SHUGABAN JAM’IYYAR PDP NA JIHAR BAYELSA. TAREDA ‘YA’YAN JAM’IYYAR PDP KIMANIN DUBU DAYA (1000) SUN CANZA SHEKA ZUWA JAM’IYYAR APC, MAI MULKI. . A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bayelsa, Kanal Sam Inokoba ya jagoranci ‘ya’yan jam’iyyar PDP kimanin dubu daya, a dandalin wasanni na Samson Siasia da ke babban birnin jihar Yenagoa, suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a kasa APC. Wannan al’amari ba karamin abu ne a wurin jam’iyyar APC, musamman ganin yadda wadansu jiga-jigan mutane suka biyo wannan ayari. Daga cikin ‘yan Bayalsan da suka shigo APC, akwai Sanata Heineken Lokpobri da Mr. Timi Alaibe da sauransu. Wannan sai ya zama wani abin mamaki ga masu sharhin al’amurran yau da kullum musamman ta yadda suke ganin wannan jihar Bayelsa nan ne mahaifar tsohon shugaban kasa na gwamnatin da ta gabata, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan. A hannu guda kuwa, Kanal Inokoba ya zayyana dalilan da suka sanya suka bar jam’iyyar PDP, wanda ya ce, akwai rashin gudanar da ingantaccen jagoranci da gazawar jam’iyyar ta PDP wajen cika alkawurran da ta dauka wa al’umma da nuna bambancin siyasa da kuma rashin adalci a tsakanin ‘ya’yanta da sauransu. Jigogin jam’iyyar APC wadanda suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Chief John-Oyegun da tsohon gwamnan jihar Bayelsa Timipre Sylba suna daga cikin wadanda suka halarci taron kuma suka gabatar da jawabai daban-daban a wurin inda suka nuna a yanzu jam’iyyar da ke mulki a jihar ta koma fanko wanda ba komai a cikinta. RARIYA da wasu daga cikin masu sharhi a kan siyasa suna ganin wannan cigaba ne na mai hakar rijiya wanda kuma tamkar abin kunya ne ga ‘yan siyasa. Ko ina dalili? Abu guda daya ga adawa mai ma’ana, a kowace dimokraddiya sukan kasance masu sanya wa gwamnati ido wajen aiwatar da ayyukanta, kuma adawa na taimakawa wajan tabbatar da an yi wa al’umma aikin da ya kamata a yi masu. ‘Ya’yan jam’iyyar adawa sukan kasance wa gwamnatin da ke mulki tamkar kadangaren bakin tulu. ‘Yan adawa da gwamnati a ko da yaushe suna da wani buri guda daya; wato su warware wa jama’a al’amuran da suka dame su. A duk lokacin da wannan ya yi gabas, to wannan yamma zai yi, ko kuma wannan ya yi hagu, sai wannan ya yi dama, ba domin komai ba sai don ganin an yi wa al’umma abubuwan da suke so. Alal misali jam’iyyar ‘Republican’ a kasar Amurka a manufar jam’iyyar ta yarda da kara kwarin gwiwa ga manyan kasuwanci a saboda samar da ayyukan yi da kuma bunkasa dukiya, kuma tana adawa da kashe kudaden gwamnati. Amma a hannu guda jam’iyyar ‘Dimocrats’ ita tana karawa gwamnati karfin gwiwa ne wajan samar kayayyakin more rayuwa ga talakawa. Idan aka duba dukkanin wadannan jam’iyyun nan guda biyu suna da hanyoyin da suke kare muradun wadanda suka zabe su; wato mutanan Amurka. Idan aka dawo Nijeriya kuwa, jam’iyyar da take mulki a halin yanzu, APC ta kafu ne a sanadiyyar hobbasa da jagoranta, Sanata Ahmad Bola Tinubu ya yi wanda ya kai gwauro ya kai mari har ta samu yawan mutane tare da bin ka’idojinsa musamman a yankin Kudu maso Yamma. Mazabar Tinubu tana adawa da jam’iyya mai mulki ta PDP. RARIYA ta yarda da cewa, muddin babu ingantaccen adawa, siyasa za ta kasance cikin wani irin hali na kokonto wanda hakan zai iya zama tamkar tsarin jam’iyya daya. Wannan ba zai haifar wa da dimokradiyya da mai ido ba. Mun riga mun tabbatar cewa, wannan Nijeriya tana da al’adar gudanar da dimokradiyya ta hanyar tsantsar adawa daga jam’iyyun siyasa wadanda suke da akidunsu ba saboda kudi ba. A jamhoriya ta biyu, a lokacin da ake gudanar da tsarin shiyya-shiyya jam’iyya mai mulki a wancan lokaci, ta NPC ta kafa gwamnati ne a sakamakon hadin gwiwa da suka yi da jam’iyyar NCNC da Chief Obafemi Awolowo wanda ya bar jam’iyyar AG na shiyyar Yamma a matsayiin Premier zuwa tsakiya saboda ya jagoranci jam’iyyar adawa. Ta hanyar suka da shawarwari daga ‘yan adawa, Marigayi Tafawa Balewa ya jagoranci gwamnati. