GA TAKAITATTUN LABARAN DUNIYA.

*Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi Rundunar sojin Najeriya da kokarin rufe shaidun kisan gilla ga mabiya mazhabar Shi’a a Najeriya.

*Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar dokokin kasar wasu gyare-gyare da ya hango a kundin kasafin kudin kasar.

*Tafkin Chadi na fuskantar Barazanar kafewa saboda sauyin yanayi da kuma ayyukan bil’adama.

*Shugaban Amurkar, Barack Obama ya bayyana goyon bayansa kan cigaba da kasancewar Birtaniya a tarayyar turai.

*Dimbin jama’a ne suka yi dafifi domin taya Sarauniya Elizabeth murnar cika shekaru casa’in a duniya.

*Kamfanin jiragen sama mafi girma a Naijeriya, Arik Air, ya yi barazanar kai hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta FAAN kara a gaban babbar kotun kasar.

*A jamhuriyar Nijar matakin kawancen adawa na aika wakilanta a majalisar dokoki da kuma hukumar zabe ta kasa, CENI na ci gaba da mamaye mahawarar siyasar kasar.

*A birnin Accra a kasar Ghana, shugaba John Mahama ya sake korar wasu karin alkalan manyan kotunan kasar guda biyu da ake zargi da hannun a badakalar cin hanci da rashawa sakamakon binciken sirrin da dan jaridan nan wato Anas Armiyau Anas ya gudanar kan wasu alkalan kotunan kasar.

*Yunwa da tsoron harin kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko haram ya ritsa da su a Yankin tafkin Chadi.

*Gwamnatin Tarayya ta mu santa raderadin da ya ke ta yaduwa a shafukan jaridu cewa wai ta Kori ministan mai, Ibe Kachikwu da ga aikinsa.

* Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Nemi Kotu Da Ta Yanke Wa Wadansu ‘Yan Shi’a Su Hamsin Hukuncin Kisa Saboda Kashe Wani Soja Da Suka Yi A Zaria

14 / Rajab 1437
22 / Afrilu 2016

Advertisements