BAbin Abinda ya halatta ga mutun ga mata tai lokacin da take cikin Haila
——————————————————
Hadith- 93: Ya Haya Ya Bani Labari daga Malik, Daga Zaidi dan Aslama
Cewa wani mutun ya ambayi manzon Allah s.a.w sai Yace
Mi ya halatta gareni ga matata
Alhali tana haila?
Sai manzon Allah s.a
W yace:
Ta daura zanenta sosai
Sannan sha’aninka ya zamo A samanta ( daga cibiyarta zuwa samanta)
.
Hadith-94: kuma Ya bani Labari daga malik, daga Rabi’ata dan Abdulrahmani:
Cewa Aisha matar manzon Allah s.a.w takasan ce a kwance
Tare da manzon Allah s.a.w acikin Tufa guda kuma hakika sai ita ta zabura zabura mai tsanani sai manzon Allah s.a.w yace da ita “miya sameki shin ko kinji haila ne”
Sai tace E! Sai yace ki tsananda abin daurinki ga kanki (ki daura zanenki) sannan ki dawo zuwa wurin kwancinki.
.
Hadith-95: Kuma Yabani labari daga malik, daga nafi’u cewa Ubaidullahi dan Abdullahi dan umar
Ya aika zuwaga Aisha yana tambayarta shin Mutun zai Rungumi matarsa alhali tana haila?
Sai Tace:
Ta tsananta abin daurinta a kasanta, (ta daura zanenta daga cibiyarta zuwa kasa) sannan ya rungume ta in yaso
.
Hadith-96: kuma ya bani labari daga malik, cewa shi labari ya sameshi, cewa salim dan Abdullahi, da sulaiman dan Yasarin, an tamba yesu akan mai haila
Shin mujinta zai zo mata (zai tara da ita)
Idan taga tsalki kamin tayi wanka?
Sai suka ce:
A’a har sai in tayi wanka.
.
Allahu wa’alamu
Allah ka amfanarda musulmi baki daya.