I

NA BAIWA SHUGABAN KASA #MUHAMMAD_BUHARI SHAWARA. DA A AJE KOMI A MAIDA HANKALI WURIN SAMUN ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALIN AL’UMMAR JIHAR ZAMFARA.


DOMIN CEWA DAI AKAI ANA DAUKAR MATAKIN SAMARDA TSARO WANNAN JAHA AMMA HAR YANZU GAFARA SAH DAI MUKEJI BAMUGA KAHO BA.

YANZU A ZAMFARA ANKAI FAGEN ‘YAN TA ADDA KE SHIGA GARURUWA SU KASHE MUTANEN GARURUWAN SU KORA WASU,JEJE, SU KUMA SU KAMA GARURUWAN NASU.

AHALIN YANZU ALLAH DAI YASAN DUBBAN MUTANENDA AKAKASHE WASU KUMA, AKA JIKKATASU, WASU SUKA BAR GARURUWAN SU SUKAJE GUDUN HIJIRA, A JIHAR ZAMFARA.

MAGANAR GASKIYA BABU WATA GWAMNATIN TA RAYYA DA DAN TA ADDA ZAI GAGARETA, SAIKO IN GWAMNATIN BADA GASKE TAKE WURIN YAKI DA WADANNAN ‘YAN TA ADDA BA, DOMIN MUN GANI KO A BOKO HARAM YANDA SHUGABA BUHARI YAYI TSAYE TSAYIN DAGA SAIDA AKA MURKUSHE KUNGIYAR BOKO HARAM.

YANZU AN MURKUSHE BOKO HARAM KUMA GA WASU ‘YAN TA ADDA SUN TSIRU WADANDA KO BBC HAUSA TA FADACEWA MUTANENDA SUKA SILWANTA SANADIYYAR WADANNAN ‘YAN TA ADDA SUNFI MUTANENDA BOKO HARAM TA HALAKA

INA BAKIN CIKIN ABUNDA KE FARUWA A JIHAR ZAMFARA KUMA INA BAKIN CIKI AKAN YANDA SHUGABA BUHARI YAYI KO IN KULA DA ABUNDA KE FARUWA A JIHAR ZAMFARA, INDA A DUK LOKACIN DA MAIGIRMA PMB. YA TASHI MAGANA AKAN WANNAN AL’AMARI SAIYA KIRASHI DA “FADAN MANOMA DA MAKIYAYA”

KUMA ALHALI WANNAN AL’AMARI YA WUCE A KIRASHI FADAN MANOMA DA MAKIYAYA ADAI YI BINCIKE.

YA MAIGIRMA SHUGABAN KASA KUSAN KULLUN INA TUNA YANDA NA GANI DA IDONA IRIN SO YAYYA DA KAUNA DA MUTANEN KARKARA SUKA NUNAMA A ZABEN 2015, DOMIN WADANNAN GARURUWA LOKACIN CAMPAIGN HAR KARFE 3:00-4:00, MUNA SHIGARSU KUMA MUTARARDA MUTANEN WADANNAN GARURUWA MAFI AKASARINSU A TSAKKIYAR DARE RIKE DA TSINTSIYOYI SUNA FADAR SAI BUHARI! SAI BUHARI!!

YA MAIGIRMA SHUGABAN KASA, KASANI BABU WATA GWAMNATI DA ZAACEWA TAYI NASARA KO TA KAWO CIGABA

MATSAWAR TA KASA KARE RAYUKA DA DUKIYOYIN AL’UMMAR TA.

AYI GAGGAWAR DAUKAR MATAKI GA ABUNDA KE FARUWA A JIHAR ZAMFARA, TUN GABANIN WADANNAN ‘YAN TA ADDA BASU KARASARDA AL’UMMAR JIHAR ZAMFARA BA

ALLAH YASA AYI AIKI DA WANNAN KIRA NAWA, NAFI FARIN CIKIN ZAMAN LAFIYAR AL’UMMA DA HARKAR SIYASA, DOMIN DA ALKHAIRI DA SHARRI DUK WANDA NAYI SAINA GANSA A GOBE KIYAMA.