BAYANI A KAN SAKE SALLAH , TARE DA “LIMAN” GA WANDA YAYI TA SHI KADAI, IN BANDA SALLAR MAGARIBA DA SALLAR SUBAHIN:
——————————————–
حدثني يحيى، عن مالك،عن زيدبن أسلم، عن رجل من بني الدل يقال له بسر بن محجن، عن أبيه محجن، أنه كان قي مجلس مع رسول الله (S.A.W) ، فأذن بالصلاة، فقام رسول الله (S.A.W) فصلى، شم رجع ومحجن قي مجلسه لم يصل معه، فقال له رسول الله (S.A.W) : “مامنعك أن تصلي مع الناس؟ ألست برجل مسلم؟” فقال بلى يا رسول الله ، ولكني قد صليت قي أه‍لي، فقال له رسول الله (S.A.W) : “إذا جءت فصل مع الناس، وإن كنت قد صليت”
.
FASSARA:
——————————-
Yahaya Ya Bani Labari, Daga Malik, Daga Zaidu Dan As lama, Daga wani mutun daga Kabilar Bani-dili, Ana ce dashi Busru Dan Mihjani, Daga babanai Mihjani,
Cewa shi Ya kasance a wani majalisi Tare da manzon Allah (S.A.W) Sai Aka yi kiran Sallah, sai manzon Allah (saw) Ya tashi Yayi Sallah, sannan Yadawo Alhali Mihjani Na wurin zama nai bai tashi Yayi Sallah Tare da shiba,
Sai manzon Allah (saw) Yace Dashi:
“miya hanaka Yin Sallah Tare da mutane? Shin kai Baka kasance mutun musulmi ba?
Sai Mihjani Yace:
A,a Ya Manzon Allah,
Sai dai Ni Hakika Nariga Nayi Sallah A Gidana,
Sai Manzon Allah (saw) Yace Dashi:
” Idan Kazo Kayi Sallah Tare Da Mutane, Koda ko Hakika ka kasance Kayi Sallah”
(Indai Kai kadai kayi Sallah To Ka sake Wata Tare Da Liman inka Is ko a nayinta, ko za’a fara ta’a cikin Jam’i)
.
و حد ثني عن مالك، عن نافع، أن عبد الله بن عمر كان يقول: من صلى المغرب أو الصبح، ثم أدركه‍ما مع الإمام فلا يعد له‍ما
FASSARA:
Kuma Ya Bani Labari Daga Malik, Daga Nafi’u, cewa Abdullahi Dan Umar Ya Kasan ce Yana cewa: Wanda Ya sallaci Sallar Magari ba ko subahin, sannan saiya riske su (Yaga Anayinsu) Tare da Liman To Kada Ya Ramasu.
.
Amma Imam Malik (Rahimahullah ) Yace:
Banga Wani Laifiba Akan Yayi Sallah (Ya maida Sallah) Tare da Liman wanda yayi Sallah Agidanai (Batare da Yayi ta cikin Jam’i ba) Sai Fa Sallar Magariba Domin Idan Ya Maida Ita Sallar ta Magariba zata zama Shafa’i.
.
KARIN BAYANI:
————————————-
Wadannan Hadissai suna karantar damu cewa:
Idan mutun Yayi Sallah shi kadai, Bayan ya kare Sai Yaga wasu jama’a sun shigo masallaci zasuyi Jam’i, ko Yayi Sallah shi kadai a wani wuri sai ya samu a na Jam’i a wani masallaci to zai bi wannan Jam’i,, Kamar yanda manzon Allah (saw) Ya Umarci Mihjani (R.A) Daya sake Sallah Acikin Jam’i Bayan yayita a Gidansa.
.
in banda Sallar Magariba da Isha’i Wadanda Abdullahi Dan Umar(R.A) Yace mutun bazai Rama suba, Bayan Ya sallace Su shi kadai,
Ko kuma Sallar Magariba da Imam Malik (Rahimahullah) Yace Sallar magari ba Ita kadai ce Sallar da mutun bazai Rama Ta-Tare da Liman ba Bayan ya Sallace ta shika dai.
.
Muna Rokon Ubangiji Allah ya bamu ikon aiki da wannan Tuna Tarwa da aka yi
Allahumma Amin.

Advertisements