*Tarihin Zamfara Yau shekaru Ashshirin (20) kenan da kirkiro Jihar Zamfara*

Abdullahi Gaula ne shugaban karamar hukumar mulkin Gusau a lokacin da aka kirkiro jihar Zamfara.

Kamishinoni biyu aka baro sokoto dasu lokacin da aka kirkiri Zamfara: Iyal Mohd Talata Mafara, kwamishinan Info and special duties. Da kuma Abubakar Anka II shine na Works, ba da jimawa ba ya rasu.

* DGs din da aka zo Zamfara da su, su 5 ne: Marigayi Alh. Sanda Ibrahim Zurmi, Alh. Sani Ahmad Nahuce, Alh. Ibrahim Bagobiri, Khalifa Attahiru Bello, Yusuf Garba (mni).
.
* Eng. Dauran Da Maigirma Yarima da Su Dansanda Maru da Sa’idu Usman Bukkuyum duk a Zamfara a ka Nada su DGs kafin su koma Perm. Secs
.
* Yarima na Director Budget/Incorporated a Ministry Of Finance Sokoto State akayi zamfara
.
* Kamar Ibrahim Suleiman yana PPS a Govt house Sokoto akayi Zamfara
.
* Alh. Bello Umar Karakkai mni Director NE a Cabinet affairs Sokoto akayi Zamfara

* Abu na farko bayan kirkiro Zamfara shi ne, Karbar Gusau LG Secretariat daga Chairman Alh. Abdulkadir Abdullahi Gaula Ubandoman Gusau, aka mayar da ita gidan gwamnati.
.
* Sai Maida makarantar Mata ta FCET Zuwa Sakariya, Wadda itace zacas a yanzu.
.
* Ita kuma ofishin Alh. Aminu Ahmad Nahuce mni Wakilin Sakkwato, Sakataren Gwamnatin Jaha na farko, ta shiga Hulda Da Masu Suturar Gari wajen shiryawa Ma’aikata wajen aiki da wurin kwana a gidajen da aka samu taimako daga Wajen su.

Kanan hukumomi 14 aka zo da su daga Sokoto. Sai dai ranar da aka fadi sunayen Jihohin, an aiko da sunayen Kananan Hukomomi 14 ta hanyar fax wanda muka karba ni da Alh. Abu Maru, lokacin yana Principal Secretary, Govt House, Sokoto. Sunayen su ne kamar haka:
1. Anka
2. Bakura
3. Bukkuyum
4. Birnin Magaji/Kiyawa
5. Bungudu
6. Gummi
7. Gusau
8. Kaura Namoda
9. Maradun
10. Maru/Dansadau
11. Talata Mafara
12. Tsafe
13. Shinkafi
14. Zurmi
.
‘Yan mintota kadan sai Gwamnan Sokoto na wannan lokacin, Navy Capt Abdulrashid Adisa Raji, ya umarci kar a yi releasing din shi for public consumption.
.
Bayan kwana biyu sai aka ambata sunayen Kananan Hukumomin kamar haka:
1. Anka
2. Bakura
3. Bukkuyum
4. Birnin Magaji
5. Bungudu
6. Gummi
7. Gusau
8. Kaura Namoda
9. Maradun
10. Maru
11. Talata Mafara
12. Tsafe
13. Shinkafi
14. Zurmi
.
Nan take sai ga wasu da abun ya shafa sun nuna rashin amincewar su da shiga cikin Jahar Zamfara. Misali mutanen Bafarawa suka nuna ba su dace da zama cikin Shinkafi L/G ba, su kuma wasu daga cikin manyan Gummi suka kyamaci shiga cikin Jahar Zamfara.
.
Wannan takaddama ta sa aka yi ta tuntubar juna har zuwa ranar da Gwamnatin Tarayya ta kafa wani Kwamiti domin duba irin wadannan matsaloli.
.
Idan ban manta ba, ranar 9/10/96, Kantoman Jihar Zamfara Lt Col. JB Yakubu ya shigo. Kwana biyu bayan shigowar shi, ya tura ni wajen Brig. Gen. Yakubu Mu’azu domin kai masa wata tazwira mai nuna Kananan Hukumomin da Kwamitin Kirkiro Jihar Zamfara ya nema tun 1982.
.
Daga karshe sai Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cire Bafarawa daga Shinkafi zuwa Isa LGA. Haka kuma aka kirkiro Kebbe LGA daga Gummi aka sa ta cikin Jihar Sokoto.
.

* Kafin ayi Zamfara Uwayen Kasa muke dasu kamar Su Sha biyar a Karkashin Masarautar Sakkwato. A halin yanzu Kuma Muna da Sarakunan Yanka 17.
.
*Ga sunan garuruwan da uwayen kasar suke:
Anka, Gummi, Bukkuyum, T/Mafara,Bakura,Maradun, Maru, Bungudu, Gusau, Dansadau, K/Koshi, TSafe, K/Namoda, Zurmi, Moriki. Idan ka hada da Shinkafi Da Birnin Magaji zaka samu Masarautu 17 Dake Jahar Zamfara a halin yanzu.
.
* Wannan sune Masarautun da kantoman Mulkin soja Na farko conal jb yakubu yafa daga darajarsu:
Anka Emirate 1st Class
Gusau Emirate 2nd Class
Gummi Emirate 2nd Class
Talata Mafara Emirate 2nd Class
Kauran Namoda Emirate 2nd Class
Chief of Zurmi
Chief of Bungudu
Chief of Dansadau
Chief of Tsafe

***
.
Alfanun yin jihar Zamfara
* Kafin samun Y’ancin kan Najeriya sai a Gundumar Uban Kasa ake yin Makarantar Firamare da asibitin disfansare. A halin yanzu muna da Makarantun Firamare 1575 (Na samo wannan bayani ne daga wani bayani mai magana kan shirin ciyar da Daliban Firamare wato Home Grown School Feeding of the Federal Government). Makarantun Sakandare 191 (Wannan na kunshe ne a cikin jawabin Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar na 29 ga watan mayu 2015 da yake magana akan ciyar da daliban Sakandaren Jahar Zamfara)
.