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki suna ganinsa tamkar wanda yake abin da bai kamata, amma ya mayar da hankalinsa ya fi komawa kan abubuwan da suka shafi gwamnati. A lokacin da yarjejeniyar hadaka ta wargaje tsakanin NPN da NPP a lokacin jamhuriya ta biyu, manyan jam’iyyun adawa da wasu gwamnoni suka hada jam’iyyar PPA wanda ta zama jam’iyyar adawa a zaben da aka yi a 1983. Wasu daga cikin gwamnoni su ne, Muhammad Abubakar Rimi na Kano PRP; Abdulkadir Balarabe Musa na Kaduna PRP; Abubakar Barde na rusasshiyar jihar Gongola GNPP; Muhammadu Goni na Borno GNPP; Pa Adekunle Ajasin na Ondo UPN; Bola Ige na Oyo UPN; Lateef Jakande na Lagos UPN; Jim Nwobodo na Anambra NPP; Solomon Lar na Plateau NPP; Ambrose Alli na tsohuwar jihar Bendel UPN. Mafi yawan masu sharhin al’amuran siyasa sun yarda cewa, rashin ingantacciyar adawa tun a shekarar1999 shi ya kawo jam’iyyar PDP ta kai wannan lokaci tana jan zarenta ba tare da tsangwama ba. RARIYA tana ba ‘ya’yan jam’iyyar PDP shawara su zauna a jam’iyyarsu ka da su bijirewa jam’iyya saboda a samu ingantacciyar adawa a Nijeriya wanda zai inganta dimokradiyya. Sauya sheka, tsalle-tsalle, kaura daga nan zuwa can da barin wannan jam’iyyar zuwa waccan ba tare da ko jin kunya ba, yana zubar

SHUGABAN JAM’IYYAR PDP NA JIHAR BAYELSA. TAREDA ‘YA’YAN JAM’IYYAR PDP KIMANIN DUBU DAYA (1000) SUN CANZA SHEKA ZUWA JAM’IYYAR APC, MAI MULKI.
.
A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bayelsa, Kanal Sam Inokoba ya jagoranci ‘ya’yan jam’iyyar PDP kimanin dubu daya, a dandalin wasanni na Samson Siasia da ke babban birnin jihar Yenagoa, suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a kasa APC. Wannan al’amari ba karamin abu ne a wurin jam’iyyar APC, musamman ganin yadda wadansu jiga-jigan mutane suka biyo wannan ayari. Daga cikin ‘yan Bayalsan da suka shigo APC, akwai Sanata Heineken Lokpobri da Mr. Timi Alaibe da sauransu.
Wannan sai ya zama wani abin mamaki ga masu sharhin al’amurran yau da kullum musamman ta yadda suke ganin wannan jihar Bayelsa nan ne mahaifar tsohon shugaban kasa na gwamnatin da ta gabata, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.
A hannu guda kuwa, Kanal Inokoba ya zayyana dalilan da suka sanya suka bar jam’iyyar PDP, wanda ya ce, akwai rashin gudanar da ingantaccen jagoranci da gazawar jam’iyyar ta PDP wajen cika alkawurran da ta dauka wa al’umma da nuna bambancin siyasa da kuma rashin adalci a tsakanin ‘ya’yanta da sauransu.
Jigogin jam’iyyar APC wadanda suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Chief John-Oyegun da tsohon gwamnan jihar Bayelsa Timipre Sylba suna daga cikin wadanda suka halarci taron kuma suka gabatar da jawabai daban-daban a wurin inda suka nuna a yanzu jam’iyyar da ke mulki a jihar ta koma fanko wanda ba komai a cikinta.
RARIYA da wasu daga cikin masu sharhi a kan siyasa suna ganin wannan cigaba ne na mai hakar rijiya wanda kuma tamkar abin kunya ne ga ‘yan siyasa. Ko ina dalili?
Abu guda daya ga adawa mai ma’ana, a kowace dimokraddiya sukan kasance masu sanya wa gwamnati ido wajen aiwatar da ayyukanta, kuma adawa na taimakawa wajan tabbatar da an yi wa al’umma aikin da ya kamata a yi masu. ‘Ya’yan jam’iyyar adawa sukan kasance wa gwamnatin da ke mulki tamkar kadangaren bakin tulu.
