BAYANI: AKAN KIRAN SALLAH DA; TA DA IQAMAR SALLAH; DA FALALAR SU; DA ABINDA SHEDAN KEYI, ALOKACIIN DA AKE YINSU:
.
Hadith- 3:
Kuma ya bani labari daga malik, daga Sumayyi Baran Abubakar Dan Abdulrahman, daga Abi salihis-sammani,
Daga Abi huraira, cewa manzon Allah s.a.w yace:
Lalle da mutane sunsan abinda ke cikin kiran sallah, da sahun farko (Saboda falala) sannan (ace) bazasu samuba face sai sunyi kuri’a Agareshi da zasuyi kuri’a,
Kuma da mutane sunsan abinda ke cikin sakko (zuwa masallaci na falala) da sunyi rige-rige zuwa ga reshi,
Kuma da mutane sunsan abinda ke cikin sallar Isha’i da Sallar subahin ( na falala) da sunzo masu koda da Rarrafe.
.
Hadith-2:
Kuma Ya bani labari daga malik, daga Abi shihaabin, daga Ada’u dan yazid Allaisiyi, daga Abi sa’idul Khudri,
Cewa manzon Allah s.a.w Yace:
” idan kukaji kiran Sallah to kufadi misalin abinda maikira ke fadi.
.
Hadith-4:
kuma ya bani labari daga malik, daga A ala’i dan Abdulrahman dan Yakuba, daga Babanai, da ishaq dan Abdullahi, cewa su sun bashi labari
Cewa su sunji Aba huraira yana cewa:
Manzon Allah s.a.w Yace:
” idan aka tada Iqamar sallah to kada kuzo mai kuna masu sauri ( gudu aguje wajen sallar) A,a kuzo mai kuna masu na tsuwa, abinda kuka riska ku sallah ce shi,abinda ya kucce maku ( na daga sallar) sai ku cika,
Domin sani cewa dayanku yana acikin sallah ne muddin ya kasance yayi nufin zuwa wurin sallah.
.
Hadith-6:
Kuma ya bani labari daga malik, daga Abizzinadi, daga A Araji, daga Abi huraira, cewa
Manzon Allah s.a.w yace:
” idan akayi kiran sallah shedan zai juya a gareshi yana mai Qara (yana mai keta Ihu), har sai ya kasance bayajin kiran, idan aka qare kira sai ya juyo ( yadawo),
Har Sai dai idan aka tada iqamar sallah sai ya juya, idan kuma An Qare iqamar sallah sai ya dawo,
Har sai ya sanya wasiwasi tsakanin mutun da rainai ( lokacinda mutun ke sallah)
Sai Yace:
tuna kaza! tuna kaza!
Mi yasa bai tuna kazaba,
Har sai Ya 6atar da mutun yazan baisan Sallah nawa yayi ba.
.
Hadith-7:
Kuma ya bani labari daga malik,
Daga Abi Haazimi dan Dinarin, daga Sahalu dan Sa’adu-ssa’idi, cewa shi yace:
Sa’o’i, Guda Biyu Ana bude kofofin Sama Gare su- Acikinsu,
Kuma mai yin Addu’a kadanne kwarai wanda za’a mai doma Addu’arsa ( wai yayi Addu’a acikin wadannan lokuttan ba’a kar6a mai ba)
Lokacin halarcin (Yin) kiran Sallah domin yin sallah,
Da lokacin da ake sahu domin Yin jahadi ( yaki don daukaka kalmar Allah).
.
Hadith-8:
Kuma ya bani labari daga malik,cewa shi labari ya sameshi: cewa mai kiran sallah yazo wajen umar dan khaddabi (R.A) ya na yi masa kiran sallar Assuba, sai ya sameshi yana kwana
Sai Yace:
Assalatu-Hairun-minannaumi.
Sai Umar ( R.A) Ya umar ceshi ya sanya ta a cikin kiran sallar subahin. ( A nan Ne aka samu cewa Assalatu hairun minannaumi, A kiran sallar asuba).
.
Allahu wa’a lamu. muna rokon Allah ya amfanar da musulmi,
Allah ya karemu da sharrin shedan je faffe daga rahmar Allah.
Don Allah Wanda yasamu dama yayi #SHARE Na wannan post don sauran musulmi su gani suma su amfana.
Allah kayi salati da salami ga manzon tsira (s.a.w)
Da iyalan-Gidansa, da sahabbansa, baki daya.