*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRA JI’UN.*
.
“`Jikina Yayi Sanyi, na kadu matuka da irin yanda Nakejin ‘Yan Bindiga dadi na shiga suna karkashe bayin Allah, suna Raunata wasu, suna Kona kayayyakin Su, suna kuma Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, a Wasu Sassan Jihata ta zamfara, Banji dadiba kuma banyi farin cikiba Da wannan bala’i dake faruwa a jihar zamfara , dukkuwa da zaman jihar Zamfara jihar Shari’ar Muslunci.
.
Kwanakkinnan Kawai Munta cin karo da labarai marasa dadi na Bala’oin dake faruwa a jihar Zamfara Wasu Kaji ance anyi Garkuwa da wancan, wasu kaji ance An kai hari Na Rashin imani an kashe mutane nan mutun 10 nan 20 can 30, in 40 can 100 can 120, kai Dadai sauran dinbin rayukan Al’ummar dake silwanta a jihar Zamfara Wadanda ko Alama bama za’a iya kididdige Adadin suba.
.
Tabbas Matsayin mu na musulmi mun Sani sarai cewa dukkan Wadannan Al’amurra mukaddarine daga Allah, domin adan iya Ilmin da Allah ya huwa ce muna Munsan Allah (SWT)
Shiya fada acikin Al-quraninsa cewa:“`
.
بسم الله الر حمن الر حيم.
.
( وَلَنَبْلُوَنَّكُم بِشَيْءٍ مِّنَ الْخَوْفِ وَالْجُوعِ وَنَقْصٍ مِّنَ الْأَمْوَالِ وَالْأَنفُسِ وَالثَّمَرَاتِ ۗ وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ )

البقرة (155) Al-Baqara
.
Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙkasa daga dũkiya da rãyuka da ‘ya’yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙkuri.
.
( الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ )

البقرة (156) Al-Baqara
.
Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: “Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa.”
.
( أُولَٰئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ )

البقرة (157) Al-Baqara
.
Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.
.
“`Ya Allah Munyi imani da samu da rashi duka a hannunka shike, kuma Allah Munsan ire iren wadannan Masifu suna faruwa ne mafi akasarinsu sakamakon Sa6unan mu, wadanda Zukatan mu ke Aikatawa Aga reka, Ya ubangiji muna Rokonka ka Yafe muna Kura kuranmu ka kawo muna karshen wadannan masifu dake faruwa a jihar Zamfara.
.
Haka zalika Muna kira ga Gwamnati musamman Gwamnatin Ta Rayyar Nigeria da tawa Allah tawa ma aikin Allah ta dauki matakin Gaggawa Ga wannan kashe-kashen dake faruwa a Jihar Zamfara, Don Allah Gwamnati ta Tashi tsaye haikan ta dauki matakin ba Sani ba Sabo ga wannan Al’amari
Domin Sune Allah (SWT) zai Tambayà a Ranar Alkiyama Na miyasasu zura ido ana kashe Alumma, Anayin Garkuwa da wasunsu, ana Karrasa wasu, basu dauki wani kwakkwaran mataki ba matsayinsu wadanda Allah ya dorama Alhakin wannan aiki, Na tsaron Rayuka da dukiyoyin Al’umma.
.
Abun Bakin cikine da ta kaici ace Jihar Zamfara jihar da Ministan tsaro , Da Shugaban Kwamitin Tsaro da Asiri Na majalisar Wakilai , Suka fito, ace wadannan bala’o’i Na faruwa,
kusani zaku hadu da Allah kuma Allah sai Ya Tambayeku akan Dukkan Amanar daya Baku akan shin Kunyi abunda ya dace da Mukamin daya baku? Ko kuwa akasin haka?
.
Ya Allah mun tuba Allah kaya fe muna ka kawo muna karshen wannan bala’i dake faruwa a jihar Zamfara, Allah kabaiwa Mahukuntan mu ikon daukar matakin dazai kawo karshen wannan Mummunar Bala’in dake faruwa a Jihar Zamfara da Kasa baki daya
Amin thumma Amin“`

Advertisements