.
Cigaba da Al’ummar zamfara Suka samu tun lokacin da a ka kirkiro Zamfara shekaru 20 da suka wuce wajen Gwamnati. Ma’ana Yan Kasuwa da Manoma da Makiyaya da Almajirai dake zaman Kansu sun samu cigaba a fannonin da suke Famarsu? Idan akwai, a bada Misali domin mu Ilmantu.
.
* Tun dai ana tsohuwar Jahar Sakkwato yankin Zamfara ke yi zarra a bangaren Hardar Al’Qurani Mai Girma. Mafi yawan mahaddatan Najeriya sun yadda da cewa mafiyawancin Mahaddatan Najeriya masu kananan Shekaru suna fitowa ne daga Jahar Zamfara
.
* To Alhamdulillah a fannin manoma babu shakka jahar zamfara tasamu cigaba samuwar jahar zamfara la,akari da shirinan na tallafama manoma da takin zamani irin shuka da maganin kwari wanda mai girma sanator yarima yayyi a lokacin mulkinsa karkashin shirin nan na hukumar zacarep wanda dukkan Gwamnatotan dasuka biyo baya basu yarda wannan mataki ba misamman wannan Gwamnati karkashin Abdul’aziz yari mafara wanda tayi iyakar kokarinta bangaren tallafama harkat noma wanda wannan nema yabbaita damar rarrabar da takin zamani akan naira dubu domin amfanuwar manoma.
.
* Ta fuskar kasuwanci , daga lokacinda anka kirkiro jahar zamfara yazuwa yau ansamu sauye sauye dadama acikin shaanin kasuwanci. Duba ayau irin tarin kamfanonan gurzar auduga da muke dasu. Duba irin tarin plaza plaza da muke dasu da ake gudanarda harkokin kasuwanci daban daban. Duba irin tarin cibiyoyin kiyon kaji da muke dasu a fadin jahar nan. Duba irin tarin filling stations da muke dasu ayau. Duba irin tarin cibiyoyin sayarda motoci da muke dasu ayau. Yawan bankuna ajahar zamfara sunkaru. Duk wadannan cigaban dana lissafa asama mun sameshine bayan an kirkiro jahar zamfara.
.
* Jihar Zamfara bango ce tun a tsohuwar jihar Sokoto a fannonin ilimi da Noma da Kasuwanci har ma da kwarewa wajen kitsa dubarun siyasa a jamhuriya ta daya da ta biyu har ma da ta Uku.
.
* Bayan kirkiro jahar zamfara munsamu :-
Sabuwar kasuwa ta zamani. Munsamu gidan talabijin mai zaman kansa na Gamji Tv inda matasa sunka samu ayukka karkashinsa. Munsamu karin asibitota na gwamnati dana yan kasuwa kuma ayukkan yi sunkara yawaita. Bullowar wayoyin zamani yakara bunkasa ayukkan yi da shaanin kasuwancin jahar zamfara. Shaanin sufuri ya bunkasa inda munka samu hukuma maikula da wapnnan fani kuma tashoshin shiga mota sunkara yawaita. Duk wannan bayan ankirkiro jahar zamfara…
.
* …..don haka, kirkiro mana jiha ya share mana fage ne wajen bunkasar tattalin arzikinmu da fadadar fannonin ilimi da kwarewar siyasa.
.
* Makiyaya. Nan kam ansamu akasi domin jahar zamfara taci baya tun bayan da anka kirkirota ta fuskar *kiyo* sakamakon wasu gungun batagari da anka samu sunka kassara makiyayanmu dakuma dabbobin kiyonsu duk da namijin kokarin d gwamnatti tayyi na kawarda wannan matsalar amma dapi ko bakomai inda anka fito , jahar zamfara ta shahara ta fuskar noma da kiyo.
.
* ….zan iya bugun gabar cewa al’ummar Zamfarawa ne suka baiwa yankin arewa ta yamma kwarin guiwa a jamhuriya ta hudu a dalilin taron aradu da ka da matashin dan siyasa a lokacin Alh Ahmad Sani Yariman Bakura yayi na jaddada shimfidar tabarmar Shehu Mujaddadi wacce duka yankunan suka kwaikwaya har kasa ta dauka baki daya kuma duniya ta sanyawa Zamfara albarka.
.
* Almajirai. Alal hakika tun bayan kirkiro jahar zamfara , ankara samun yaiwatar almajirai dake kwararowa daga makobtan jahohin *Kebbi* da *Sokoto* dama jamhuriyar *Nijar* domin neman ilimin addini da kasuwanci. Hakama makarantun islamiyya sun yawaita matuka ainu tun bayan kirkiro jahar zamfara wanda zaman lissafin irin wadannan makarantun islamiyya , wani aikine mai zaman kansa saidai muyi ishara kawai.
.
* Haka kuma mun zo da Ma’aikata 7,000, amma yanzu mun kai fiye da 20,000.
.
* JADDADA SHARI’AR MUSULUNCI. yana daga jigon abin da ya fitar da jihar Zamfara tayi fice ba kawai a tsakanin sa’oin

Advertisements