Qur’ani na da harrufa 323,015
.
Qur’ani na da Juzi’i 30
.
Qur’ani na da Hizbi 60
.
Qur’ani na da rubu’i 240
.
Qur’ani na da ushuri 480
.
Surorin Makkah 85
.
Surorin Madinah 29
.
Surarin da suka fara da ‘Alhamdu’ guda 5
.
Surorin da suka fara da Tasbihi guda 6
.
Surorin da suka fara da harrufa guda 19
.
Guraren Sujjada a Qur’ani guda 15
.
Farkon wanda ya fara bayyana karatun Qur’ani cikin
Sahabbai a Makkah shi ne Abdullahi bn Mas’ud
.
Kalma mafi tsayi a cikin Qur’ani ita ce ‘Fa’asqainaakum
uhu’ ta na da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.
.
Qira’ar da tafi shahara wajen karatun Qur’ani ita ce
ruwayar Hafs daga Aasim. Hafs ya bar duniya a shekara ta
180 H, Asim kuma 127H
.
Tsuntsaye da aka ambaci sunayen su a Qur’ani;
*Alba’ubh
*As Salwa
*Al Guraab
*Al Jarad
*An Nahl
*Al Hudhuda
*Az Zubab
.
Sahabin da aka ambaci sunan sa a Qur’ani Zaidu bn
Thabit a cikin Suratu Ahzab
.
Rabe-raben Qur’ani ; akwai Surori masu suna;
*As Saba’ud Diwaal- sune Bakara, Aali Imran, Nisa’i,
Ma’ida, A’araf, An’am, Yunus. Su 7 ne, su suka fi tsayi.
*Akwai Almi’aini; daga bayan Yunus zuwa Surorin da suka
kai ayoyi 100 ko kusa da haka
*Almathani
*Almufassal su ne kananan surori daga ‘Qaaf’ ko ‘Hujrat’
.
Surah mafi girma ita ce Suratu Fatiha
.
Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu
.
Shugaban masu Tafsirin Qur’ani shi ne Imamud Dabariy
.
Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur’ani shi ne
Annabi Musa (s.a.w) sau 136
.
Sura ta karshen sauka cikin Qur’ani ita ce suratun Nasr
(Iza ja’a)
.
Aya ta karshen sauka a Qur’ani ita ce aya ta 281 a cikin
Bakara (Wattaquu yauman) a magana mafi inganci
.
Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi;
*Baqara-Saniya
*Namli-Tururuwa
*Ankabut-Gizo Gizo
*Nahli-Qudan Zuma
*Fiyl-Giwa
.
Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa;
*Suratu Yusuf
*Suratu Hud
*Suratu Ibrahim
*Suratu Muhammad
*Suratu Nuh
*Suratu Yunus
.
Surorin da aka ambace su da sunayen su taurari;
*Suratut Najm
*Suratul Qamar
*Suratud Dariq
*Suratush Shams
*Suratul Buruj
.
Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta;
*Suratul Fajr
*Suratul Laili
*Suratud Dhuha
*Suratul Asr
.
Dabbobin da aka ambace su cikin Qur’ani;
*Baqara Saniya
*Ba’ubha Kwarkwata
*Zubaab Quda
*Namli Tururuwa
*Hudhuda tsuntsu
*Naaqah Raquma
*Khail Doki
*Bighaal Alfadari
*Himar Jaki
*Qusuurah Zaki
*Jaraad Fari
*Zi’b Kerkeci
*Kalb Kare
*Guraab Hankaka
*Fiyl Giwa
*Ankabuut Gizo Gizo
*Nahl Zuma
*Su’ban
*Ibil Rakumi
.
Sunayen Mala’iku da ya zo cikin Qur’ani;
*Jibril
*Miika’iil
*Maalik
*Haruut
*Maarut
.
Daular da aka ambace ta cikin Qur’ani ita ce daular
Rumawa-Ruum
.
Qabilar da aka ambace ta a cikin Qur’ani ita ce qabilar
Quraishawa-Quraish
.
Littattafan Tafsiri da suka fi shahara;
*Tafsirud Dabari
*Tafsiru Ibn Katheer
*Tafsiru Ruhul Ma’ani-Aluusiy
*Tafsirul Qurdabi
*Tafsiru Mafaatihul Gaib
.
Gurare 4 sunan Mai Gidan mu ya zo a cikin Qur’ani;
*Aali Imran aya ta 144
*Ahzab aya ta 40
*Muhammad aya ta 2
*Fathi aya ta 29.
.
Daga littafin
ﻣﺎﺫﺍ ﺗﻌﺮﻑ ﻋﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻭﺍﻟﻨﺒﻲ
Please don’t forget to share, this is worth sharing. Qur’ani
abin Alfahari ne.