BAYANI AKAN MASU KUDIN DA BASU FITAR DA “ZAKKA” DA AZABAR DA ALLAH (S. W. T) YA TANA DAR MASU A RANAR GOBE KIYAMA.
.
Allah (s.w.t) Yace: “kaga wadanda suke 6oye zinari da azurfa basa ciyarda ita don daukaka kalmar Allah to kamasu bushara da azaba mai radadi, A ranarda zaa kone su da wutar jahannama akone goshinsu da fatar jikinsu da ta bayansu ( mala’iku su ce dasu) “wannan fa abin da kuka boye ne na dukiyarku.
To ku dandani azaba da abinnan da kuka taskace.” (surar Tauba)
.
ALLAH (S. W.T) Yace: “Azaba ta tabbata Ga mushrukai wadanda basu bada ZAKKA” ( surar fussilat)
.
Allah (s.w.t) yace:
“Kada wadanda suke yin Rowa da abinda Allah Ya basu na daga cikin falalatai su zaci Yin hakan shine Alkhairi A Ga resu.
A’a hakan sharri ne A garesu.
Da Sannu za’a rataya masu abinnan da suke yin Rowa dashi Aranar Alkiyama-(Ayi masu azaba dashi)” (Surar Ali Imran)
.
Allah s.w.t Yace: ” kuma kuciyar da abinda muka azzirta ku dashi tun kafin mutuwa tazo ma Dayanku sai yazo yana cewa Ya ubangiji ina ma Adan jinkirtamin zuwa wani lokaci kadan Don nayi sadaqa kuma na kasance daga cikin salihhai to kusani Allah bazai jinkirtawa wata rai ba idan ajalinta yazo
Shi Allah Mai bada labari ne Ga abinda kuke aikatawa.” (surar munafikkun)
.
Hadith daga Abu huraira (R. A) manzon Allah s.a.w yace: ” duk Wanda Allah yaba dukiya Yaki fitarda zakkarta za’a mayar da wannan dukiyar Aranar kiyama shirgegen Kumurcin-maciji yanada wasu Digagga guda Biyu akan idonsa, Za’a Rataya Mai shi awuyansa Ranar Alkiyama, sannan Ya rika cha6o Mukamukansa (yarika saran kafadunsa ) Sannan ya ce dashi Nine dukiyarka nine Taskarka!
Sai manzon Allah s.a.w yakaranta:
“Kada wadanda suke yin rowa da abinda Allah Ya basu na daga falalarsa su zaci hakan Alkhairi ne aga resu. A’a hakan sharri ne A Ga resu da sannu Ranar Alkiyama za’a rata ya masu Abinnan da suke Rowa dashi.
(Bukhari, Muslim, Tirmizi, da Nisa’i suka fitar da wannan Hadith).
.
Yaku masu kudi muna kira gareku da kuji tsoron Allah kurika bada zakka, kurika taimakon Mabukata Da Gajiyayyu, kamar yanda Allah da manzon sa suka umar ta, Ayi domin gujewa Afkuwa acikin wadannan Azabobin da Allah Ya tanada Ga duk Wanda yazo a ranar kiyama An bashi dukiya yayi kememe wurin fitarda zakka. Da Taimakon mabu Kata.
Dafatan IN kunne yaji to gangar jiki
Ta tsira,
Masu kudi dubara dai ta rage ga Mai shiga rijiya.

Advertisements