin sune: dole na
sauke Qur’ani kullum, nayi azumi kowace rana, sannan kuma na
kwana ina bautawa Allah.
Alkalin yace: “shin kacika wadannan sharudan Duka?”. Cikin
nitsuwa da kwanciyar hankali mutumin yace: “Eh ya mai shariah”.
Alkalin yace: “kayiwa kotu karya domin matarka ta shaidawa kotu
baki cika sharadunba shiyasa ta kawoka kara. Shin kana sauke
Qur’ani a kowace rana?”
Mutumin Ya amsa yace: “Eh ya mai shariah!”
Alkalin yace: “ta yaya haka bayan ka wuni kana sungurlanka?”
Mutumin yace : “Ya Mai shari’ah na karanta Suratul Ikhlas sau 3,
kuma Sayyidil waraa sallallahu alaihi wasallam yace duk wanda ya
karanta Suratul Ikhlas sau 3 kamar ya karance Qur’ani ne duka”
Alkalin yaya zugum ya zare idanu sannan yace: “naji wannan, shin
tayata kake azumin a kowace rana?”
Mutumin cikin ruwan sanyi yace: “ya mai shariah! Inayin azumin
Ramadan gaba daya sannan kuma nabishi da sitta shawwal, a
fadin Sayyidil waraa sallallahu alaihi wasallam duk wanda yayi
hakan kamar ya azumci shekerar ce gaba daya”.
Alkalin fa abun naso kureshi, sai yayi shiru na wani lokacin sai
yace: “naji dukkan wadannan bayane naka, ammana na karshen
nasan baka cikiba, domin matarka tana ganinka sharar bacci
kakeyi har asuba tayi, ammana kuma kacewa kotu kana kwana
ibada’, tayaya hakan zai kasance?”. Alkalin yana jiran mutumin
yakasa amsawa a garkameshi.
Cikin kwanciyar hankali kamar yayi pillow da gawa yace: “Ya Mai
shari’ah Inayin sallar isha’i tareda jama’ah sannan kuma haka
sallar asuba ma a jam’i nake yinta da jama’ah, kuma Sayyidil
waraa sallallahu alaihi wasallam yace : “duk wanda yayi sallar
isha’i cikin jam’i kana ya samu asuba cikin jama’ah kamar ya
kwana yana bautawa Allah Ta’ala ne”.
Alkalin ya gyara zama ya kalli mutuminnan. Sauran kuma a yanke
shari’ah kowa na jira. Sai alkalin Ya kalli mutuminnan da matarsa
yace: “kuje, ku tafi kawai aurenku nanan bawani matsala tattare
dashi”.
Yan’uwa masu hankali, sai mu dage muyi amfani da wadannan
hadisai guda 3 domin samun garabasar rayuwa. A wani Hadisin
Sayyidil waraa sallallahu alaihi wasallam Yana cewa: “duk wanda
yayi raka’atanul fajr kafin sallar asubah, wannan shine yafi kowa
arziki a duniya domin wadannan raka’ah biyu sunfi duniya da
abinda ke cikinta daraja”
Allah Ta’ala Ya bamu ikon aikata hakan