‘Yan adawa da gwamnati a ko da yaushe suna da wani buri guda daya; wato su warware wa jama’a al’amuran da suka dame su. A duk lokacin da wannan ya yi gabas, to wannan yamma zai yi, ko kuma wannan ya yi hagu, sai wannan ya yi dama, ba domin komai ba sai don ganin an yi wa al’umma abubuwan da suke so.
Alal misali jam’iyyar ‘Republican’ a kasar Amurka a manufar jam’iyyar ta yarda da kara kwarin gwiwa ga manyan kasuwanci a saboda samar da ayyukan yi da kuma bunkasa dukiya, kuma tana adawa da kashe kudaden gwamnati. Amma a hannu guda jam’iyyar ‘Dimocrats’ ita tana karawa gwamnati karfin gwiwa ne wajan samar kayayyakin more rayuwa ga talakawa. Idan aka duba dukkanin wadannan jam’iyyun nan guda biyu suna da hanyoyin da suke kare muradun wadanda suka zabe su; wato mutanan Amurka.
Idan aka dawo Nijeriya kuwa, jam’iyyar da take mulki a halin yanzu, APC ta kafu ne a sanadiyyar hobbasa da jagoranta, Sanata Ahmad Bola Tinubu ya yi wanda ya kai gwauro ya kai mari har ta samu yawan mutane tare da bin ka’idojinsa musamman a yankin Kudu maso Yamma. Mazabar Tinubu tana adawa da jam’iyya mai mulki ta PDP.
RARIYA ta yarda da cewa, muddin babu ingantaccen adawa, siyasa za ta kasance cikin wani irin hali na kokonto wanda hakan zai iya zama tamkar tsarin jam’iyya daya. Wannan ba zai haifar wa da dimokradiyya da mai ido ba.
Mun riga mun tabbatar cewa, wannan Nijeriya tana da al’adar gudanar da dimokradiyya ta hanyar tsantsar adawa daga jam’iyyun siyasa wadanda suke da akidunsu ba saboda kudi ba.
A jamhoriya ta biyu, a lokacin da ake gudanar da tsarin shiyya-shiyya jam’iyya mai mulki a wancan lokaci, ta NPC ta kafa gwamnati ne a sakamakon hadin gwiwa da suka yi da jam’iyyar NCNC da Chief Obafemi Awolowo wanda ya bar jam’iyyar AG na shiyyar Yamma a matsayiin Premier zuwa tsakiya saboda ya jagoranci jam’iyyar adawa.
Ta hanyar suka da shawarwari daga ‘yan adawa, Marigayi Tafawa Balewa ya jagoranci gwamnati. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki suna ganinsa tamkar wanda yake abin da bai kamata, amma ya mayar da hankalinsa ya fi komawa kan abubuwan da suka shafi gwamnati.
A lokacin da yarjejeniyar hadaka ta wargaje tsakanin NPN da NPP a lokacin jamhuriya ta biyu, manyan jam’iyyun adawa da wasu gwamnoni suka hada jam’iyyar PPA wanda ta zama jam’iyyar adawa a zaben da aka yi a 1983. Wasu daga cikin gwamnoni su ne, Muhammad Abubakar Rimi na Kano PRP; Abdulkadir Balarabe Musa na Kaduna PRP; Abubakar Barde na rusasshiyar jihar Gongola GNPP; Muhammadu Goni na Borno GNPP; Pa Adekunle Ajasin na Ondo UPN; Bola Ige na Oyo UPN; Lateef Jakande na Lagos UPN; Jim Nwobodo na Anambra NPP; Solomon Lar na Plateau NPP; Ambrose Alli na tsohuwar jihar Bendel UPN.
Mafi yawan masu sharhin al’amuran siyasa sun yarda cewa, rashin ingantacciyar adawa tun a shekarar1999 shi ya kawo jam’iyyar PDP ta kai wannan lokaci tana jan zarenta ba tare da tsangwama ba.
RARIYA tana ba ‘ya’yan jam’iyyar PDP shawara su zauna a jam’iyyarsu ka da su bijirewa jam’iyya saboda a samu ingantacciyar adawa a Nijeriya wanda zai inganta dimokradiyya. Sauya sheka, tsalle-tsalle, kaura daga nan zuwa can da barin wannan jam’iyyar zuwa waccan ba tare da ko jin kunya ba, yana zubar

Published by Lecturer Aminu Muhammad kaura

Lecturer Aminu Muhammad Kaura Namoda LG zamfara state Nigeria.

Leave a comment